ETFund Ta Koka Kan Gibin Da Ake Samu A Sashin Lafiyar Najeriya
Published: 13th, August 2025 GMT
Biyo bayan wani rahoto da ma’aikatar lafiya ta tarayya ta fitar na cewa sama da likitoci 16,000 ne suka bar Najeriya a cikin shekaru bakwai da suka gabata domin neman aiki a wasu kasashe, gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani sabon shiri na cike gurbin da likitocin suka haifar.
Da yake zantawa da manema labarai a Katsina, Shugaban Hukumar Kula da Ilimi ta Kasa (TETFund), Alhaji Aminu Bello Masari, ya ce hukumar ta kaddamar da wani shiri na musamman domin horar da karin likitoci, ma’aikatan jinya, masu harhada magunguna da kwararrun dakin gwaje-gwaje a manyan makarantun kasar nan.
Ya ce tuni hukumar ta TETFUND ta zuba sama da Naira biliyan 100 a manyan makarantu goma sha takwas domin kara karfinsu na horar da dalibai a fannin ilimin likitanci, ta hanyar samar da dakunan karatu, dakunan gwaje-gwaje da sauran abubuwan da suka shafi ababen more rayuwa da ilimi.
Masari ya ce, wannan matakin shiri ne don ba da damar tsarin kiwon lafiya ya farfado daga ficewar ma’aikatan lafiya tare da kara karfin ma’aikata a fannin.
Ya bayyana cewa an zabo manyan makarantu guda uku a kowace shiyyar siyasar kasar nan saboda kowace cibiya ta samu Naira biliyan 4 don gudanar da ayyuka da kuma sayan kayan aikin da ake bukata domin kara karfin daukar dalibai da horar da dalibai a fannin ilimin likitanci.
Masari ya bayyana cewa sun dauki matakin ne saboda muradin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na ganin an magance karancin ma’aikata a fannin kiwon lafiya da ke yin illa ga ayyukan hidima a fannin.
“A shekarun baya-bayan nan, likitoci da ma’aikatan jinya da yawa da masana harhada magunguna da kwararrun likitoci da sauran kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya sun bar kasar nan don neman aiki mai gwabi a kasashen waje.
Isma’il Adamu/Katsina
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Wakilai ta nemi gwamnati ta gaggauta dauko Jonathan daga Guinea Bissau
Majalisar Wakilai a ranar Alhamis, ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta yi amfani da diflomasiyya da duk wasu hanyoyi don tabbatar da dawowar tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan lafiya daga Guinea Bissau, bayan juyin mulkin sojoji a ƙasar.
Wannan kuduri ya biyo bayan amincewa da kudurin gaggawa da Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Farfesa Julius Ihonvbere, ya gabatar.
Ihonvbere ya shaida wa Majalisar cewa Jonathan, wanda ya je ƙasar domin sa ido kan zaɓe, ya makale bayan juyin mulkin, yana mai cewa gwamnati ta nemo hanyoyin da za su tabbatar da dawowarsa lafiya.
Muna tafe da karin bayani…