Fadin Yankin Da Ke Fama Da Zaizayar Kasa Na Kasar Sin Ya Ragu A 2024
Published: 22nd, March 2025 GMT
Ma’aikatar kula da albarkatun ruwa ta kasar Sin ta bayyana a jiya Juma’a cewa, fadin yankin kasar dake fama da zaizayar kasa ya ragu zuwa murabba’in kilomita miliyan 2.6019 a shekarar 2024, wanda ya samu raguwar murabba’in kilomita 25,700, idan aka kwatanta da na shekarar 2023.
Wadanann alkaluman wani bangare ne na sakamakon aikin sa ido kan zaizayar kasa a kasar Sin a shekarar 2024, wanda aka kammala a kwanan nan.
Wani jami’in ma’aikatar ya bayyana cewa, sakamakon da aka samu ya nuna cewa, ana samun ci gaba bisa daidaito wajen magance zaizayar kasa a kasar Sin, inda aka samu raguwar fadin yankin da ke fuskantar matsalar da ma karfin zaizayar kasa, gami da raguwar zaizayar kasa bisa dalilan ruwa da iska.
Manyan kogunan da suka hada da kogin Yangtze, Rawayen Kogi, da kogin Huaihe, sun kai kashi 73.19 cikin 100 na yankin da aka samu raguwar zaizayar kasa a fadin kasar baki daya. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: zaizayar kasa a kasar Sin
এছাড়াও পড়ুন:
Adadin Falasdinawan da Isra’ila take kashewa a Gaza yanzu ya haura 60,000
A ci gaba da hare-haren da dakarun Isra’ila ke kai wa a Zirin Gaza, yanzu adadin Falasdinawan da suka kashe ya kai 60,034.
A cewar wasu alkaluma daga Ma’aikatar Lafiya ta Gaza, baya ga wannan, adadin wadanda aka raunata kuma a yanzu sun haura 145,870.
Ma’aikatar ta kuma ce har yanzu ana zargin akwai mutanen kuma da ke karkashin baraguzan gine-ginen da aka rusa, wadanda ba za a iya ciro su daga ciki ba.
Fiye da kaso daya cikin uku na mutanen yankin na shafe kwanaki ba su ci abinci ba, kamar yadda wani rahoton samar da abinci mai lakabin IPC na Majalisar Dinkin Duniya ya tabbatar.
Rahoton ya ce ana samun karin hujjoji da ke nuna ana fama da yunwa da karancin abinci da kuma karuwar mace-mace masu alaka da yunwa a yankin da sama da mutum miliyan biyu da dubu dari daya ke rayuwa a cikinsa.
Hukumomi daban-daban na Majalisar Dinkin Duniya dai sun yi gargadin cewa ana fama da matsananciyar yunwar da aka kirkira da gangan a Gaza, inda a iya wannan watan, rahotanni suka tabbatar da mutuwar mutum 63, dalilin yunwar.
Hukumomin dai sun dora wa Isra’ila duk alhakin matsalolin, kasancewar ita ta yi wa yankin kawanya ta kuma hana a shigar da kayan agaji.
Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya ce: “Abubuwa ne ga su nan a Zahiri, ba a boye suke ba. Falasdinawan da suke Gaza na cikin mawuyacin hali da tsananin bukatar agaji.
“Wannan ba wai gargadi muke yi ba. Gaskiya ce ga ta nan karara. Dole kayan agaji su ci gaba da kwarara. Abinci, ruwan sha, magunguna da man fetur dole su ci gaba da shiga ba tare da kowanne irin tarnaki ba,” in ji Guterres.