Bello Turji ya kashe manoma 11 a Sakkwato
Published: 14th, April 2025 GMT
Kasurgumin dan ta’addar nan da ke addabar yankin Sakkwato ta Gabas da Zamfara, Kacalla Bello Turji ya kashe manoma 11 a garin Lugu cikin Karamar Hukumar Isa ta Jihar Sakkwato.
Dan gwagwarmaya da ke biye da lamarin rashin tsaro a yankin Sakkwato ta Gabas Bashiru Altine Guyawa ya sanar wa manema labarai cewa, Turji ya dawo daga yawon sallah ne ya far wa garin da hari.
“Turji da yaransa sun bar kauyensa na Fakai a Karamar Hukumar Shinkafi suka shiga wasu kauyukka a Karamar Hukumar Isa a hanyarsu ta komawa Fakai bayan sun gama yawon Sallah suka kashe manoma 11.”
Guyawa yana ganin laifin jami’an tsaro kan lamari, inda suka gaza daukar mataki kan bayanan sirri da suke da shi.
Dan majalisar dokokin jiha, Honarabul Aminu Boza ya ce, ya samu bayanin sai dai dan bindigar bai shiga yankin da yake wakilta ba a lokacin bikin Sallah.
Ya ce, “muna sane da cewa Turji ya shirya kai ziyara a gabashin Gatawa, a nan ne muka dauki mataki, mun je Sabon Birni, inda muka dauki matakin tsaro don kare faruwar hakan, shi ne dalilin huce haushinsa a kan manoma a Isa’’.
Akwai bayanan da ke nuna cewa, Turji ya tsaya a kauyen Tozai, ya kashe shugaban ‘yan sintiri na garin.
A lokacin da aka tuntubi Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Ahmad Rufa’i ya ce, jami’an soja ne kadai za su iya tabbatar da farmakin saboda su ne ke aiki a yankin.
Duk da sojoji sun ayyana suna neman Turji ruwa jallo, amma ya ci gaba da kai farmaki a kauyukkan gabashin Sakkwato.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Sakkwato Jihar Zamfara
এছাড়াও পড়ুন:
Mummunan Hatsarin Mota Ya Kashe Mutane 7, Wasu 11 Sun Raunato
Aƙalla mutane bakwai sun mutu yayin da wasu 11 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya faru a ƙauyen Essa da ke kan hanyar Agaie-Badeggi, ƙaramar hukumar Katcha, jihar Neja.
Binciken LEADERSHIP ya nuna cewa motar ɗauke da hatsi ta gwamnatin tarayya ce, kuma fasinjojinta maza ne kimanin 36, daga Legas zuwa Kano.
Sojoji Sun Harbe Mutane Biyu Har Lahira Da Ake Zargi Ɓarayin Mota Ne A Filato An Tsinci Gawarwakin Yara Biyar Cikin Tsohuwar Mota A NasarawaHatsarin ya faru ne da ƙarfe 3 na daren ranar Lahadi, lokacin da direban ya yi ƙoƙarin ƙetare wani ɓangare mara kyau na hanyar da ake ginawa.
Daraktan hukumar kula da sufuri na Jihar Neja (NSEMA), Abdullahi Baba Arah, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa ana kan aikin ceto da binciken kan iftila’in.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp