Fursunoni 16 sun tsere daga gidan yarin Keffi
Published: 13th, August 2025 GMT
Ana fargabar cewa wasu fursunoni 16 sun tsere daga gidan yarin Keffi da ke Jihar Nasarawa bayan wani kwantan bauna da suka yi wa gandirebobi.
Wata sanarwa da mai magana da yawun Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali a Nijeriya, Umar Abubakar, ta ce fursunonin da ke gidan sun yi wa ma’aikatan da ke tsaronsu rubdugu, lamarin da ya bai wa mutane 16 damar guduwa a safiyar wannan Talatar.
Sanarwar ta ce biyu daga cikin jami’ai biyar da suka ji rauni a yayin harin na cikin mawuyacin hali, kuma yanzu haka ana duba lafiyarsu a wani asibitin gwamnati.
Ya kara da cewa an kamo mutumin bakwai daga cikin waɗanda suka tsere yayin da ake ci gaba da neman ragowar fursunoni tara.
Sanarwar ta ambato cewa Kwanturola-Janar na Hukumar Gidajen Gyaran Hali a Nijeriya, NCoS, Sylvester Nwakuche, ya ziyarci wurin bayan faruwar lamarin, inda ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike tare da gargaɗin cewa duk wani ma’aikaci da aka samu da hannu zai kuka da kansa.
Haka kuma, Nwakuche ya ba da umarnin a gaggauta fita samamen haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin kamo waɗanda suka tsere.
Mahukunta sun yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu, tare da neman su hanzarta bayar da rahoton duk wani motsi ko alamar mutanen da suka tsere ga ofishin tsaro mafi kusa.
A ‘yan shekarun nan dai, an samu tserewar fursunoni a Nijeriya lokuta daban-daban, inda a bara kaɗai, fursunoni 118 sun tsere daga gidan gyaran hali na Suleja a Jihar Neja, bayan ruwan sama mai karfi ya lalata bangon gidan yarin da ake cewa daɗewarsa ce ta janyo rushewar ginin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gidan Yarin Keffi Jihar Nasarawa
এছাড়াও পড়ুন:
Maryam Sanda na cikin waɗanda Tinubu ya yi wa afuwa
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa Maryam Sanda afuwa, wadda aka yanke wa hukuncin kisa a shekarar 2020 bisa laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello, ɗan tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Alhaji Haliru Bello.
Maryam,’ mai shekara 37, ta shafe shekaru shida da watanni takwas a gidan yarin Suleja kafin yi mata afuwa.
Talauci da tsangwama na hana yara mata karatu a Gombe — Kwamishina Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaroRahotanni sun nuna cewar an yi mata afuwar ne bayan yin nadama da aikata kyakkyawan halaye.
Iyayen Maryam sun roƙi gwamnati da ta sake ta saboda ’ya’yanta biyu da ta ke da alhakin kula da su, tare da alƙawarin sauya halayenta.
Shugaba Tinubu, ya kuma yi wa wasu mutane afuwa da suka haɗa da Manjo Janar Mamman Vatsa, Ken Saro-Wiwa, da kuma Sir Herbert Macaulay.
Gaba ɗaya mutane 175 ne shugaban ya yi musu afuwa, ciki har da masu manyan laifuka, tsoffin fursunoni, da waɗanda suka yi kyakkyawan tuba.
Wannan shi ne karon farko da Shugaba Tinubu ya yi amfani da ikon yafe laifi don tausaya wa waɗanda suka aikata laifuka tun bayan hawansa mulki.