Boko Haram ta kashe mutum 300 ta kwace ƙananan hukumomi 3 a Borno — Ndume
Published: 14th, April 2025 GMT
Sanatan Kudancin Borno, Ali Ndume, ya bayyana cewa a halin yanzu mayaƙan Boko Haram sun ƙwace yankunan ƙananan hukumomi uku a jihar.
Ndume ya bayyana cewa mayaƙan kungiyar sun kashe fararen hula sanda a 200 da sojoji 100 a sabbin hare-haren da suka kai a sassan jihar a baya-bayan nan.
A wata zantawar da aya yi da ’yan jarida a ƙarshen mako, ɗan Majalisar Dattawan ya ce mayaƙan Boko Haram sun kai hare-hare 252 a daga watan Nuwamban 2024 zuwa yanzu.
Ya bayyana damuwa game da dawowar munanan ayyukan kungiyar a jihar duk kuwa da kokarin da sojoji da sauran hukumomin tsaro ke yi domin murƙushe su.
Abincin karnuka ya fi wanda ake ba mu —Fursunonin Najeriya NAJERIYA A YAU: Dalilan Farfaɗowar Boko Haram A Jihar BornoA sakamako haka ne ya ce sanatoci da ’yan majalisar wakilan Jihar Borno da Gwamna Babagana Zukum, suka yi zama da sojoji da sauran hukumomin tsaro domin shawo kan matsalar.
Da yake tsokaci kan dawowar hare-haren, Sanata Ndume ya ce, “Wannan abin damuwa ne, duk da cewa sojoji sun halaka ’yan ta’adda sama da 800, su kuma ’yan ta’addan su kashe sama da 500 a sakamakon rikicin ISWAP da Boko Haram.”
Ya ce, “daga watan Nuwambar 2024 zuwa yanzu sun kai hare-hare 252, sun kashe sojoji 100 da fararen hula 500. Yanzu haka kuma kananan hukumomi uku na Jihar Borno — Gudumbari, Maye da Abadam — na hannunsu,” haka zalika sun tarwatsa wasu sansanonin soji da ke wurin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Boko Haram hare hare
এছাড়াও পড়ুন:
ISWAP ta sace ’yan mata 13 a Borno
Mayaƙan ISWAP sun sace wasu ’yan mata a Ƙaramar Hukumar Askira-Uba a Jihar Borno.
Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Borno, Abdullahi Askira, ya tabbatar da sace ’yan matan.
Ɗalibai 50 da aka sace a Neja sun kuɓuta — CAN An rufe duk makarantu a KebbiYa ce an sace ’yan natan ne yayin da suke aiki a gonakinsu da ke yankin Mussa.
A cewarsa, ’yan matan guda 13 masu shekaru tsakanin 15 zuwa 20 sun tafi gona domin girbe amfanin gonarsu, sai maharan suka yi awon gaba da su.
Tun da farko an mayar da mutanen Huyim zuwa Mussa saboda matsalar rashin tsaro a garuruwansu.
Sai dai ya ce ɗaya daga cikin ’yan matan da aka sace ta tsere kuma ta koma gida a safiyar ranar Lahadi, amma sauran 12 har yanzu suna hannun maharan.
Sanata Mohammed Ali Ndume, wanda ke wakiltar yankin, ya yi kira ga hukumomin tsaro da su ceto ’yan matan cikin ƙoshin lafiya.
Ya kuma roƙi al’ummar yankin da su ci gaba da yin addu’a, tare da sanar da hukumomi duk wani abun zargi.