Sojojin Yemen Sun Kai Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’Ila Har Sau Shida
Published: 13th, August 2025 GMT
Sojojin Yemen sun sanar da cewa: Sun kai hari kan muhimman wurare hudu na haramtacciyar kasar Isra’ila da jirage marasa matuka guda shida
Sojojin Yemen sun sanar a yammacin jiya Talata cewa: Sun kai farmakin soji ta hanyar amfani da jiragen sama marasa matuka ciki guda shida, inda suka kai hari kan wasu muhimman wurare 4 na haramtacciyar kasar Isra’ila a yankunan Haifa, Negev, Umm al-Rashrash, da kuma Bi’ersheba na Falasdinu da aka mamaye.
Kakakin rundunar sojin kasar Birgediya Janar Yahya Sari’e ya tabbatar da cewa: “Ayyukan sun cimma nasarar cimma manufofinsu,” yana mai jaddada ci gaba da ayyukan bayar da tallafi har sai an daina kai hare-haren wuce gona da iri kan Zirin Gaza.
Sari’e ya ce: Ci gaba da aiwatar da shirin da makiya yahudawan sahayoniyya suke yi na da nufin kawar da al’ummar Falastinu ta hanyar kisan kiyashi da kakaba yunwa da tilasta musu gudun hijira daga mahaifansu zai haifar da mummunan sakamako ga dukkanin kasashen Larabawa da na musulmi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Wakilan Hamas sun isa Alkahira don shawarwarin tsagaita wuta a Gaza August 13, 2025 Iran: Amurka Da Isra’ila Ne Da Kansu Suka Bukaci Dakatar Da Bude Wuta August 13, 2025 Habasha: Madatsar ruwanmu amfanin dukkanin kasashen yankin ne August 13, 2025 Bankin Duniya Zai Kashe $300m Don Inganta Rayuwar ’Yan Gudun Hijira A Arewacin Nijeriya August 13, 2025 Nijeriya Da Isra’ila Na Kara Karfafa Alaka A Tsakaninsu August 13, 2025 Kasashe 27 Sun Bukaci Isara’ila Ta Kawo Karshen Hana Shigar Da Abinci A Gaza August 12, 2025 Iran: Duk Wani Sabon Hari, Zai Fuskanci Mummunan Martanin Soji August 12, 2025 Larijani: Iraki Ba Ta Karbar Umarni Daga Iran August 12, 2025 Iran: Ma’aikatar Harkokin Waje Ce Ke Kula Da Lamarin Makamashin Nukliyar Kasar August 12, 2025 Armenia Ta Tabbatarwa Iran Zata Kula Da Muradunta Bayan Yarjeniya Da Azarbaijan A Amurka August 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Gayyaci Mukaddashin Jakadan Kasar Oman Zuwa Ma’aikatar Harkokin Wajenta
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta gayyaci muqaddashin jakadan kasar Oman a kasarta
Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta gayyaci babban jami’in ofishin jakadancin kasar Oman a birnin Tehran a jiya Lahadi, bayan wani rade-radin da ake yadawa cewa; Mutane biyu a kasar Oman sun mutu sakamakon shan ruwan ma’adinai da aka shigo da su daga kasar Iran.
Bayan wasu zarge-zarge marasa tushe da wasu kafafen yada labarai na kasar Oman suka wallafa na alakanta mutuwar mutane biyu a masarautar Oman da shan ruwan ma’adinan da aka shigo da su daga kasar Iran, a ranar Lahadin da ta gabata ne Abdul Rasoul Shabibi, shugaban sashen ma’aikatar kula da tekun Farisa ta ma’aikatar harkokin wajen kasar ya gayyaci mai kula da ofishin jakadancin Oman a Tehran zuwa ma’aikatar harkokin wajen kasar.
Shugaban Sashe na biyu na yankin Tekun Fasha a ma’aikatar harkokin wajen kasar ya bayyana rashin amincewar kasar Iran a hukumance kan yadda kafafen yada labarai suka rika yada munanan kalamai dangane da ruwan ma’adinan da aka shigo da su daga kasar Iran, yana mai kira da a gaggauta yin karin haske kan lamarin. Ya kara da cewa bai dace a yi amfani da wani lamari da bai da alaka da ruwan sha da ake dangantawa da wani kamfanin kasar Iran, saboda lamarin yana da alaka da sabani a tsakanin wani dangi da ake kyautata zaton an kashe mutanen ne ta hanyar Sanya musu guba a abincinsu domin ramuwar gayya, sai aka danganta lamarin a matsayin wani tushe na bata sunan wani samfurin da aka shigo da shi daga kasar Iran.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Yemen Ta Gargadi Isra’ila Kan Fuskantar Hare-Hare Idan Ta Karya Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta October 13, 2025 Cibiyar Lafiya Ta Nasser Ta Ce: Yaran Gaza 5,500 Suna Bukatar Agajin Gaggawa A Kasashen Waje October 13, 2025 Shugaban Amurka Ya Yi Barazanar Aikewa Ukraine Makamai Masu Linzami Kirar Tomahawk October 13, 2025 Trump, da Al’Sisi za su jagoranci taron zaman lafiya kan Gaza October 12, 2025 ‘Yan Kamaru na kada kuri’a a zaben shugaban kasar October 12, 2025 Wata Kotu a Faransa ta yi watsi da rufe wata makarantar musulmi a birnin Nice October 12, 2025 Gwamnatin Cuba ta yi watsi da zargin da Amurka ke yi na hannu a yakin Ukraine October 12, 2025 Arachi: HKI Ba Abar Amincewa Ba Ce, Falasdinawa Su Yi Hattara October 12, 2025 Iran Ta Yi Allawadai Da HKI Kan Hare-Haren Da Take Kaiwa Kudancin Lebanon October 12, 2025 An Gudanar Da Taron ‘Farkawar Musulmi’ A Nan Tahren Inda Aka Tattauna Batun Falasdinu October 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci