Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-08-13@12:01:34 GMT

Tinubu Ya Nada Hukumar Gudanarwa Ta NCC Da Sauran su

Published: 13th, August 2025 GMT

Tinubu Ya Nada Hukumar Gudanarwa Ta NCC Da Sauran su

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da kundin tsarin mulki na hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC) da asusun samar da ayukka na kasa da kasa (USPF), dukkanin su a karkashin ma’aikatar sadarwa, kirkire-kirkire da tattalin arziki na zamani.

 

A cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai baiwa shugaban kasa shawara kan yada labarai ya fitar, ya ce an nada Idris Olorunnimbe a matsayin shugaban hukumar NCC, yayin da Dr.

Aminu Waida ya ci gaba da zama mataimakin shugaban zartarwa/Babban jami’in gudanarwa, mukamin da aka nada shi a watan Oktoban 2023 kuma majalisar dattawa ta tabbatar da shi a watan Nuwamba na wannan shekarar.

 

A baya Olorunnimbe ya yi aiki a hukumar kula da ayyukan yi na jihar Legas (LSETF), inda ya jagoranci kwamitin masu ruwa da tsaki da gudanar da mulki tare da jagorantar shirye-shiryen samar da ayyukan yi da samar da kasuwanci ga matasa.

 

Sauran mambobin hukumar NCC sun hada da Abraham Oshidami (Kwamishina, Ayukkan Fasaha), Rimini Makama (Kwamishiniyar Gudanarwa), Hajia Maryam Bayi (Kwamishinar kula da ma’aikata), Col. Abdulwahab Lawal (Rtd), Sanata Lekan Mustafa, Chris Okorie, Gimbiya Oforitsenere Emiko, da Sakataren Hukumar.

 

 

Ga USPF, Dokta Bosun Tijani, Ministan Sadarwa, Ƙirƙiri da Tattalin Arziki na Zamani, zai zama shugaba. Olorunnimbe kuma an nada mataimakin shugaba.

 

Sauran mambobin sun hada da Oshidami, Makama, Aliyu Edogi Aliyu (wakilin FMCIDE), Joseph B. Faluyi (Ma’aikatar Kudi ta Tarayya), Auwal Mohammed (Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsare ta Tarayya), Uzoma Dozie, Peter Bankole, Abayomi Anthony Okanlawon, Gafar Oluwasegun Quadri, da Sakataren USPF.

 

PR/Bello Wakili

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Hukumar Kwatsam ta kama makamai da ƙwayoyin N10bn a Legas

Hukumar Kwastam Najeriya ta kama kwantainoni 16 ɗauke da makamai da miyagun ƙwayoyi da magungunan da wa’adin aikinsu ya ƙare da wasu haramtattun kaya na kimanin Naira 10 a Tashar Jiragen Ruwa ta Apapa da ke Jihar Legas a ranar Litinin.

Hukumar ta bayyana cewa ta kama mutane shida dangane da wannan haramtattun kaya da aka yi fasa-ƙwaurin su zuwa Najeriya.

Kwanturola Janar na Kwastam, Adewale Adeniyi, ya sanar da cewa an yi ƙarya wajen bayyana kayan da  kwantainonin suke ɗauke da su, inda aka ɓoye makamai, harsasai da magungunan da ba su da rajista.

“A yau, muna sanar da kama kwantainoni 16 da shigowarsu ke karya dokokinmu kuma suna barazana ga tsaron ƙasa. Darajar harajin da za a biya kan waɗannan kaya ya haura Naira biliyan 10,” in ji Shugaban Hukumar.

Yadda ɗan shekara 70 ya rasu a gobarar tankokin gas a Zariya EFCC ta tsare tsohon Gwamnan Sakkwato Aminu Tambuwal kan zargin N189bn

Kayan da aka kama sun haɗa da:

– Bindigogi biyu na pump-action, bindiga ɗaya nau’in Smith & Wesson da harsasai fiye da 80

– Kwalaye 202 na kayan maye (Colorado Loud), nauyinsu ya kai kilo 101

– Kwantainoni 7 na magungunan da suka daina da haramtattu

– Kwantainoni 3 na abinci da ya lalace.

– Kwantainoni 3 na haramtattun tufafi

– Kwantainoni 2 ɗauke da magungunan codeine

– Kwantaina ɗaya da ke ɗauke da kwalaye 305 na man goge baki na ƙarya da aka ɓoye da ɗinki da kayan ado

Adeniyi ya ce an gudanar da binciken tare da haɗin gwiwar Hukumar NDLEA da sauran hukumomin gwamnati.

Ya jaddada cewa har yanzu an dakatar da amfani da tashoshin wajen fitar da magunguna.

An kama mutane biyar, inda uku daga cikinsu aka gurfanar da su kuma suna tsare a gidan yari na Ikoyi har sai an fara shari’ar su.

Hukumar Kwastam ta ce tana aiki da abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa don gano tushen waɗannan kaya da hana Najeriya zama wurin zubar da haramtattun kaya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Lafiyar Tinubu kalau – Soludo
  • Yadda Kwastam ta kama makamai da ƙwayoyin N10bn a Legas
  • Tinubu Ya Sake Nada Dankaka A Matsayin Shugaban Hukumar Kula Da Da’ar Ma’aikata Ta Kasa
  • Hukumar Kwatsam ta kama makamai da ƙwayoyin N10bn a Legas
  • Tinubu Ya Jinjinawa NAFDAC Bisa Matsayin Da Ta Taka A Hukumar Lafiya Ta Duniya
  • Araghchi: Mataimakin Shugaban IAEA Zai Ziyarci Tehan َA Gobe Talata
  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Kaddamar Da Tantance Malamai Da Ma’aikatan Lafiya
  • EFCC ta kama ’yan damfara a ɗakin karatun Obasanjo 
  • UADD Ta Yaba Wa Gidauniyar Tunawa Da Sardauna Kan Himma Da Kishin Kasa