Sakataren Majalisar Kolin Tsaron Kasar Iran Ya Jaddada Kasancewar Iran Tare Da Kasar Lebanon Koda Yaushe
Published: 13th, August 2025 GMT
Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya bayyana cewa: Iran za ta kasance tare da al’ummar Lebanon a koyaushe
Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya tabbatar da cewa: Alakar al’adu tsakanin Iran da Lebanon ta taimaka wajen karfafa alaka tsakanin al’ummomin kasashen biyu.
Larijani ya kara da cewa: Iran da Labanon suna da dadaddiyar wayewa, kuma a ko da yaushe akwai alaka ta kut-da-kut a tsakanin al’ummomin kasashen biyu. Ya kara da cewa, wannan alaka ta al’adu ta haifar da alaka ta musamman tsakanin al’ummomin kasashen biyu, ta yadda a lokacin da al’ummar kasar Labanon ke cikin wahala, al’ummar Iran su ma suna jin wannan zafi.
Haka nan kuma ya bayyana aniyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran na tsayawa tsayin daka a kan al’ummar kasar Lebanon a kowane hali, yana mai jaddada muhimmancin hadin kai da hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu wajen fuskantar kalubalen da suke fuskanta.
Da yake karkare jawabinsa, Larijani ya bayyana muhimmancin tarukan da zai yi a yau Laraba tare da shugaban kasar, da shugaban majalisar dokoki, da fira minista, da kuma wasu ‘yan siyasar kasar ta Lebanon.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kasar Iraki Ta Ce: Yarjejeniyar Da Ta Kulla Da Iran Zai Amfani Dukkan Kasashen Yankin August 13, 2025 Sojojin Yemen Sun Kai Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’Ila Har Sau Shida August 13, 2025 Wakilan Hamas sun isa Alkahira don shawarwarin tsagaita wuta a Gaza August 13, 2025 Iran: Amurka Da Isra’ila Ne Da Kansu Suka Bukaci Dakatar Da Bude Wuta August 13, 2025 Habasha: Madatsar ruwanmu amfanin dukkanin kasashen yankin ne August 13, 2025 Bankin Duniya Zai Kashe $300m Don Inganta Rayuwar ’Yan Gudun Hijira A Arewacin Nijeriya August 13, 2025 Nijeriya Da Isra’ila Na Kara Karfafa Alaka A Tsakaninsu August 13, 2025 Kasashe 27 Sun Bukaci Isara’ila Ta Kawo Karshen Hana Shigar Da Abinci A Gaza August 12, 2025 Iran: Duk Wani Sabon Hari, Zai Fuskanci Mummunan Martanin Soji August 12, 2025 Larijani: Iraki Ba Ta Karbar Umarni Daga Iran August 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Larijani ya
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Yemen Sun Kai Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’Ila Har Sau Shida
Sojojin Yemen sun sanar da cewa: Sun kai hari kan muhimman wurare hudu na haramtacciyar kasar Isra’ila da jirage marasa matuka guda shida
Sojojin Yemen sun sanar a yammacin jiya Talata cewa: Sun kai farmakin soji ta hanyar amfani da jiragen sama marasa matuka ciki guda shida, inda suka kai hari kan wasu muhimman wurare 4 na haramtacciyar kasar Isra’ila a yankunan Haifa, Negev, Umm al-Rashrash, da kuma Bi’ersheba na Falasdinu da aka mamaye.
Kakakin rundunar sojin kasar Birgediya Janar Yahya Sari’e ya tabbatar da cewa: “Ayyukan sun cimma nasarar cimma manufofinsu,” yana mai jaddada ci gaba da ayyukan bayar da tallafi har sai an daina kai hare-haren wuce gona da iri kan Zirin Gaza.
Sari’e ya ce: Ci gaba da aiwatar da shirin da makiya yahudawan sahayoniyya suke yi na da nufin kawar da al’ummar Falastinu ta hanyar kisan kiyashi da kakaba yunwa da tilasta musu gudun hijira daga mahaifansu zai haifar da mummunan sakamako ga dukkanin kasashen Larabawa da na musulmi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Wakilan Hamas sun isa Alkahira don shawarwarin tsagaita wuta a Gaza August 13, 2025 Iran: Amurka Da Isra’ila Ne Da Kansu Suka Bukaci Dakatar Da Bude Wuta August 13, 2025 Habasha: Madatsar ruwanmu amfanin dukkanin kasashen yankin ne August 13, 2025 Bankin Duniya Zai Kashe $300m Don Inganta Rayuwar ’Yan Gudun Hijira A Arewacin Nijeriya August 13, 2025 Nijeriya Da Isra’ila Na Kara Karfafa Alaka A Tsakaninsu August 13, 2025 Kasashe 27 Sun Bukaci Isara’ila Ta Kawo Karshen Hana Shigar Da Abinci A Gaza August 12, 2025 Iran: Duk Wani Sabon Hari, Zai Fuskanci Mummunan Martanin Soji August 12, 2025 Larijani: Iraki Ba Ta Karbar Umarni Daga Iran August 12, 2025 Iran: Ma’aikatar Harkokin Waje Ce Ke Kula Da Lamarin Makamashin Nukliyar Kasar August 12, 2025 Armenia Ta Tabbatarwa Iran Zata Kula Da Muradunta Bayan Yarjeniya Da Azarbaijan A Amurka August 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci