Kasashen Larabawa Na Yankin Tekun Farisa Sun Yi Fatan Al-Khairi Ga Iran Da Amurka A Tattaunawar Shirin Nukliyar Kasar
Published: 14th, April 2025 GMT
Babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa na yankin tekun Farisa (PGCC) ya yi fatan alkhairi ga kasashen Iran da Amurka a tattaunawa ba kai tsaye ba a tsakaninsu dangane da shirin Nukliya ta kasar Iran na zaman lafiya wanda suka fara, a birnin Mascat na kasar Omman a ranar Asabar da ta gabata.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Jasem Mohamed AlBudaiw yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa, kungiyar tana bukatar gidan an warware matsaloli tsakanin kasashen duniya ta hanyar tattanawa.
AlBudaiw ya yabawa kasar Omman da shirya wannan tattaunawar, sannan ya yi fatan tattaunawan da aka fara zai kai ga rage tada jijiyoyin wuya a yankin da kuma kasashen duniya, ya kuma ce kasashen yankin suna fatan zasu kai ga sakamako mai kyau tsakanin kasashen biyu.
Gwamnatin kasar Iran dai tana har yanzun suna shakkar kasar Amurka saboda yawan yaudarar da tayiwa kasar a baya. Musamman fitar kasar daga yarjeniyar JCPOA a shekara ta 2018. Da kuma yawan takunkuman da ta dorawa a kasar tun lokacin.
Daga karshe babban sakataren kungiyar ta PGCC ya ce tana fatan za’a kawo karshen duk wani rikici a gabas ta tsakiya daga ciki har da na HKI a falasdinawa a Gaza ta hanyar tattaunawa da fahintar Juna.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Jagora: Iran a shirye take domin aiki kafada da kafada tare da Saudiyya
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa, Iran a shirye take yin aiki tare da Saudiyya a dukkanin bangarori, domin cin gajiyar al’ummomin kasashen biyu da ma duniyar musulmi, tare da yin ishara da cewa, dukkanin ci gaban da Iran ta samu a dukkanin bangarori na ilimin kimiyya da fasaha, a shirye take ta taimaka ma Saudiyya a wadannan bangarori.
Wannan na zuwa ne a lokacin da Ministan tsaro Yarima Khalid bin Salman dan uwa ga Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ya gana da Ayatollah Khamenei a Tehran da yammacin jiya Alhamis don mika sakon Sarki Salman na Saudiyya.
Jagoran ya ce: “Mun yi imanin cewa dangantakar da ke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Saudiyya za ta kasance mai amfani ga kasashen biyu, kuma kasashen biyu za su iya kara kaimi domin karfafa juna.”
Ya kara da cewa “Yana da kyau ‘yan’uwa a yankin su hada kai da taimakon juna fiye da dogaro da wasu.”
Ayatullah Khamenei ya jaddada cewa fadada alaka tsakanin kasashen biyu ba abu ne da makiya za su yi farin ciki da shi ba, amma ya zama wajibi a yi hakan domin amfanin al’ummomin kasashen yakin da kuma al’ummar musulmi.
Ministan tsaron Saudiyya ya bayyana matukar jin dadinsa game Na zo Tehran ne da ajandar fadada alaka da Iran da kuma yin hadin gwiwa a dukkan fannoni,” in ji Yarima Khalid,
Ya kara da cewa “Kuma muna fatan wannan tattaunawar mai ma’ana za ta samar da kyakkyawar alaka tsakanin Saudiyya da Jamhuriyar Musulunci ta Iran fiye da kowane lokaci a tarihi.”