DAGA LARABA: Yadda sinadaran dandanon abinci ke yin illa ga lafiya
Published: 13th, August 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
A yau, yawancin mutane suna amfani da sinadaran dandano wajen girki domin ƙara wa abinci ɗanɗano da ƙamshi. Amma, binciken masana ya nuna cewa ana yawan amfani da su fiye da yadda ake bukata, musamman irin waɗanda aka sarrafa a masana’antu.
Wannan rashin kiyaye ƙa’ida yana iya jawo matsaloli ga lafiya.
Sau da yawa mutane kan manta cewa a cikin waɗannan sinadarai akwai gishiri mai yawa da wasu ƙarin abubuwan da idan aka tara su a jiki na dogon lokaci, suna iya haifar da illa.
NAJERIYA A YAU: Yadda matasa ke bayar da gudunmawa ga ci-gaban al’umma DAGA LARABA: Me Ke Sa Matasa Zama Karnukan Farautar ‘Yan Siyasa A Kafafen Sadarwa Na Zamani?Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan irin matsalolin da amfani da sinadarin dafa abinci fiye da kima ke jawowa ga lafiyar mutane.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Fursunoni 16 sun tsere daga gidan yarin Keffi
Ana fargabar cewa wasu fursunoni 16 sun tsere daga gidan yarin Keffi da ke Jihar Nasarawa bayan wani kwantan bauna da suka yi wa gandirebobi.
Wata sanarwa da mai magana da yawun Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali a Nijeriya, Umar Abubakar, ta ce fursunonin da ke gidan sun yi wa ma’aikatan da ke tsaronsu rubdugu, lamarin da ya bai wa mutane 16 damar guduwa a safiyar wannan Talatar.
An kama ɗan shekara 18 kan zargin fashi da makami a Gombe An kama basarake kan zargin yi wa ’yar shekara 12 fyaɗe a GombeSanarwar ta ce biyu daga cikin jami’ai biyar da suka ji rauni a yayin harin na cikin mawuyacin hali, kuma yanzu haka ana duba lafiyarsu a wani asibitin gwamnati.
Ya kara da cewa an kamo mutumin bakwai daga cikin waɗanda suka tsere yayin da ake ci gaba da neman ragowar fursunoni tara.
Sanarwar ta ambato cewa Kwanturola-Janar na Hukumar Gidajen Gyaran Hali a Nijeriya, NCoS, Sylvester Nwakuche, ya ziyarci wurin bayan faruwar lamarin, inda ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike tare da gargaɗin cewa duk wani ma’aikaci da aka samu da hannu zai kuka da kansa.
Haka kuma, Nwakuche ya ba da umarnin a gaggauta fita samamen haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin kamo waɗanda suka tsere.
Mahukunta sun yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu, tare da neman su hanzarta bayar da rahoton duk wani motsi ko alamar mutanen da suka tsere ga ofishin tsaro mafi kusa.
A ‘yan shekarun nan dai, an samu tserewar fursunoni a Nijeriya lokuta daban-daban, inda a bara kaɗai, fursunoni 118 sun tsere daga gidan gyaran hali na Suleja a Jihar Neja, bayan ruwan sama mai karfi ya lalata bangon gidan yarin da ake cewa daɗewarsa ce ta janyo rushewar ginin.