Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Ya Yi Bikin Easter Tare da Al’ummomin Kiristoci
Published: 19th, April 2025 GMT
Makera, Jihar Kaduna – Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Rt. Hon. Yusuf Dahiru Liman, ya halarci bukukuwan Easter tare da al’ummomin Kiristoci na Gundumar Makera, inda ya bukaci su yi amfani da lokacin wajen tabbatar sa saƙon bangaskiya, yabo, da sadaukarwa da ke tattare da bikin.
A jawabin da ya gabatar, Hon.
Kakakin ya kuma yi kira ga daukacin jama’ar Jihar Kaduna da su ci gaba da bunkasa zaman lafiya da juna ba tare da la’akari da bambancin addini, kabila ko ra’ayin siyasa ba, yana mai cewa hadin kai shi ne ginshikin ci gaban jihar da kasa baki daya. Ya jaddada bukatar gudanar da addu’o’i don dorewar zaman lafiya da inganta sha’anin tsaro.
A kokarinsa wajen inganta kiwon lafiya, Hon. Yusuf Dahiru Liman ya dauki nauyin mutane 200 da suka hada da tsofaffi da mabukata daga Kakuri-Gwari da unguwar Television domin shiga tsarin inshorar lafiya na KACHMA wanda ke ba da damar samun kulawar lafiya mai araha.
Baya ga hakan, Kakakin ya bayar da guraben karatu ga dalibai 200 daga wadannan al’ummomi domin tallafa musu a harkar ilimi da gina al’umma mai wayewa.
Bikin na Easter ya samu halartar shugabannin addini da sarakuna, shugabannin matasa da mata, da sauran manyan masu ruwa da tsaki na al’umma.
A nasa jawabin, Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Mr. James Kanyip ya yabawa nasarorin da aka samu wajen karfafa tsaro da inganta zaman tare a jihar. Ya bayyana cewa gwamnati na amfani da hanyoyin sasantawa da tattaunawa wajen magance matsalolin tsaro, tare da kira ga jama’a da su kasance masu lura da kuma sanar da hukumomi duk wani abin da ba su amince da shi ba.
Shugabannin al’umma su ma sun yi amfani da damar wajen yabawa Kakakin bisa kokarinsa na kawo ci gaba. Mista Monday Kazah daga Kakuri-Gwari da Mista Ishaya Amfani daga unguwar Television sun jinjinawa Hon. Liman saboda shirye-shiryensa na tallafawa jama’a ta hanyar bayar da guraben karatu, koyar da sana’o’i, da samar da ayyukan yi. Sun kuma tabbatar masa da goyon baya da addu’o’i domin samar da dokokin da za su bunkasa rayuwar jama’a.
Shamsuddeen Mannir Atiku
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Dalilin Da Ya Sa Hukumar NIWA Ta Fara Gyaran Hanyoyin Ruwa A Jihar Legsa
Manajar ofishin na NIWA, da ke a jihar ta Legas Injiniya Sarat Braimah ta bayyana cewa, tura ma’ikatan hukumar domin yin aikin, zai taimaka wajen gudanar da aikin a cikin inganci.
Kazalika, ya sanar da cewa, hakan zai kuma bayar da damar yin safarar kaya a cikin sauki da kuma safarar matafiya da ke bin hanyar ruwa ta yankin na Ikorodu.
“Mun yi nazari a cikin kwanciyar hankali kan yadda za a tabbatar da an cire fulawar da ke a cikin kasan ruwan ba tare da wata miskila ba tare da kuma bai wa jiragen ruwan damar yin zirga-zirgarsu a hanyoyin ruwan, ba tare da wata matsala ba, “ Inji Injiya Braimah.
“ Aikin ya wuce batun fannin samar da saukin yin sufurin jiragen ruwan har da tabbatar da an kiyaye janyo matsala ga ayyukan kamun Kifi a hanyoyin na ruwan, “ A cewar Inji Manajar.
Ta kara da cewa, babban shugabanmu na hukumar ta NIWA, Bola Oyebamiji, ne tuni ya riga ya bayar da kwangilar yin aikin, ba wai a jihar Legas kawai ba, har da a sauran hanyoyin ruwa da ke a sassan kasar.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA