Jiragen saman NAF Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 592, Sun Lalata Kayayyakin Yaki 372
Published: 12th, August 2025 GMT
Ejodame ya rahoto CAS, yana cewa “Tare da ingantattun jirage da ke da ingantattun tsare-tsaren kai hare-hare na dare, jirgin NAF ya kai hare-hare guda 798”.
A nasa jawabin, Gwamna Zulum ya yabawa NAF bisa ci gaba da bayar da tallafi ta sama wajen gurgunta karfin ‘yan ta’adda da kuma kare al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamnan Bauchi ya yi ta’aziyyar rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Bauchi, a matsayin babban rashi ga al’umma.
Gwamnan ya bayyana malamin a matsayin jagoran haɗin kai, zaman lafiya, da fahimtar juna tsakanin Musulmi da mabiya addinai daban-daban.
’Yan sanda sun gano harsasai 210 a kan titin Zariya-Funtuwa Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwaA cikin saƙon ta’aziyya da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Mukhtar Gidado, ya sanya wa hannu, gwamnan ya ce Gwamnatin Jihar Bauchi tana alhinin rasuwar malamin.
Dahiru Bauchi, ya rasu da safiyar ranar Alhamis, 27 ga watan Nuwamba, 2025 a Bauchi, yana da shekara 102.
Gwamnan, ya ce Sheikh Dahiru Bauchi babban malami ne na addinin Musulunci, mai imani, tawali’u da hikima.
A cewarsa ya sadaukar da rayuwarsa wajen yaɗa addinin Musulunci, koyar da Alƙur’ani, da kuma taimaka wa mutane wajen tarbiyya.
Marigayin, ya koyar da dubban ɗalibai da suka haddace Alƙur’ani tare da yaɗa addinin Musulunci a sassan nahiyar Afrika.
Gwamnan, ya ƙara da cewa gudunmawar da marigayin ya bayar a fannin tafsiri, fiqhu da tarihi sun taka muhimmiyar rawa wajen ɗora al’umma kan turbar tsira.
Har ila yau, ya ce Gwamnatin Jihar Bauchi za ta ci gaba da girmama marigayin ta hanyar tallafa wa makarantu da manufofin da ya gina, musamman a fannin ilimin addinin Musulunci, tarbiyya da ci gaban al’umma.
Ya yi addu’a rAllah ya gafarta masa kurakuransa, ya sanya shi aAljannatul Firdausi, ya kuma bai wa iyalansa, mabiyansa da ɗaukacin al’ummar Musulmi haƙurin rashinsa.