Majalisar dokokin jihar Kano ta karbi karin kudirin kasafin kudi na shekarar 2025 daga bangaren zartarwa na jihar domin tantancewa.

 

Bukatar, wacce aka mika ta wata wasika daga bangaren zartarwa, ta nemi amincewar majalisar ta kara kasafin kudi naira biliyan 169,522,463,294.82 domin daukar muhimman ayyukan raya kasa a fadin jihar.

 

Kakakin majalisar Alhaji Jibril Isma’il Falgore ya bayyana cewa hukumar zartaswa na kokarin ganin an kara wa kasafin kudin domin gudanar da ayyuka masu ma’ana da za su shafi rayuwar mazauna.

 

Bayan sun yi duba, ‘yan majalisar sun mika kudirin dokar ga kwamitin kasafin kudi na majalisar domin tantancewa da daukar matakin da ya dace.

 

A wani labarin kuma, Majalisar ta kuma samu takarda daga bangaren zartarwa na tantance Barista Saidu Yahaya a matsayin sabon shugaban hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC).

 

Nadin ya biyo bayan cikar wa’adin tsohon shugaban Barista Muhyi Magaji Rimin Gado.

 

An mika sunan ga kwamitin majalisar kan korafin jama’a don ci gaba da aiwatar da doka.

 

Majalisar ta dage zaman ta ne zuwa washegari sakamakon kudirin da shugaban masu rinjaye, Lawan Hussaini Dala ya gabatar.

 

COV/Khadija Aliyu08164127760

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

MDD za ta yi zaman gaggawa kan yunƙurin ƙwace Gaza

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kira taron gaggawa a wannan Lahadin domin tattauna ƙudirin Isra’ila na ƙwace iko da Zirin Gaza.

Wannan shirin, wanda Majalisar Tsaron Isra’ila ta amince da shi a ranar Juma’a, ya jawo suka daga ƙasashen duniya.

Al-Hilal ta ɗauki Nunez daga Liverpool Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram a Borno

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres ya kwatanta shirin da abin da zai ƙara dagula lamura a fadan da aka kwashe watanni 22 ana yi.

Kasashen Turai da ke cikin Kwamitin Sulhun da suka hada da Denmark da Faransa da Girka da Burtaniya da Slovenia ne suka kira wannan zaman gaggawan a birnin New York na Amurka.

DW ya ruwaito cewa, dukkan mambobin Kwamitin Sulhun banda Amurka sun goyi bayan wannan zaman na yau Lahadi wanda zai dubi abinda ya dace a yi a kan yunkurin na Isra’ila.

Za a fara zaman ne da misalin ƙarfe 10 na safe wato ƙarfe biyu kenan agogon GMT da Ghana.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Babban Sakataren Majalisar Kolin Tsaron Kasar Iran Ya Ce: ‘Yan Gwagwarmaya Sun San Abubuwan Da Suka Dace
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Sanar Da Mutuwan Mutane 60 Saboda Yunwa A El-Fasher Na Sudan
  • EFCC ta tsare tsohon Gwamnan Sakkwato Tambuwal kan zargin N189bn
  • Za a gyara tarbiyar tubabbun ’yan daban Kano
  • Majalisar Dokokin Kano Ta Karɓi Ƙarin Kasafin Kuɗi Na 2025
  • Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya Ya Gudanar Da Zaman Taro Kan Aniyar ‘Yan Sahayoniyya Kan Gaza
  • Inganta Harkokin Gwamnati: Oyebanji Ya Sauke Kwamishinoni 19
  • MDD za ta yi zaman gaggawa kan yunƙurin ƙwace Gaza
  • Sanatocin Da Ba Su Kawo Ƙudiri Ba Tun Bayan Ƙaddamar Da Majalisar Dattawa Ta 10