‘Yan Nijeriya Miliyan 14 Sun Yi Bikin Murnar Karɓar Kyautar N23m Daga Bankin STANBIC IBTC
Published: 12th, August 2025 GMT
Hakan ya gudana a ƙarƙashin jagorancin hukumomin da ke lura da yadda ake tafiyar da gasar da kuma kare haƙƙin masu amfani da kaya (FCCPC), hukumar kula da tallace-tallace ta Nijeriya (ARCON), da hukumar kula da harkokin caca da wasanni ta Jihar Legas (LSLGA).
Zaɓen ya kasance cikin gaskiya da adalci, inda waɗanda yi nasara suka bar Naira 10,000 a cikin asusun ajiyarsu na Stanbic IBTC ko @ease Wallet har tsawon kwanaki 30.
Daga mata ‘yan kasuwa, zuwa ɗalibai, har zuwa ma’aikatan da suka yi ritaya, waɗanda suka yi nasara yanzu suna iya biyan kuɗin makaranta, fara ƙananan sana’o’i, ko kuma tafiyar da buƙatun gidajensu cikin sauƙi.
An ƙara sanya wasu mutane takwas cikin farin ciki a zaɓen babbar garaɓasar wata huɗu ta farkon shekara wanda aka yi a ranar 7 ga wata.
Mutane bakwai daga kowace shiyya sun samu Naira miliyan ɗaya kowannensu, yayin da babbar kyauta ta wata huɗu ta kai Naira miliyan biyu aka bai wa mutum ɗaya.
Jimillar kyautar ta kai Naira miliyan tara. Hanyoyin da aka bi wajen zaɓar waɗanda suka yi nasara sun nuna irin yadda Bankin Stanbic IBTC ke bai wa kowane mai ajiya muhimmanci.
Zaɓen waɗanda suka yi nasara saboda ajiyar kuɗi a watan Mayun 2025, bankin ya raba Naira miliyan 30 ga mutane 218 a karo na huɗu, yayin da aka raba wa mutane sama da 2,000 Naira miliyan 300 masu asusun ajiya tun fara shirin a shekarar 2021.
Bankin Stanbic IBTC ya kasance ginshiƙi wajen tallafanwa rayuwar ‘yan Nijeriya.
Emmanuel Aihevba, Shugaban Bankin Stanbic IBTC a Nijeriya, ya ce: “Bikin zaɓar waɗanda suka cancanta, ba su kyauta, da yadda aka gudanar da shi a cikin wata biyu, har ma na farkon wata huɗu na bana, ya nuna yadda muke farin ciki da abokan hulɗarmu da suka mayar da hankali kan ajiya. Mun saka wa masu hulɗa da mu 148 zunzurutun kuɗi har Naira miliyan 23 saboda amincewarsu da tafiya tare da mu. Muna son su yi amfani da wannan kuɗi don bunƙasa harkar ilimi ko sana’a.
“A Bankin Stanbic IBTC, muna nuna cewa ya dace mu samar wa abokan hulɗarmu damar bunƙasa rayuwarsu da kuma koya musu yadda za su saba da al’adar ajiyar kuɗi a faɗin Nijeriya.”
Kesena Igben, wani mutum da ya yi ritaya kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka yi nasara a gasar, ya bayyana farin cikinsa.
“Na zo tare da ‘yata domin karɓar kyauta. A hanya ta ce, ‘Baba, na ga kana farin ciki.’ Sai na ce mata, ‘Kin san wannan kuɗi zai taimaka min wajen sayen man fetur na mako biyu?’ A gare ni, wannan kyauta ta Bankin Stanbic IBTC babbar alfarma ce, saboda ta rage min damuwar neman kuɗin fetur na mako biyu.”
Yadda Stanbic IBTC ke nuna damuwarsa kan farin cikin abokan hulɗarsa ya nuna yadda suka saka gaskiya da adalci a harkokinsu.
Hukumar Kare Haƙƙin Masu Amfani da Kaya ta bai wa bankin kyautar ARCON a shekarun 2023 da 2024.
Don haka kai ma shiga cikin jerin waɗanda za su kasance cikin farin ciki!
Ajiye Naira 10,000 kacal ko sama da haka har tsawon kwanaki 30 ko a asusun ajiyarka na Stanbic IBTC ko @ease Wallet domin samun damar shiga sahun waɗanda za su lashe kyautar.
Latsa wannan domin samun damar shiga https://smebanking.stanbicibtc.com/AccountOpening/tier-one ko ka ziyarci kowanne reshen bankin, ka fara daga yau!
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Abokan Hulɗa Ajiya Kyauta waɗanda suka yi nasara Naira miliyan
এছাড়াও পড়ুন:
China Ta Yi Tir Da Yadda Kasar Japan Ta Girke Makaamai Masu Linzami A Kusa Da Yankin Taiwan
A jiya Litinin ne dai mahukuntan kasar ta China su ka yi Allawadai da yadda kasar Japan din ta girke makamai masu linzami a wani tsibirinta da yake kusa da yankin Taiwan, tare da bayyana hakan a matsayin kokarin tayar da hargitsi a cikin yankin.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar China Máo Níng ta bayyana cewa: Daukar mataki irin wannan, wanda kuma ya zo bayan furucin Fira Ministar kasar ta Japan Sanae Takaichi,wani yanayi ne mai hatsarin gaske wanda yake da bukatuwa da kasashen yankin su kasance a cikin fadaka, haka nan kuma kungiyoyin kasa da kasa.
Shi kuwa ministan tsaron kasar Japan ya bayyana cewa; Girke makamai masu linzami da kasarsa ta yi a tsibirin Yonagoni dake kusa da Taiwan, zai iya taimakawa wajen ragen yiyuwar kaai wa Japan hari.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Velayati: Alakar Iran da Iraki tana da karfi November 25, 2025 Arakci Ya Yi Gargadi Akan Abin Zai Biyo Bayan Keta Dokokin Duniya Da “Isra’ila” Take Yi A Cikin Wannan Yankin November 25, 2025 An Gudanar Da Jana’izar Shahidai 300 A Dai-Dai Ranar Shahadar Zahra (s) A Jiya Litinin November 25, 2025 Amurka Da HKI Sun Kawo Karshen Hukumar GHF Mai Raba Abinci A Gaza November 25, 2025 Babban Kwamandan Sojojin Sudan Ya Yi Watsi Da Shirin Trump Na Zaman Lafiya November 25, 2025 Hamas Ta Ce Keta Hurumin Tsagaita Wutan Da HKI Take Yi Zai Iya Kawo Karshen Tsagaita Wutar November 25, 2025 Gwamnonin Kudu Maso Yammacin Najeriya Sun Ce Lokacin Kafa Yansandan Jihohi Ya Yi November 25, 2025 Hizbullah Ta na Juyayin shahadar Babban Kwamanda Haitham Ali Da Isra’ila Ta Kashe. November 24, 2025 Dubban Alummar Kasar Tunisia Ne Suka Gudanar Da Zanga-zangar Adawa Da Mulkin Kama Karya A Kasar November 24, 2025 Mutane 6 Ne Suka Mutu Sakamakon Harin Kunar Bakin Wake Da Aka Kai A Peshavar Na Kasar Pakistan November 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci