2025-08-12@17:05:30 GMT
إجمالي نتائج البحث: 15

«waɗanda suka yi nasara»:

    Sakamakon wannan mummunan ta’annuti, Mataimakin Gwamnan ya jagoranci wata ƙaƙƙarfar tawaga, wacce ta haɗa manyan ma’aikatan gwamnati da jami’an tsaro zuwa Banga da sauran wurare uku da waɗannan hare-hare ya shafa, don a jajanta masu, tare da ba su tallafi na abinci da kuɗaɗe.   Mataimakin Gwamnan ya kuma tabbatar wa da waɗannan al’ummu cewa gwamnatin na nan tana duk abin da za ta iya yi don kawo dawwamammen zaman lafiya a yankin.   Lokacin da ya ke mayar da jawabi, shugaban Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda, Manir Haidara ya yaba da ƙoƙarin gwamnatin jihar na ganin ta samar da tsaro a duk faɗin jihar Zamfara. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Filato a ranar Alhamis ta gurfanar da wasu mutane 22 da ake zargi da kashe matafiya bikin aure da a unguwar Mangun da ke Ƙaramar hukumar Mangu ta Jihar Filato. An kashe mutum 13 daga cikin matafiyan, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon harin da wasu da ake zargin ’yan daba ne suka kai lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa unguwar Qua da ke ƙaramar hukumar Qua’an Pan ta Jihar Filato. ’Yan sanda sun ƙaddamar da sabon samame, sun kama mutum 98 a Kano Jami’ar Tarayya ta Gashuwa za ta ba matar Tinubu digirin girmamawa Adadin waɗanda aka kashe mutum 32 da suka haɗa da maza da mata da ƙananan yara suna cikin...
    Rahoton LEADERSHIP ya tabbatar da cewa wannan ikirari ƙarya ne. Bincike ya nuna cewa ba wanda aka sace daga cikin mutanen da ke bidiyon yana da alaƙa da Gwamna Dauda Lawal. Haka kuma, binciken ya nuna cewa ƴar uwar Gwamnan da aka sani mace ce, ba namiji ba. Hakanan, mutumin da ke cikin bidiyon na bayyana cikin tsananin firgici da damuwa, alamar cewa yana fuskantar tilas daga barayin daji da suka umurce shi da ya faɗi abin da suke so. Da yake martani kan bidiyon, mai magana da yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa wannan wata sabuwar dabara ce da ɓarayin suka bullo da ita don jawo hankali. Ya ce, “Idan aka kalli bidiyon da kyau,...
    A karon farko Nijeriya za ta fara fitar da tataccen man fetur zuwa nahiyyar Asia kamar yadda wata majiya daga Matatar Dangote ta sanar. Majiyar ta ce wani jirgin ruwan dako mai ɗauke da tan 90,000 na man fetur zai yi jigilar daga Matatar Dangote da ke Nijeriya zuwa nahiyar Asia. HOTUNA: Yadda Tinubu ya ziyarci waɗanda suka jikkata a harin Benuwe Hare-haren Benuwe: Tinubu ya ziyarci waɗanda suka jikkata a asibiti  Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ambato majiyar wadda ta buƙaci a sakaya sunanta tana cewa “yanzu jirgin ruwan Mercuria zai tafi Asia a ranar 22 ga Yuni.” “Muna sayar da kayanmu ne ga waɗanda suka yarda su ba mu farashi mafi yawa. Mai saye na da haƙƙin...
    Hukumar Kula da Yanayi (NiMet), ta sake fitar da gargaɗi game da yiwuwar ambaliyar ruwa a wasu jihohin a daminar bana. A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, hukumar ta bayyana cewa Jihar Akwa Ibom ce ke fuskantar barazana mafi tsanani a halin yanzu. Gwamnan Kaduna ya bai wa sabon Sarkin Moro’a sandar mulki Farashin fetur ya tashi a kasuwar duniya bayan harin Isra’ila a Iran Sauran jihohin da abin ka iya shafa sun haɗa da Sakkwato, Zamfara, Filato, Yobe, Bauchi, Bayelsa, Nasarawa, Binuwai, Ogun, Ekiti, Delta da kuma Ribas. NiMet ta shawarci al’umma, musamman waɗanda ke zaune a cikin waɗannan jihohin, da su tabbatar sun yashe magudanan ruwa domin bai wa ruwa hanyar wucewa. Haka kuma...
    Rundunar ’yan sanda a Jihar Taraba ta cafke mutane tara kan zargin satar mutane. Haka kuma, rundunar ta gano bindigogi ƙirar AK-47 guda huɗu da kuma bindigogi ƙirar AK-49 guda uku da alburusai guda arba’in da biyar a hannun waɗanda aka cafke. Dalilin faɗuwar farashin kayan abinci a kasuwannin Arewa Ƙungiyoyin da suka yi shuhura a Firimiyar Ingila Kakakin rundunar ’yan sandan, ASP James Lashen ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a birnin Jalingo. Ya bayyana sunayen ababen zargin da aka kama da suka haɗa da Shehu Ibrahim da Abdullahi Haruna da kuma Yusuf Bello. Sauran kuma sun haɗa da Sulaiman Muhammed da Tijjani Bello da Muhammed Umar. Kazalika, akwai kuma Adamu Ibrahim...
    Sanarwar ta ƙara da cewa, ’yan kasuwa 1,000 za su samu jarin fara aiki na Naira 150,000 kowannensu, da nufin sauya akalar kasuwancin su zuwa sana’o’i na zamani a faɗin Jihar Zamfara.   A nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada cewa bayan hawansa mulki, gwamnatinsa ta bullo da shirye-shiryen ƙarfafawa da dama tare da samar da damarmaki don cimma manufofinsa na ceto.   “Waɗannan tsare-tsare ba wani kebantaccen abu ba ne, wani ɓangare ne na babban burinmu wajen samar da jihar Zamfara mai albarka don haɗa abokan hulɗa don magance ɗimbim matsalolin zamantakewa da tattalin arziki. “Yawancin tsare-tsare na rage raɗaɗin talauci da wannan gwamnati ta bullo da su sun yi tasiri ga rayuwar dubban ‘yan jihar, ƙudirin...
    Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Neja ta kaddamar da rabon sutura da jakunkunan hannu masu nauyin kilo 8 ga maniyyatan bana, a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen aikin Hajji na shekarar 2025. A lokacin da yake jawabi yayin kaddamar da rabon, Shugaban Hukumar, Sheikh Muhammad Awwal Aliyu, ya bayyana cewa rabon kayayyakin na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da sauƙin tafiya da kuma aikin Hajji ba tare da wata tangarda ba ga maniyyatan jihar. Shugaban wanda Daraktan Gudanarwa, Babani Aliyu Yahaya, ya wakilta a yayin bayar da kayan ga Jami’in Alhazai na Ƙaramar Hukumar Chanchaga, ya ce kayayyakin na maniyyatan  da suka kammala biyan kuɗin kujerunsu ne. Daraktan Gudanarwar ya kuma yi kira ga waɗanda har yanzu ba su...
    Rahotanni sun ce an kashe wani uba da ‘ya’yansa biyu a ƙauyen Zogu da ke Gundumar Miango a Ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Filato. Kakakin Ƙungiyar ci gaban Irigwe (IDA), Sam Jugo, wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Jos, ya bayyana sunayen waɗanda harin ya rutsa da su kamar haka, Weyi Gebeh a mai shekara 56, da Zhu Weyi mai shekara 25 da Henry Weyi mai shekara 16. ‘Tell Your Papa’: NBC ta haramta amfani da waƙar da ke sukar Tinubu An kama mutum 8 kan faɗan daba a Kano A cewar Jugo, an kashe mutanen ne cikin dare a lokacin da suke barci, inda ya bayyana lamarin a matsayin dabbanci. Ya ce, “An sanar da shugabannin...
    Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin, ya ziyarci iyalan mafarauta 16 da aka kashe a yankin Uromi da ke Jihar Edo, tare da ba su tallafin Naira miliyan 16. Matan matatan sun fito ne daga ƙananan hukumomin Bunkure, Kibiya, Rano, da Garko a Jihar Kano. Mutum 2 sun rasu, 13 sun ɓace a hatsarin jirgin ruwa a Bayelsa HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Galadiman Kano Barau ya gana da iyalan mamatan a Masallacin At-Taqwa da ke Bunkure a ranar Laraba tare da Ministan Harkokin Gidaje, Yusuf Abdullahi Ata da sauran manyan jami’ai. Barau, ya yi ta’aziyya da kuma tabbatar da cewa waɗanda suka aikata laifin za su fuskanci hukunci. “Na zo nan ne domin na taya ku jaje kan...
    Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da takwaransa na Jihar Edo Monday Okpebholo, sun ziyarci garin Torankawa da ke Kano domin jajanta wa iyalai da yan uwan mafarautan nan guda 16 da aka kashe a Jihar Edo. Gwamnonin biyu sun ziyarci garin ne da manufar tabbatar wa da iyalan waɗanda lamarin ya shafa cewa lallai gwamnatin jihar Edo za ta hukunta waɗanda suka yi wannan aika-aika sannan kuma gwamnatin za ta biya su diyya. Ta zuba wa abokan aikinta guba bayan taƙaddama kan ƙarin matsayi Mene ne matsayin azumin Sitta Shawwal a Mazhabar Malikiyya “Wannan ziyara ba kawai ta jaje da ta’aziyya ba ce, a’a ta nuna tabbacin ƙoƙarin samar da adalci. “Iyalan waɗannan mamata na buƙatar abin da ya...
    Har yanzu dai kisan wasu matafiya ’yan Arewa da aka yi a garin Uromi da ke Ƙaramar Hukumar Arewa maso Gabashin Esan na ci gaba da tayar da ƙura a faɗin Nijeriya. A bayan nan ne wasu hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta suka nuna wasu mutane ɗauke da makamai suna far wa matafiyan da suka taso daga Kudanci zuwa Arewacin Nijeriya. Hotunan bidiyon sun nuna yadda aka yi wa waɗanda abin ya shafa jina-jina sannan aka cinna musu wuta suka ƙone ƙurmus. Za mu tura tawaga ƙauyen Torankawa —Gwamnatin Kano Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa zai tura tawaga ta musamman zuwa ƙauyen Torankawa domin jajanta wa iyalan mafarautan da aka kashe a Jihar...
    ’Yan kasuwa da abokan hulɗa da dama sun jikkata yayin da gubar harsashi ta tarwatse wannan Talatar a Jihar Zamfara. Aminiya ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a babbar kasuwar garin Talatan Mafara wadda ke ci duk ranar Talata. Galibi waɗanda lamarin ya rutsa da su ’yan kasuwar ne da kuma wasu abokan hulɗarsu da suka samu ƙonuwa da raunika daban-daban. Hotuna da wakilinmu na naɗa ya hasko waɗanda lamarin ya shafa suna kwance ana kawo musu agaji, inda galibi sun ƙone a ƙafafu da cinya har zuwa mazaunai.  
    ’Yan sanda sun yi nasarar kama wasu mutane biyu da ake zargi da laifin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 12 fyaɗe a kauyen Jalingo da ke Ƙaramar Hukumar Tarmuwa a Jihar Yobe. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Dungus Abdulkarim, ya fitar a Damaturu ranar Litinin. Gwamnati ta raba wa mata tallafin awakai na N5bn a Katsina Yadda na yi wa budurwar da muka haɗu a Facebook gunduwa-gunduwa —Matashi Ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:30 na yammacin ranar 15 ga watan Fabrairu, inda waɗanda ake zargin suka kai yarinyar wani kango a jeji suka keta mata haddi. Rahoton na cewar, “Hedikwatar ‘yan sandan jihar reshen Ƙaramar Hukumar...
    Wata gobara da ta tashi a wata makarantar tsangaya da ke Ƙaramar Hukumar Kaura-Namoda a Jihar Zamfara, ta yi ajalin almajirai 17. Dukkanin almajiran sun ƙone ƙurmus, ta yadda ba a gane kowa a cikinsu ba. Saura ƙiris Bello Turji ya zo hannu – Ministan Tsaro Tinubu ya ƙara kasafin kuɗin 2025 zuwa N54.2trn Shaidu sun bayyana cewa gobarar ta farq ne cikin daren ranar Talata, kuma ta ɗauki kimanin sa’o’i uku tana ci. Rahotanni sun bayyana cewar wasu almajirai 16 sun samu munanan raunuka a gobarar. Wani mazaunin yankin, Abdulrasaq Bello Kaura, ya bayyana cewa gobarar ta fara ne sakamakon kamawar wasu itatuwa da aka ajiye. Wani ganau ya shaida cewar, “Abin ya faru ne a makarantar Malam Ghali,...
۱