Rundunar ‘Yan Sandan Kano Ta Yi Gargadi Game Da Sabawa Dokokin Fitillun Bada Hannu A Titinan Jihar
Published: 12th, August 2025 GMT
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayar da gargadi game da hawan keken masu kananan shekaru da rashin biyayya ga fitilun ababen hawa a cikin babban birnin Kano.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanya wa hannu, kuma aka rabawa manema labarai a Kano.
Gargadin na zuwa ne bayan an samu munanan hadurran kan tituna guda 16 a cikin watan Agustan 2025, wanda ya yi sanadin jikkata da asarar dukiyoyi.
Rundunar ta lura cewa hawan keken ƙananan yara yana haifar da babban haɗari ga mahaya da sauran masu amfani da hanyar.
An shawarci iyaye da masu kula da su da su guji barin ‘ya’yansu da ba su da shekaru su yi amfani da keken mai kafa uku, domin hakan zai jawo hukunci mai tsanani a karkashin dokar.
Rundunar ta kuma lura da yanayin rashin biyayya ga fitilun ababen hawa da kuma dokokin hanya daga wasu masu amfani da hanyar.
“Wannan dabi’a tana haifar da cunkoson ababen hawa da ba dole ba, da kuma hadurran da za a iya kaucewa, da jefa rayukan mutane cikin hadari da kuma kawo cikas ga zirga-zirgar ababen hawa.”
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kebe jami’an tsaro domin tabbatar da bin ka’idojin zirga-zirga.
Rundunar ta bukaci duk ‘yan kasar da su bi dokokin hanya da kuma bayar da rahoton duk wani abu na hawan keken kanana, tukin ganganci, ko wasu keta haddi.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya tabbatar wa jama’a cewa rundunar ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaro na rayuka da dukiyoyi a jihar.
Abdullahi jalaluddeen/Kano
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Fitillun hanya ababen hawa Rundunar ta
এছাড়াও পড়ুন:
Ahmed Musa Ya Nemi Afuwar Ƙungiyar 3SC Akan Abinda Ya Faru Da ‘Yan Wasansu A Kano
Sanarwar ta kara da cewa, “mun yi farin cikin ganin cewar yan wasan kungiyoyin biyu da jami’an wasan duk sun bar filin wasan ba tare da samun wani rauni ba kuma jami’an tsaro suka yi musu rakiya, kungiyar ta kara da cewa an kama wasu da dama da ake zargi da hannu a rikicin tare da mika su ga hukumomin tsaro domin gudanar da bincike tare da gurfanar da su gaban kuliya.
Kungiyar ta jaddada kudirinta na tabbatar da zaman lafiya da da’a, kungiyar ta jaddada cewa za ta ci gaba da tabbatar da ingancin wasan kamar yadda hukumar NPFL da hukumar kwallon kafar Najeriya NFF ta tanada, Pillars ta kuma yi kira ga magoya bayanta da su gudanar da ayyukansu cikin lumana tare da ci gaba da ba kungiyar goyon baya, amma kuma wani bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yan wasan 3SC da aka jikkata tareda raunuka a jikinsu.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA