Fashin Baki Kan Kasafin Kudin 2025 Na Naira Tiriliyan 54.99
Published: 22nd, March 2025 GMT
Bubu da kari, abin mahimmancin shi ne, shi talakan Nijeriya zai iya gani a kas na irin wadannan shirye-shiyen da gwamnatin ke son aiwatarwa?
Fannin Da Gwamnatin Za Ta Zuba Kudaden:
A kasafin kudin na 2025, Gwamnatin Tarayya ta warewa bangaren tsaro Naira tiriliyan 6.11 wanda ya kai ta samar da karin kaso 88 daga cikin kasafin kudin da ta warewa fannin na Naira tiriliyan 3.
Shin wannan burin na Gwamnatin zai iya cika, duba da yadda aka gaza dakile ta’addanci, ‘yan fashin daji, wanda idan ba a mayar da hankali ba, a 2025, tarihi ne zai sake mai-maita kansa.
An ware Naira tiriliyan 5.99 a cikin kasafin kudin don yin tituna, gadoji da kuma manyan ayyuka a babbar hanyar da ta tashi daga Legas zuwa Kalaba da ta Sokoto zuwa Badagry, inda aka samu karin da ya kai sama da kaso 350 sabanin Naira tirliyan 1.32 da aka ware a kasafin kudin bara.
Idan har da a gudanar da wadannan ayyukan, za su kara samar da ayyukan yi da habaka kasuwanci.
Bugu da kari, a kasafin kudin na 2025, an warewa ilimi, kiwon lafiya da bunkasa hazaka Naira biliyan 5.7 wanda ya kai kaso 161, sabanin Naira tiriliyan 2.18 da aka ware a kasafin kudi na 2024, inda fannin aikin noma ya samu Naira tiriliayan 3.73, wanda hakan ya nuna an samu kari mai yawa da ya zarta na Naira biliyan 362, inda an yin wannan karin ne, don a karya farashin kayan abinci a kasar.
Sai dai, shin ko wannan karin kudaden zai samar wa talakawan kasar sauki?
Amma wasu kwararu a Cibiyar Tsare-Tsare Da Bincike Kan Tattalin Arzikin Kasa (CEPR) ta yi nuni da cewa, idan har ba a wanzar da kuma kara kudi a cikin kasafin kudi hakan ba zai yi tasiri ba.
Kara Yawan Karbo Rancen Kudade:
Kudin ruwan da bashin da Gwamnatin ke biya ya lakume Naira tirilaya 16.3, wanda ya kai kaso 98, inda hakan ya nuna an samu karin Naira 8.25 a kasafin kudi na 2024.
Sai dai, wani babban kalubalen shi ne, yadda Nijeriya ke biyan bashin kudin ruwa na bashin da ta karbo fiye da wanda rake son kashewa a bangarorin ilimi, kiwon lafiya da samar da kayan aiki.
Gwamnatin ta yi hasahsne kudaden shiga da take son samu za su karu daga Naira tiriliyan18.32 zuwa Naira 36.35 trillion, wadanda suka kai karin kaso 123.19, musamman ta hayar tara haraji da zuba hannun jari na ketare.
Duba da yadda a arihin Nijeriya ka gaza tara kudaden shigar da ake sa ran tarawa, wasu kwararru a taron kungiyar tattalin arziki Nijeriya (NESG) sun yi garadin cewa, bai mai yuwa banen wadannan hasashen da aka yi su tabbata ba.
Kasafin kudin kasar ya rubanya a cikin shekara daya, amma duk da haka kudaden shigar kasar sun yi rauni.
Alal misali, a cikin kasafin kudin na 2025, ‘yan Majalisa sun samu karin Naira biliyan 344.85, wanda a kasafin kudi na 2024, suka samu karin Naira biliyan 197.93, inda kuma su ke son ‘yan kasar su kara jan damarar ci gaba da kula da rayuwarsu.
Bugu da kari, ‘yan Malasira Dokoki sun sun samawar da kansu karin sma da Naira biliyan 7 na kudaden sun a tafiye-tafiye, da kuma wasu dimbin kudaden da suka warewa kansu na jin dadi da na biyan kafafen ‘yada labarai.
A shirye-shiyen jin kan alumma, an ware Naira biliyan 723.68 kacal wanda aka kara kudin zuwa Naira biliyan 600, amma duk da haka, wani dan bangare kadan ne, aka kashe kan ayyukan gwamnatin.
Akwai dai dimbin buri da aka sanya a cikin kasafin kudin na 2025, wanda duk da wannan burin, cin abinci sauku a rana, na neman gagarar talakan kasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Naira tiriliyan Naira biliyan
এছাড়াও পড়ুন:
Sauya Sheka Ya Sa APC Ta Samu Gagarumin Rinjaye A Majalisun Tarayya
Biyo bayan sauya sheka da aka yi kwanan nan, a zauren majalisar dattawa, APC na da kujeru 68; PDP na da 30; LP na da 5; SDP na da 2; NNPP na da 1; APGA na da 1 da kuma kujeru guda biyu da babu kowa, guda daya daga Jihar Edo da daya daga Jihar Anambra.
Masana harkokin siyasa na ganin cewa bisa yadda lamura suke a halin yanzu, adadin na iya haurawa lokacin da majalisar tarayya ta dawo daga hutu, bayan sauya shekar Gwamna Umo Eno na Jihar Akwa Ibom daga PDP zuwa APC. Ana sa ran wasu daga cikin ‘yan majalisar tarayya na jihar za su iya bin sahunsa. A halin yanzu, Jihar Akwa Ibom tana da sanatan PDP guda biyu da ‘yan majalisar wakilai guda bakwai daga PDP.
Tun da aka rantsar da majalisar dattawa ta 10 a watan Yuni 2023, ‘yan majalisa da dama sun koma APC, wanda ya sa jam’yyar na ci gaba da samun gagarumar rinjaye.
Sanata Ibrahim Abdullahi Danbaba, mai wakiltar Sakkwato ta kudu na jam’iyyar PDP, ya koma APC a watan Maris 2024. Da farko, Sanata Ifeanyi Ubah ya canza sheka daga YPP zuwa APC a watan Oktoba 2023 kafin rasuwarsa.
A watan Fabrairu na 2025, Sanata Ned Munir Nwoko, mai wakiltar Delta ta arewa ya bar PDP ya koma APC, yana mai bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida a PDP na Delta ya sa ya sauya sheka.
Haka kuma, Sanata Ezenwa Onyewuchi, mai wakiltar Imo ta gabas, wanda aka zaba a karkashin jam’iyyar LP, ya koma APC a watan Yulin 2024, yana mai cewa batutuwan cikin gida ne suka jawo hakan.
Sanata Kawu Sumaila, mai wakiltar Kano ta kudu, wanda aka zabe a karkashin tutun jam’iyyar NNPP, ya sauya sheka zuwa APC a ranar 7 ga Mayu, 2025.
Bayan haka, sanatoci guda uku daga Kebbi da suka hada da Adamu Aliero, mai wakiltar Kebbi ta tsakiyar da Yahaya Abdullahi, mai wakiltar Kebbi ta arewa, da Garba Maidoki, mai wakiltar Kebbi ta kudu, suka sauya sheka daga PDP zuwa APC bayan taron da Shugaban kasa Bola Tinubu ya kira a fadar shugaban kasa.
Kazalika, tun lokacin da aka kaddamar da majalisar wakilai ta 10 a watan Yuni na shekarar 2023, wannan majalisa ya fuskanci lamarin sauya sheka ga wasu daga cikin ‘yan majalisa, wanda ya faru sakamakon sabani na ciki gida a jam’iyyu, matsin lamba na mazabu da kuma sabbin tsarin siyasa wanda hakan ya amfanar da APC.
Da farko, APC ta rike kujeru 175; PDP na da 118; LP na da 35; NNPP na da 19; APGA na da 5; ADC na da 2; SDP na da 2; YPP na da 1; yayin da kujeru uku babu kowa. Gaba daya dai, ‘yan adawar na rike da kujeru 182 fiye da APC. Amma yau, adadin kujerun ’yan adawar ya ragu zuwa 150.
An fara wannan salo ne a ranar 23 ga Yuli, 2024, lokacin da Hon. Idris Salman, mai wakiltar Kabba-Bunu/Ijumu a Jihar Kogi, ya canza sheka daga ADC zuwa APC, yana mai cewa akwai rikicin shugabanci da kuma matsi daga mazabarsa wanda ya sa ya koma jam’iyyar da ke mulki.
