‘Yan Sanda Sun Kama Wasu Da Ake Zargin ‘Yan Kungiyar Asiri Ne A Jihar Kwara
Published: 12th, August 2025 GMT
Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta kama wasu mutane biyu da ake zargin ’yan kungiyar asiri ne tare da kwato musu wasu abubuwa na bata gari a Ilorin.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Adetoun Ejinre-Adeyemi ya fitar, ya ce, ‘yan sandan da ke aiki bisa sahihiyar bayanan sirri daga majiyoyin tsaron al’umma, sun dauki wami mataki kan wani harin fashi da makami da ya afku a wani dakin kwanan dalibai da ke unguwar Eleko, Ilorin.
Sanarwar ta ce ba tare da bata lokaci ba jami’an ‘yan sanda da ‘yan banga, sun kai ga kama wasu maza biyu da ake zargi.
Ta ce wadanda ake zargin sun hada da Ishola Adeyemi, da Ismail Rafiu dukkansu na Ibadan, jihar Oyo.
A cewarsa yayin da ake yi musu tambayoyi na farko, wadanda ake zargin sun amsa cewa wani Qudus mai suna “Tiny”, memba ne na kungiyar Ido Cult Fraternity, ya gayyace su zuwa Ilorin don kawar da wani dan kungiyar asiri.
Ya yi nuni da cewa, a lokacin da harin nasu bai yi nasara ba, sai suka koma yin fashi a gidajen kwanan dalibai a yankin.
Ya yi bayanin cewa wadanda ake zargin, tare da baje kolin da aka kwato an mika su zuwa Sashen Yaki da Fashi, Sashen Binciken Laifukan Jiha (SCID), hedikwatar Jiha, don ci gaba da bincike da kuma gurfanar da su a gaban kotu.
REL/ALI MUHAMMAD RABIU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: da ake zargin
এছাড়াও পড়ুন:
Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja
Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya sauke Kwamishinan ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, Ajao Adewale, daga muƙaminsa.
Ko da yake ba a bayyana cikakken dalilin da ya sa aka sauke shi ba, majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa hakan ya faru ne sakamakon yadda rundunar Abuja, ta tafiyar da lamarin sanya gilishin mota mai duhu da kuma mutuwar ’yar jaridar gidan talabijin na Arise News.
Tinubu ya tafi Rome don halartar taro kan sha’anin tsaro Mutane 2 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a KebbiƊaya daga cikin majiyoyin ta bayyana cewa waɗannan matsalolin guda biyu ne suka janyo sauya masa wajen aiki.
Ta ƙara da cewa za a tura Adewale wani waje daban, inda za a fi buƙatar ƙwarewarsa.
Da aka tambayi inda za a tura shi, majiyar ta ce Sufeton Janar na ’yan sanda ne zai bayyana hakan, tare da jaddada cewa Adewale ya yi iya bakin ƙoƙarinsa a matsayin kwamishina.
Kakakin rundunar ’yan sanda ta ƙasa, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da wannan sauyi, inda ya ce sauyin wajen aiki al’ada ce da ake yi domin inganta ayyukan jami’an rundunar.