A watan Oktoba na 2024, Hon. Chris Nkwonta, mai wakiltar mazabar Ukwa ta yamma da Abiya ta yamma, ya bar PDP ya koma APC a ranar 2 ga Oktoba. Bayan haka a wannan watan, Hon. Sulaiman Abubakar, mai wakitar Gummi/Bukkuyum a Zamfara, shi ma ya fice daga PDP.
Jam’iyyar LP, wacce ta sami karfi a shekara ta 2023, ta fara fuskantar manyan tangarda a karshen shekarar.
A ranar 5 ga Disamba, 2024, ‘yan majalisar LP hudu cikin har da Hon. Chinedu Okere, mai wakiltar Owerri da kewaye da Hon. Mathew Donatus, mai wakiltar Kaura a Kaduna da Hon. Bassey Akiba, mai wakiltar Kalabar da kewaye /Odukpani a Kuros Ribas da Hon. Esosa Iyawe, mai wakiltar Oredo a Jijar Edo, sun koma APC, suna mai bayar da hujja kan rikice-rikicen cikin gida da suka kawo cikas ga kwazonsu.
Hon. Alfred Ajang, mai wakiltar Jos ta kudi / gabas a Filato, ya biyo bayansu a ranar 12 ga Disamba, yana jaddada dalilai masu kama da juna.
Sauyin ya ci gaba har zuwa 2025. A ranar 11 ga watan Fabrairu, Hon. Amos Magaji, mai wakiltar Zangon Kataf/Jaba a Jihar Kaduna) ya sauya sheka daga PDP zuwa APC, yana mai cewa akwai rigima a cikin jam’iyyarsa ta asali.
Washagarin ranar, Hon. Garba Koko, wai wakiltar Kebbi shi ma ya shiga APC daga PDP.
A ranar 18 ga Maris, Hon. Jallo Hussaini Mohammed, mai wakiltar Igabi a Jihar Kaduna, da Hon. Adamu Tanko, mai wakiltar Gurara/Suleja/Tafa a Neja, sun sauya sheka zuwa APC daga PDP, su yi ikirarin cewa rashin jin dadin shugabancin PDP da kuma bayyana kwarin gwiwa a gwamnatin Tinubu su ne makasudin sauya shekarsu.
A ranar 27 ga Maris, Farfesa Chinwe Clara Nnabuife, mai wakiltar Orumba ta arewa/kudu, a Jihar Anambra) ta fice daga YPP zuwa APGA, tana zargin an tsame ta daga ayyukan jam’iyyar.
A watan Mayu na shekara ta 2025, ya zama lokacin da aka sami manyan sauye-sauye. A ranar 6 ga Mayu, ‘yan majalisar PDP guda shida daga Jihar Delta sun canza sheka zuwa APC bayan gwamnan jihar, Sheriff Oborebwori ya jagoranci wannan sauyin. ‘Yan majalisar dai su ne, Hon. Bictor Nwokolo, mai wakiltar Ika arewa, gabas/Ika ta kudu da Hon. Julius Pondi, mai wakiltar Burutu da Hon. Thomas Ereyitomi, mai wakiltar mazabar Warri da Hon. Nicholas Mutu, mai wakiltar Bomadi/Patani) da Hon. Ukodhiko Jonathan, mai wakiltar mazabar Isoko da Hon. Ezechi Nnamdi, mai wakiltar Ndokwa/Ukwuani).
A ranar 15 ga watan Mayu, ‘yan majalisa biyu daga jam’iyyar NNPP, Kabiru Usman da Abdullahi Sani, sun shiga APC. A wannan ranar, dan majalisan PDP mai wakiltar Oriade/Obokun daga Jihar Osun, Oluwole Oke, shi ma ya koma APC.
A ranar 22 ga Mayu, Hon. Sunday Umeha, mai wakitar Udi/Ezeagu daga Jihar Inugu, wanda aka zaba a karkashin LP, ya koma APC, yana cewa har yanzu matsalolin cikin gida na ci gaba da raba kawunan ‘ya’yan jam’iyyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp