2025-08-12@09:26:06 GMT
إجمالي نتائج البحث: 763

«domin amsa tambayoyi»:

    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) murna bisa ci gaba da riƙe matsayin Maturity Level 3 (ML3) na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) wajen kula da magunguna da rigakafi. Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Bayani da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, a cikin wata sanarwa, ya bayyana cewa, an gudanar da binciken sake tantance matsayin WHO daga 28 zuwa 30 ga Mayu, 2025, inda aka kimanta NAFDAC bisa ka’idojin ƙasa da ƙasa. Hukumar ta fara samun wannan matsayi na ML3 ne a 2022, inda ta zama hukumar farko a Afrika mai kula da ƙasashen da ba sa samar da magunguna da ta cimma wannan nasara. Wannan sabon...
    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC) ta yi wa tsohon gwamnan Jihar Sokoto, Sanata Aminu Tambuwal, tambayoyi kan zargin fitar da wasu kuɗi har Naira biliyan ₦189 ta hanyar cire kuɗin daga banki. Rahotanni sun nuna cewa, Tambuwal ya isa shalƙwatar EFCC a Abuja da misalin karfe 11:30 na safiyar yau Litinin, inda yake ci gaba da fuskantar tambayoyi daga jami’an bincike kan zargin. Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a tabbatar ko za a tsare shi ba na dogon lokaci ba. Ku Yaƙi Cin Hanci Ba Ƴan Adawa Ba – ADC GA EFCC EFCC Ta Kama Mutane 11 Kan Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Akwa Ibom Majiyoyi daga EFCC sun tabbatar da...
    Kasashen Turai biyar na kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya sun ki amincewa da matakin mamaye Gaza Wakilin dindindin na Slovenia ya gabatar da wata sanarwa ga kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya a madadin Burtaniya, Faransa, Denmark, da Girka, yana mai cewa: “A matsayinsu na kasashen Birtaniya, Denmark, Faransa, Girka, da Slovenia, sun kira taron gaggawa na kwamitin tsaron Majalisar kan halin da ake ciki a Gaza. Suna Allah wadai da matakin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta dauka na fadada ayyukanta na soji a Gaza. Ya kuma jaddada cewa: Hakan yana barazana tare da keta dokokin kasa da kasa, yana mai kiran gwamnatin mamayar Isra’ila da ta hanzarta janyewa daga wannan matsayi.  Ya jaddada cewa: Duk wani matakin mamaye yankunan Falasdinawa...
    Mahalarta taron masu ruwa da tsaki na yini daya don tabbatar da sakamakon bincike kan al’amuran zamantakewa da suka shafi ilimin ‘ya’ya mata a jihar Zamfara, sun bukaci iyaye, shugabannin al’umma, da gwamnati a dukkan matakai da su magance matsalolin da ke hana yara mata zuwa kammala karatun sakandare.   Kungiyar AGILE da ke Jihar Zamfara tare da hadin gwiwar Media and Publicity Consult ta shirya taron masu ruwa da tsaki na rana daya domin tabbatar da sakamakon binciken da aka yi kan ka’idojin zamantakewa da ke kawo cikas ga ’yan mata matasa da ke hana shiga makarantun gaba da sakandare a jihar Zamfara.   Da yake jawabi a wajen taron, Farfesa Abubakar Aliyu Liman na Jami’ar Ahmadu Bello da...
    Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da zaman gaggawa a hedikwatar MDD da ke birnin New York a jiya Lahadi, bayan matakin da majalisar ministocin Isra’ila ta dauka na fadada ayyukan soji da kuma mamaye yankin zirin Gaza. Mataimakiyar  Sakatare-Janar mai kula da harkokin Turai, Tsakiyar Asiya da Amurka, Miroslav Jenča, ta jaddada a yayin zaman  cewa, “ba za a iya dakatar da dimbin wahalhalun jin kai da ake fama da su a Gaza ba, sai ta hanyar tsagaita bude wuta nan take kuma mai dorewa,” tana mai kira da a gaggauta sakin dukkan fursunoni ba tare da wani sharadi ba. Jenča ta yi kira ga Isra’ila da ta bi abin da ya rataya a wuyanta a karkashin...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da matakin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta dauka na mamaye zirin Gaza Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da matakin baya-bayan nan da majalisar ministocin gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta dauka na mamaye yankin zirin Gaza da korar al’ummarta, tare da la’akari da hakan a matsayin wani mataki na kammala shirin kisan gillar ga Falasdinawa da suke yi da kawar da asalin wanzuwar Falastinu. A cikin bayanin da ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar dangane da abubuwan da suke faruwa a zirin Gaza da yankunan Falastinu da aka mamaye, ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana matukar damuwarta da takaicin yadda ake ci gaba da...
    Jami’in ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa; Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 Ali Baqiri Kani mamba a majalisar tsare-tsaren a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa da yahudawan sahayoniyya. Baqiri ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi ta gidan talabijin a yammacin jiya Asabar cewa: Tabbas Iran ta cimma matsayi sosai a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa, yana mai jaddada muhimmancin diflomasiyya wajen tunkarar hare-haren da ake kai wa kasar, yana mai jaddada cewa: “Dole ne Iran ta mayar da martanin wuce gona da iri...
    Jami’in ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa; Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 Ali Baqiri Kani mamba a majalisar tsare-tsaren a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa da yahudawan sahayoniyya. Baqiri ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi ta gidan talabijin a yammacin jiya Asabar cewa: Tabbas Iran ta cimma matsayi sosai a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa, yana mai jaddada muhimmancin diflomasiyya wajen tunkarar hare-haren da ake kai wa kasar, yana mai jaddada cewa: “Dole ne Iran ta mayar da martanin wuce gona da iri...
    Dubban mutane sun fito kan tituna a faɗin Isra’ila, don adawa da matakin gwamnatin ƙasar na faɗaɗa farmakin sojin da take a Gaza. A ranar Juma’a ne majalisar tsaron Isra’ila ta amince da sharuɗa biyar na kawo karshen yaƙin, ciki har da shirin karɓe iko da Birnin Gaza, inda sojojin Isra’ilar suka ce za su “shirya karɓe iko” da Gaza baki ɗayanta. Masu zanga-zangar da suka haɗa da iyalan mutum 50 ɗin da ake garkuwa da su a Gaza – ciki har da 20 ɗin da ake kyautata zaton suna raye, suna fargabar cewa shirin zai saka rayuwar ƴan uwansu cikin haɗari, inda suka buƙaci gwamnatin Isra’ila da ta yi ƙoƙarin don ganin an sake su. Shugabannin Isra’ila sun yi...
    Wani lokacin, yanayin shekaru da Jinsin Jini ne ke fayyace irin girma ko ƙantantar Ƙwan da Kajin za su yi. 2- Wajen Kwana: Kajin na buƙatar a tabbatar da ana samar musu da wadataccen ruwan sha a ɗakunan kwanansu da kuma ba su kariya daga kamuwa da cutuka da rage musu wahala da cunkoso da kuma zafi, wanda hakan na iya shafar Ƙwan da za su yi kai tsaye. 3- Abinci Mai Gina Jiki: Ciyar da su abinci mai gina jiki, wanda ke ɗauke da sinadaran ‘protein, amino acids’, waɗanda za su sanya su yi nauyi tare kuma da buƙatar a riƙa yi musu allurar ƙara musu lafiya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
    Manchester United sun kammala sayen ɗan wasan gaba na RB Leipzig, Benjamin Sesko, a kan kuɗi kimanin fam £73.7 miliyan. Sesko, ɗan ƙasar Slovenia mai shekaru 22, ya rattaba hannu kan kwangilar shekaru biyar tare da ƙungiyar. An biyan £66.3m kai tsaye, yayin da sauran kuɗin zai kasance a matsayin ƙari (add-ons). Wannan shi ne sayen ɗan wasa na uku a ɓangaren gaba da United suka yi a wannan kakar, bayan sayen Matheus Cunha a kan fam £62.5m da Bryan Mbeumo a fam £65m, wanda £6m na ƙari ne. Dukansu an gabatar da su ga magoya bayan ƙungiyar kafin wasan wasannin shirin kakar a gida da Fiorentina ranar Asabar. Manchester United Da Everton Na Zawarcin Wilfred Ndidi Sin Ta Gabatar...
    Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Shirin gwamnatin mamayar Isra’ila shi ne shirin share al’umma Falasdinu daga kan doron kasa Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana cewa: Shirye-shiryen da gwamnatin ‘yan sahayoniyya take yi na mamaye yankin Zirin Gaza da kuma tilastawa al’ummar yankin gudun hijira wani karin shaida ne na musamman da wannan gwamnatin take da niyyar aikata kisan kiyashi a Falastinu da ta mamaye. Ismail Baqa’i ya bayyana shirin gwamnatin ‘yan sahayoniyya na mamaye garin Gaza da sojoji da kuma tilastawa mazauna yankin kauracewa gidajensu a matsayin wani shiri na kammala kisan gillar da  take yi wa al’ummar Falastinu, yana mai jaddada tofin Allah tsine da Allah wadai da wannan mummunan cin zarafi....
    Kwamandan Dakarun Qudus na Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa: Gudun da Amurka ta yi daga Yemen wani shan kaye na soji da ba a taba ganin irin sa ba Kwamandan Dakarun Quds na Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Ismail Qaani, ya kaddamar da wani kakkausar suka kan Amurka, yana mai bayyana sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na janyewa daga fagen daga a Yemen a matsayin “Halayen soja mafi wulakanci da kunya” a tarihin Amurka. A cewar wani faifan bidiyo da kafar yada labaran “Dakarun Qudus” suka wallafa a shafinsu na Telegram, Birgediya Qaani ya ce: Shugaban Amurka Donald Trump, da kansa ba wani ba—ba kawai kakakin...
    Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira da a gaggauta janye shirin gwamnatin mamayar Isra’ila na mamaye Gaza Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya soki shirin gwamnatin mamayar Isra’ila na kwace iko da birnin Gaza a jiya Juma’a, inda mai magana da yawunsa ya bayyana matakin a matsayin wani abu mai hadari. A nasa bangaren, Volker Turk, babban jami’in kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya, ya yi kira a jiya Juma’a da a dakatar da shirin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da ke da nufin wanzar da cikakken ikon soji a zirin Gaza ta hanyar mamaya. A cikin wata sanarwa da ta fitar sa’o’i kadan bayan da majalisar ministocin tsaron gwamnatin mamayar Isra’ila ta amince da kudurin...
    Fitattun matsayi na kasashen Larabawa da kungiyoyi sun yi Allah wadai tare da tofin Allah tsine da matakin gwamnatin mamayar Isra’ila na mamaye Gaza Kasashe da kungiyoyin Larabawa sun yi Allah wadai da matakin da majalisar ministocin gwamnatin mamayar Isra’ila ta dauka mai hatsari na sake mamaye yankin Zirin Gaza tare da tilastawa Falasdinawa kusan miliyan daya gudun hijira daga birnin Gaza da arewacin zirin Gaza zuwa kudancin kasar. A cikin sanarwar da suka fitar a jiya Juma’a, sun yi la’akari da wannan shawarar da kuma shirin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi a matsayin mai hatsarin gaske da zai haifar da bala’in jin kai a zirin Gaza kuma ba za ta taimaka wajen kawo karshen rikicin ba, suna masu...
    “Kuma za a yi hakan ne saboda a matsayinmu na al’umma, muna ci gaba da ƙoƙarin canza abubuwan da ‘yan siyasa ba sa son canzawa,” in ji shi. Ya kuma bayyana cewa ba yau aka fara aikin gyaran kundin tsarin mulkin ƙasar kan batun cin gashin kan ƙananan hukumomi ba. Ejah ya ƙara da cewa ana sa ran kashi biyu cikin uku na ‘yan majalisar wakilai za su kaɗa ƙuri’ar amincewa ko kuma ƙin amincewa da gyaran. Ya ƙara da cewa gwamnatin Bola Tinubu ta bayar da umarnin ne kawai, biyo bayan hukuncin da kotun ƙoli ta yanke, cewa a biya kason kuɗaɗen da majalisun za su samu kai tsaye a asusunsu. A cewarsa, wannan ba gyara ba ne, domin...
    Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya sanar a yau jumma’a cewa Jamus za ta dakatar da duk wani izinin fitar da kayan aikin soji da za a iya amfani da su a zirin Gaza, biyo bayan matakin Isra’ila na mamaye Gaza. Da yake magana bayan zaman majalisar ministoci ta Isra’ila da kuma amincewarta da shirin kwace birnin Gaza tare da mamaye shi, Shugaban gwamnatin Jamus Merz ya ce Berlin na ci gaba da ba da goyon baya ga ‘yancin “Isra’ila” na kwance damarar Hamas tare da ganin an sako fursunoni, amma kuma duk da haka basu goyon bayan duk wani mataki zai kai ga kara tabarbarewar lamurra na jin kai a Gaza. “Gwamnatin Jamus ta yi imanin cewa matakin soji...
    Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce kasarsa ta kammala shirin amfani da sojoji wajen mamaye ilahirin Zirin Gaza na Falasdinawa domin ya koma karkashin ikonta. A cikin wata sanarwa da ofishinsa ya fitar da safiyar Juma’a, Netanyahu ya tabbatar da shirin inda ya ce, “Sojojin Isra’ila za su shirya karbe iko da Zirin Gaza baki daya sannan a samar wa fararen hula agaji a wajen yankunan da ake gwabza yaki.” Tinubu zai kashe tiriliyan 1.5 wajen gina layin dogo na zamani a birnin Kano NAHCON ta ƙayyade N8.5m kafin alƙalami na kujerar Hajjin 2026 Kazalika, wasu majiyoyi biyu daga gwamnatin Isra’ila sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa duk hukuncin da majalisar tsaron kasar ta yanke zai bukaci...
    A wannan Juma’a ne Australia ta bukaci Isra’ila da ta janye shirinta na mamaye yankin Zirin Gaza, inda ta yi gargadin cewa hakan zai kai ga barkewar matsaloli na jin kai a yankin. Ministar harkokin wajen Australiya Penny Wang a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce: Australia ta yi kira ga Isra’ila da kada ta bi wannan zabi, wanda zai kara ta’azzara matsaloli a zirin Gaza, tana mai jaddada cewa, tilasta tsugunnar da  Falastinawa a wajen yankunansu ya sabawa dukanin dokoki na kasa da kasa. Wang ta sake nanata kiranta na “tsagaita bude wuta, da shigar da kayan agaji ba tare da wani cikas ko tarnaki ba, da kuma sakin fursunonin da Hamas ke tsare da su tun...
    Majalisar ministocin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta amince da kudirin firaminista Benjamin Netanyahu na mamaye birnin Gaza, wanda ke zama matakin farko na wani gagarumin farmakin soji da ka iya kaiwa ga mamaye daukacin zirin Gaza, a cewar wani babban jami’in Isra’ila. Matakin ya biyo bayan tattaunawa sama da sa’o’i 10 da aka shafe ana yi tare da nuna wani gagarumin shiri na ci gaba da kai  hare-haren Isra’ila kan Gaza. Jami’an Amurka sun ce shugaba Trump ya zabi kada ya shiga cikin lamarin, inda ya zabi barin Isra’ila ta yanke shawarar kanta. A wani bangare na sabon farmakin da ke tafe, ana sa ran dakarun haramtacciyar kasar Isra’ila (IOF) za su ba da umarnin kwashe Falasdinawa kimanin miliyan 1 da...
    Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Wakilai, Abubakar Kabir Abubakar, ya ce Gwamnatin Tarayya za ta kashe Naira tiriliyan daya da rabi don gina layin dogo na zamani domin saukaka harkar sufuri a cikin birnin Kano. Ya bayyana hakan ne lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Kano, inda ya ce aikin zai saukaka wa mazauna birnin wahalar da suke sha a harkar sufuri. Zamfarawa sun yi zanga-zanga kan hare-haren ’yan bindiga Abba ya yi alhinin hadiminsa da ’yan daba suka kashe a Kano Ya ce, “Wannan aikin na gina layin dogo na zamani ya kai Dalar Amurka biliyan daya, kwatankwacin Naira tiriliyan daya da rabi. “Ga wadanda suke tafiye-tafiye zuwa kasashen waje, musamman kasashen Turai da nahiyar Asiya,...
    Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana alhini kan rasuwar Sadiq Gentle, wani hadiminsa kan harkokin yada labarai a Ma’aikatar Tarihi da Al’adu ta jihar, wanda wasu da ake zargi ’yan daba suka kai masa harin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa. Wata sanarwa da Kakakin Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a Facebook, ta bayyana Sadiq a matsayin jarumi, ƙwararre, kuma mai kishin kasa a fannin kafafen sada zumunta. NAHCON ta ƙayyade N8.5m kafin alƙalami na kujerar Hajjin 2026 An kashe mutum huɗu da tayar da ƙauyuka 17 a Sakkwato Gwamna Abba ya ce mutuwar Sadiq Gentle ta girgiza shi sosai, inda ya bayyana mamacin a matsayin mutum mai kamun kai, haƙuri, da sadaukarwa ga ci gaban Jihar Kano....
    Hukumar NAHCON mai kula da sha’anin aikin Hajji a Nijeriya NAHCON, ta bayyana cewa an ƙayyade naira miliyan 8.5 a matsayin kafin alƙalami na kuɗin kujerar aikin Hajjin 2026. NAHCON ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Alhamis, bayan gudanar da taro da shugabanni da kuma sakatarorin hukumomin aikin hajji na jihohin ƙasar. An kashe mutum huɗu da tayar da ƙauyuka 17 a Sakkwato ’Yan sanda sun ƙwato jariri da aka sace a asibitin Ekiti Mai magana da yawun NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta ce an ƙayyade ƙafin alƙalamin kuɗin kujerar domin fara shirye-shiryen ibadar ta wannan shekarar ta Musulunci. Hajiya Fatima ta ambato shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, yana cewa an ƙayyade...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Amurkawa sun yi kuskure idan suna tunanin cewa hari kan cibiyoyin makamashin nukiliya zai canza matsayin Iran ko kuma ya sa ta ja da baya Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Dole ne a fara wani sabon mataki na dangantaka tsakanin Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA saboda gaba daya sabbin al’amura sun bullo. Dokokin majalisar Shawarar Musulunci da yanayin filin sun canza, kuma an kai hari da bama-bamai da kuma lalata cibiyoyin makamashin nukiliya da yawa. Ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana cewa, Amurkawa sun yi kuskure idan har suna tunanin kai hari kan cibiyoyin makamashin nukiliya zai sauya matsayin Iran ko kuma ya...
    Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Injiniya Abdullahi Garba Ramat a matsayin sabon Shugaba kuma Babban Jami’in Gudanarwa (CEO) na Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC). Haka kuma, ya naɗa  Abubakar Yusuf a matsayin Kwamishinan Harkokin Abokan Hulɗa, da Dr. Fouad Olayinka Animashun a matsayin Kwamishinan Kudi da Harkokin Gudanarwa. A cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara ta Musamman kan Harkokin Watsa Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya sanya wa hannu, shugaban ƙasar ya bukaci waɗanda aka naɗa su yi amfani da ƙwarewarsu wajen tabbatar da burin gwamnatinsa a fannin wutar lantarki. Onanuga ya bayyana cewa  waɗannan nade-naden suna jiran tantancewar Majalisar Dattawa. Sai dai, domin kauce wa gibin shugabanci a hukumar, Shugaba...
    Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ta bayyana alhinita  kan kisan gilla da aka yi wa Umar Abdullahi Hafizi, dalibi da ke matakin karatu na 3 a Sashen Ilimin Zamantakewa (Sociology), wanda wasu masu kwacen waya suka daba wa wuka har lahira a gidansa da ke unguwar Dorayi a ƙaramar hukumar Gwale. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Hulɗa da Jama’a na jami’ar, Malam Lamara Garba, ya fitar, wacce aka rabawa manema labarai. A cewarsa, kodayake lamarin ya faru ne a wajen harabar jami’ar, shugabannin BUK sun jaddada cewa suna kokari wajen tabbatar da tsaron ɗalibansu. Shugaban Jami’ar, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya bayyana wannan lamari a matsayin babban rashi da ya girgiza al’ummar jami’ar, tare...
    Hukumar NDLEA ta Nijeriya da takwararta ta Indiya sun amince da yin aiki tare domin daƙile safarar miyagun ƙwayoyi tsakanin ƙasashen biyu. Wannan yarjejeniya ta fito ne daga wata tattaunawa ta kafar intanet tsakanin Shugaban NDLEA na Nijeriya, Janar Buba Marwa (mai ritaya), da shugaban hukumar ta Indiya, Anurag Garg. Shugabannin sun jaddada buƙatar haɗin gwuiwa, musamman wajen hana shigo da haramtattun magunguna daga Indiya zuwa Nijeriya. Marwa ya ce akwai buƙatar a ƙarfafa wannan dangantaka bisa yarjejeniyar da aka rattaba wa hannu a shekarar 2023. Bayan Shekaru 7 Yana Ɓoye, NDLEA Ta Cafke Babban Dillalin Ƙwayoyi NDLEA Ta Kai Samame Fitattun Wuraren Shaye-shaye, Ta Cafke Mutane 19 A Kano Buba Marwa ya roƙi hukumar Indiya da ta tallafa wa...
    Sayar da Nunez zai ba Liverpool damar siyan Alexander Isak daga Newcastle. Sai dai Newcastle ta ƙi karɓar tayin fam miliyan 110 daga Liverpool, saboda tana so ta siyar da Isak ne abkan fam miliyan 150. Liverpool ta riga ta siyo Florian Wirtz daga Bayer Leverkusen a kan fam miliyan 116 da kuma Hugo Ekitike daga Frankfurt a kan fam miliyan 79. Hakan ya sa Liverpool ta kashe kusan fam miliyan 250 a wannan kakar kasuwanni. Ta kuma siyar da Luis Diaz ga Bayern Munich ankan fam miliyan 65.5 da Tyler Morton ga Lyon a kan fam miliyan 15. Ɗan wasan Ingila Harvey Elliott ma na iya barin ƙungiyar a bana. A watan Janairu da ya wuce, Liverpool ta ƙi...
    “Ko da yake lamarin ya faru ne a wajen harabar jami’a, Hukumar Gudanarwa ta jami’ar na cikin jimami matuƙa da wannan mummunan lamari, kuma tana miƙa ta’aziyyarta ga iyalan marigayin, abokansa da sauran ɗalibai,” in ji sanarwar. Shugaban Jami’ar, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya bayyana cewa jami’ar na aiki tare da hukumomin tsaro domin a kama waɗanda suka aikata wannan laifi. An binne marigayin a garinsu da ke Zariya a Jihar Kaduna. Jami’ar ta buƙaci ɗalibai su kwantar da hankalinsu tare da kasancewa masu lura da abin da ke faruwa a tare da su. Haka kuma ta roƙi jama’a da su taimaka wa jami’an tsaro da duk wani bayani da zai iya taimakawa wajen gudanar da bincike. Daga kanmu,...
    Matasan Kauru Sun zargin Dan Majalisar Dokoki Barnabas Danmaigona da Rashin tabuka komai Wata kungiyar matasa, Kauru Youth Ambassadors (KYA) a karamar hukumar Kauru sun nuna matukar damuwa kan yadda Barnabas Danmaigona, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kauru a majalisar dokokin jihar Kaduna, ya gaza samar da ingantaccen wakilci tun bayan zaben sa. A wata sanarwa da kungiyar ta fitar mai taken daga ‘Daga Fata zuwa Yaudara’ wanda kuma Junaidu Ishaq Maisalati, ya sanyawa hannu, kungiyar ta caccaki dan majalisar kan abin da ta bayyana a matsayin mai dimama kujera kuma ɗan siyasar da ya gaza wajen gudanar da ayukka a mazabar da kuma aikin da zai amfani al’umma. Sanarwar ta koka da yadda al’ummar Kauru suka sanya kyakkyawan...
    Bayan kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin tubabbun ’yan bindiga da jama’ar gari a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, mazauna yankin sun ce yanzu matsalar tsaron ta dauki sabon salo. A watan Oktoban 2024 ne dai aka kulla yarjejeniyar sulhun tsakanin bangarorin biyu. Yarjejeniyar na zuwa ne bayan shafe sama da shekara 10 ana fama da rikicin da ya mayar da babbar hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari daya daga cikin mafiya hatsari a Najeriya. Bai kamata ake bai wa ɓarayi muƙamin ministoci ba — Sarki Sanusi II Ma’aikatan gwamnati na amfani da kudaden sata wajen gina rukunin gidaje – EFCC Daga shekara ta 2015, mazauna yankin sun sha fama da hare-hare da garkuwa da su, yayin da matafiya kuma...
    “Bari in yi bayani a fili: ba za mu yarda da duk wata dabi’a wacce za ta ruguza dabi’un da muke tsaye a kai ba. Dole ne kowane jami’in gwamnati ya kasance mai lura da al’amuransa, ba wai kawai ofishin ku kuke wakilta ba, har da mutuncin gwamnati baki daya.” In ji Gwamna Abba Kabir   Gwamna Yusuf, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya jaddada cewa, duk wanda aka samu yana taimakawa ko aikata laifuka to zai fuskanci cikakken fushin doka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin...
    Shugaban ya kuma yabawa cibiyoyin koyon ilimi tare da bayyana cewa wadannan nasarorin da aka samu shaida ne na ingancin ilimin Nijeriya wanda ke kekkenshe yara masu basira a duniya.   Tinubu ya yi imanin cewa, ilimi muhimmin abu ne ga ci gaban kasa; don haka, babbar hobbasar da gwamnatinsa ta yi a fannin, shi ne kawar da matsalolin kudi ga ‘yan Nijeriya marasa galihu da ke neman manyan makarantu ta hanyar ba su ba shi a ashirin Asusun ba da lamuni na ilimi na Nijeriya (NELFUND). Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki...
    Kakakin dakarun juyin juya halin musulun a nan Iran ya bayyana cewa nasarar da JMI ta samu na tunkude hare-harenda HKI ta kawowa kasar ya saya abubuwa da dama a bangaren siyasa da wasu al-amura a yankin da kuma duniya gaba daya. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto General Ali Mohammad Naeini yana fadar haka a wani wani taro na tunawa da daya daga cikin shahidan yakin kwanaki 12 wanda HKI da Amurka suka kallafawa kasar. Ya kara da cewa duniya ta sauya sabada nasarar sannan musamman a fagen diblomasiyya da kuma kafofin yada labarai a duniya, wanda ya bar tasiri mai kyau ga kasar. Labarin ya kara da cewa, akalla kasha 60 % na mutanen duniya...
    Ta sake kafa tarihi bayan da jaridar National Concord mallakar MKO Abiola ta naɗa ta a matsayin editan jaridar ta farko, inda A shekarar 1986, aka ɗaga darajarta zuwa matsayin Manajan Darakta kuma Babban Edita mace ta farko da ta riƙe wannan matsayi a tarihin jaridun Nijeriya. Ta auri MKO Abiola a shekarar 1981, kuma ta tsaya tsayin daka tare da shi wajen gwagwarmayar siyasarsa da rikicin da ya biyo bayan zaɓen 12 ga watan Yuni, inda ta bayar da gagarumar gudunmawa a fagen jarida, tare da shafe kusan shekaru 30 tana jan ragamar kafafen yaɗa labarai a Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya nada Ali Larijani babban mai baiwa Jagoran juyin juya halin Musulunci shawara a matsayin sabon babban sakataren kwamitin kolin tsaron kasar. Larijani ya taba rike mukamin sakataren majalisar koli ta tsaron kasar daga ranar 15 ga watan Agustan shekarar 2005 zuwa ranar 20 ga watan Oktoban shekarar 2007, sannan ya rike mukamin kakakin majalisar dokokin kasar Iran daga shekarar 2008 zuwa 2020. A ranar Lahadin da ta gabata, Iran ta sake gudanar da wasu sabbin canje-canje a kwamitin tsaron kasar, domin yin nazari a  kan tsare-tsaren tsaro da kuma karfafa karfin sojin kasar. Sanarwar da aka fitar a hukumance ta bayyana cewa, shugaba Masoud Pezeshkian ne zai jagoranci kwamitin tsaron, kuma zai hada da...
    A wata ganawa da ya yi da manyan jami’an tsaro a wannan  Talata don kammala dabarun yakin Gaza, Firayim Ministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya amince da kwace yankin zirin Gaza baki daya da karfin soji, duk da  hadarin da ke tattare da sauran fursunonin yahudawa da ke tsare a hannun ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa a Gaza. Ofishin Netanyahu ya fitar da wata ‘yar gajeriyar sanarwa da ke tabbatar da cewa Netanyahu ya gudanar da wani zaman  shawarwarin tsaro na tsawon sa’o’i uku, inda babban kwamnadan rundunar sojojin Isra’ila ya bayyana yuwuwar aiwatar da Shirin mamaye zirin yakin Gaza baki. Sanarwar ta kara da cewa rundnar sojin Isra’ila  ashirye take domin aiwatar da duk wani matakin da majalisar tsaron kasa...
    Wannan kuma ya tabbatar da cewa, gwamnatin Lai Ching-te a zahiri ‘yar dara ce a hannun Amurka, wadda za ta iya amfani ko watsi da ita. (Mai fassara Bilkisu Xin)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An samu bullar sabani da rikici a tsakanin ‘yan sahaypniyya game da mamaye Gaza a daidai lokacin da ake ci gaba da kai hare-hare da kuma rage yawan sojojinsu a yankin Yakin kisan kiyashi yana ci gaba da gudana a Gaza ta hanyar ci gaba da kai hare-hare kan mai uwa da wabi, tare da nau’o’i daban-daban na aiwatar da kashe-kashe da kuma kakaba yunwa. Duk da yadda kasashen duniya ke ci gaba da nuna bacin ransu kan irin girman kai da gwamnatin mamayar Isra’ila ke nuna wa, kafafen yada labaran haramtacciyar kasar isra’ila sun rawaito cewa: Majiyar fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu ta bayyana cewa ya yanke shawarar mamaye yankin gaba daya da aka killace saboda yana...
    Kwalejin Horasda Hafsoshin Soja ta Kasa dake Kaduna -NDA ta karyata jerin sunayen wadanda suka yi nasara shiga kwalejin dake yawo a halin yanzu.   A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na makarantar, Manjo Mohammed Maidawa ya fitar ya ce jerin sunayen ba su fito daga Kwalejin NDA ba.   Don haka ya shawarci jama’a da su yi watsi da jerin sunayen da aka zayyana, domin za a buga sahihan jerin sunayen a cikin fitattun jaridu na kasa da kuma a yanar gizon NDA a kan https://NDA.edu.ng/, a lokacin da ya dace.   PR/Usman Sani.
    Gwamnatin Tarayya ta gabatar da karramawar kasa da kuma tukuicin kudade ga kungiyar kwallon Kwando ta mata ta Najeriya, D’Tigress, bayan nasarar da suka samu a gasar cin kofin kwallon kwando na mata ta FIBA karo na biyar a jere.   A wata liyafar karrama su da aka yi a fadar shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, mai wakiltar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa kowane dan wasa zai karbi dala 100,000, yayin da koci da kungiyar kwararru za su samu dala 50,000 kowanne, tare da karramawar kasa ga daukacin kungiyar. Ya kuma yi alkawarin karin tukuicin da zai zo.   Shettima ya ce ba wai don murnar nasarar da kungiyar ta samu a cikin shekaru 78-64...
    Afirka ta Kudu ta zayyana matakan tallafi ga ‘yan kasuwa na cikin gida da kashi 30% na bangaren da harajin Amurka ya shafa a wannan makon, tare da kebe wasu ka’idojin samun wannan tallafin kudi. Kasar mafi karfin tattalin arziki a Afirka ta kwashe watanni tana kokarin tattaunawa da Washington, inda ta yi tayin sayen iskar gas na Amurka da kuma zuba jarin dala biliyan 3.3 a masana’antun Amurka a wata yarjejeniya da tawagar shugaban Amurka Donald Trump ta gabatar. Wannan yunƙurin ya ci tura. Jami’an Afirka ta Kudu sun ce, a cewar kamfanin dillancin labaran  Reuters, harajin Amurka zai iya janyo asarar dubunnan ayyuka, musamman a fannin noma da kera motoci. A wani taron manema labarai, ministocin ciniki da...
    Babban sakatare na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS, kana shugaban kasar, Xi Jinping ya bayar da muhimmin umarni game da binciken ra’ayoyin jama’a masu amfani da shafukan Intanet kan aikin tsara shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15 a kwanan nan, inda ya ce, ya kamata aikin tattara ra’ayoyin jama’a ta yanar gizo wajen tsara shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 15 ya samu shigar jama’a sosai, kuma ya kasance wani aiki na dimokuradiyya dake shafar dukkan bangarori. Jama’a sun yi ta ba da shawarwari tare da gabatar da ra’ayoyi masu muhimmanci, wadanda ya kamata sassan da abin ya shafa su yi nazari a hankali tare da shigar da su cikin tsarin. Kuma dole ne...
    “Jerin sunayen yaran Gaza da ke mutuwa “, dole ne a tabbatar da ba a kara yawansu ba. Shin wadannan sunayen yara kanana da hotunan su ba za su iya tada hankalin bangarori masu rikici ba?   Akasarin kasashen duniya sun yarda cewa “shawarar samar da kasashe biyu” ita ce mafitar warware matsalar Falasdinu, kuma amincewa da kasar Falasdinu wani muhimmin mataki ne na aiwatar da wannan shawara. Kwanan nan, an gudanar da babban taron kasa da kasa kan warware matsalar Falasdinu da aiwatar da shawarar “samar da kasashe biyu” a hedkwatar MDD da ke birnin New York, inda ministocin harkokin wajen kasashe 15 suka sanya hannu kan sanarwar hadin gwiwa, suna nuna niyyar amincewa da kasar Falasdinu. A yanzu,...
    Wakilin hukumar abinci na noma ta duniya FAO,  Farrukh Toirov, ya bayyana cewa sauyin yanayi ya shafi dukkan kasashen yankin Asiya da kudu, don haka yana daga cikin ayyukansu su samar da sabbin dabarbanun ayyukan noma tare da kasar Iran. Sannan JMI a matsayin kasa wacce take tsakiyar kasashen yankin tana iya aika da wadan nan dabarbaru ga sauran kasashen yankin. Kamfanin dillancin labaran Iran Press ko IP na kasar Iran ya nakalto Farrukh Toirov yana fadar haka, a dai-dai lokacinda ya mika takardun kama aiki a nan Tehran, daga babban cibiyarsu a MDD. Sabon wakili FAO a Iran ya kammala da cewa hukumarsa zata yi aiki tare da makarantu da cibiyoyin ayyukan noma don aiki tare da kuma samun...
    Bloomberg, ya nakalto wasu majiyoyi uku da ba a bayyana sunansu ba, sun ruwaito cewa, hukumar binciken manyan laifuka ta kasar Amurka (FBI) ta sauya sunan shugaban Amurka na yanzu Donald Trump da wasu manyan mutane daga takardun gwamnati da suka shafi shari’ar marigayi mai kudi Jeffrey Epstein. Hukumar ta bayyana cewa sun yanke shawarar sauya sunayen da suka hada da na Trump ne saboda matsayinsu na ‘yan kasa a lokacin da aka fara gudanar da bincike a shekarar 2006, inda ta ce bayyanar sunayen mutane a irin wadannan fayiloli ba wai yana nufin suna da hannu cikin wani laifi ba. An kama Epstein a cikin 2019 kuma an tuhume shi da laifin safarar yara kanana don yin lalata, laifin...
    Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta sanar a jiya Lahadi cewa, Sin da Rasha sun fara atisayen soja na hadin gwiwa mai taken “Tekun hadin gwiwa na shekarar 2025” a tekun Japan, a wani bangare na kokarin zurfafa hadin gwiwarsu ta fuskar “mutumin Amurka.” Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta bayyana cewa, sojojin biyu za su gudanar da ayyukan ceto a cikin ruwa, da yaki na hadin gwiwa na yaki da jiragen ruwa, da na yaki da jiragen ruwa, da na jiragen ruwa a kusa da tashar jiragen ruwa na Vladivostok na Rasha. Sanarwar ta ce, jiragen ruwa na kasar Sin 4 ne ke halartar atisayen tare da na Rasha, ciki har da makami mai linzami Shaoxing da Urumqi. Rasha da...
    Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun bayyana cewa: Masu shirin halaka Gaza suna neman hadiye duniyar Musulunci  ne Dakarun kare juyin juya halin Musulunci nanIran sun yi gargadin cewa; Bangarorin da ke shirya kisan kiyashi a Gaza ba wai kawai halakar al’ummar Falastinu ba ne kawai, a’a suna neman mamaye yankuna masu arziki da muhimmanci na duniyar Musulunci ne a wani bangare na ci gaba da fadada ayyukan da suka shafi tsaro da albarkatun kasa. Dakarun kare juyin juya halin na Musuluncin sun bayyana a cikin wata sanarwa cewa: Tsayin daka da gwagwarmayar da al’ummar Falastinu suke yi a yau a zirin Gaza wajen fuskantar kisan kare dangi da laifukan yahudawan sahayoniyya, wata shaida ce da ke...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da babban shirin dashen bishiyoyi miliyan biyar a shekarar 2025. An fara dashen ne yankin Yanbawa da ke Ƙaramar Hukumar Makoda. Sake zaɓen Tinubu zai lalata makomar Najeriya — El-Rufai  Gwamnan Yobe ya naɗa Gadaka a matsayin sabon Sarkin Gudi Gwamnan ya ce wannan shiri na nufin yaƙi da sauyin yanayi, farfaɗo da ƙasar da ta lalace, da kuma kare muhalli. Ya ce an fara dashen bishiyoyin a wannan fili tun shekarar 1972, amma aka bari ya lalace. Yanzu gwamnatinsa ta gyara shi don ya taimaka wajen shawo kan matsalolin fari da sauyin yanayi. Ya ƙara da cewa wannan shiri yana daga cikin ayyukan muhalli da gwamnatinsa ta aiwatar cikin shekara guda....
    Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da naɗa Hon. Ismaila Ahmed Gadaka a matsayin sabon Sarkin Gudi, bayan rasuwar Alhaji Isa Bunuwa Madugu Ibn Kaji. Sabon Sarkin na Gudi, Ismaila Ahmed Gadaka, ya shahara da ƙwarewa a fannoni da dama. Sojoji sun ceto malamin Jami’a da aka sace a Taraba Ma’aikatan jinya sun dakatar da yajin aiki a faɗin Najeriya Ya taɓa zama ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Fika/Fune daga 2011 zuwa 2019, kuma kafin nan ya yi aiki a matsayin Kwamishina a Jihar Yobe daga 2007 zuwa 2010. Gadaka, ƙwararren ma’aikacin banki ne, inda ya yi aiki da bankuna irin su UBA da Standard Trust Bank, inda ya kai matsayin Manajan Kasuwanci. Kafin naɗa shi Sarki, ya...
    A cewar shugaban kwamitin, Katsina na kuma goyon bayan batun sauke wasu ikon gwamnati daga matakin tarayya zuwa jihohi, saka sarakunan gargajiya a cikin kundin tsarin mulki da kuma sake fasalin harkokin kuɗi. Sanata Ibrahim ya shaida wa kwamitin cewa an tattara dukkan ra’ayoyi da buƙatun jama’ar Katsina, tare da gabatar da su a cikin takardar matsayar. Tun da farko, yayin da yake ƙaddamar da taron jin ra’ayoyin jama’a, shugaban kwamitin majalisar dattawa kan gyaran kudin tsarin mulki ya buƙaci a riƙa yin irin wannan taron lokaci zuwa lokaci domin ya dace da halin da ake ciki. Sanata Barau Jibrin, wanda shi ne mataimakin shugaban majalisar dattawa, ya tabbatar da cewa dukkan abubuwan da aka tattara daga gwamnati, ƙungiyoyi da...
    An ƙara hakimai shida a Masarautar Katsina kamar yadda mahukunta suka tabbatar. Wata sanarwa da Sakataren Masarautar Katsina, Alhaji Bello M. Ifo ya fitar ta ce tuni an fitar da sunayen sabbin hakimai shida da iyakokin da za su jiɓinci jagorancinsu. Jamus ta soma jefa kayan agaji a Zirin Gaza Ambaliya: Mutum 165 sun mutu a Nijeriya a bana — NEMA Sabbin hakiman sun haɗa da Karshin Katsina, Alhaji Sanusi Kabir a matsayin Hakimin Shinkafi da Tsohon Ministan Harkokin Sufurin jiragen sama Sanata Hadi Sirika a matsayin Marusan Katsina — Hakimin Shargalle. Sauran sun haɗa da Alhaji Ahmad Abdulmuminu Kabir Usman — Danmajen Katsina a matsayin Hakimin Dankama da Alhaji Abubakar Dardisu Sarkin Muduru a matsayin Hakimin Muduru. Sanarwar ta...
    Wani fim mai suna “Dead to Rights”, wanda aka shirya game da kisan kiyashin da aka yi a birnin Nanjing, ya mamaye kasuwar fina-finai ta lokacin zafi ta kasar Sin, inda kudin shigar da aka samu da shi ya zarce yuan biliyan daya, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 140 cikin kwanaki takwas kacal. Wanda aka yi amfani da ingantattun shaidun hotuna na ta’asar yakin da Japanawa suka aikata a lokacin kisan kiyashin Nanjing, Fim din na “Dead to Rights” ya ba da labari ne na wani rukunin fararen hula na kasar Sin da suka nemi mafaka a dakin daukar hoto a lokacin muguwar mamayar da azzaluman Japanawa suka yi a birnin Nanjing. A wani yunkuri na neman tsira da rayukansu hajaran-majaran,...
    Fiye da shekaru goma da suka gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya dora samun ci gaba marar gurbata muhalli a matsayin wata muhimmiyar manufar raya kasa. Ya taba fitar da manufar raya kasa ta hanyar bayar da muhimmnci ga “Muhalli”, wadda ta yi nuni da cewa ingantaccen yanayin muhalli abu ne mai matukar daraja don samun ci gaba. Tun daga wannan lokacin, kasar Sin ta ci gaba da yin sauye-sauye masu kiyaye muhalli, inda ta zama kasa mafi girma a duniya wajen kera batir na lithium da motocin masu amfani da lantarki. Game da hakan, a yayin da ake tattaunawa da Jorge Moreira da Silvas, babban darektan ofishin kula da ayyuka na MDD, a wani shiri mai suna “Leaders Talk” da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kafin ya yi ritaya daga Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya, AVM Kaita ya riƙe muƙamai da dama, ciki har da Daraktan Tsare-tsare a Hedikwatar Tsaro da kuma Shugaban Sashen Kirkire-Kirkire na tsaro. Ana girmama shi saboda gudunmawar da ya bayar wajen horarwa da inganta ayyukan rundunar sojin sama. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kasar Spain ta bayyana abin da ke faruwa a Gaza a matsayin abin kunya ga bil’adama Ministan harkokin wajen kasar Spain José Manuel Albares ya yi kira ga mahukuntan Isra’ila a ranar Alhamis da su bude mashigar ruwa na dindindin domin ba da damar kai agajin jin kai zuwa zirin Gaza, yana mai gargadin cewa; Bala’in jin kai a yankin da aka killace zai iya ta’azzara. A nasa jawabin Albares ya jaddada cewa: Gaza na fuskantar yunwa sakamakon killacewar da haramtacciyar  kasar Isra’ila ta mata, kuma abin da ke faruwa a wurin abin kunya ne ga bil’adama. Ya kara da cewa yunwa na ci gaba da lakume rayukan fararen hula a yankin a kowace rana. Ministan na Spain ya jaddada...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana naɗin Saidu Yahya a matsayin sabon Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafen Jama’a da yaƙi da cin hanci da rashawa (PCACC), bayan ƙarewar wa’adin tsohon shugaban, Barrister Muhuyi Magaji Rimin Gado, a watan Yuni. Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ta tabbatar da naɗin Sa’idu Yahya, mai shekaru 47, jami’i a fannin bincike kan cin hanci, inda ya shafe fiye da shekaru 18 yana aiki a Hukumar ICPC. Za A Kammala Aikin Titin Jirgin Ƙasan Kaduna-Kano A 2026 – Gwamnatin Tarayya Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Belin Dillalin Kwaya An bayyana cewa Yahya na da digiri a fannin tattalin arziki daga Jami’ar Bayero Kano,...
    Gwamna Zulum ya nuna jin dadinsa ga kwamishinonin biyu, tare da yi musu fatan alheri a cikin ayyukansu na gaba.   Sai dai ya sanar da nadin Engr. Mohammed Habib da Ibrahim Hala Hassan domin maye gurbin kwamishinonin biyu da aka sauke.   A halin da ake ciki, Gwamna Zulum ya kuma amince da nadin Farfesa Yusuf Gana Balami a matsayin Shugaban Hukumar Ilimin Sakandare ta Jihar Borno.   Balami, Farfesa a fannin ilimi, ya fito ne daga Hawul da ke kudancin jihar.   Zulum ya taya Balami murna tare da bukatar sa da ya yi amfani da shekarunsa na gogewa a fannin ilimi, a matsayin shugaba a bangaren gudanarwa da karantarwa wajen sake fasalin ilimin sakandare a jihar. ...
    Melaye wanda shi ne dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a zaben jihar Kogi a 2023, har yanzu bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba a nan gaba. Sai dai rahotanni na nuni da cewa, yana iya sauyawa zuwa jam’iyyar ADC – wata gamayyar jam’iyyar adawa da a baya-bayan nan ta jawo hankalin wasu jiga-jigan masu sauya sheka da suka hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A daidai lokacin da yakin Gaza yake cika kwanaki 664, sojojin HKI suna ci gaba da kisan kiyashi akan Falasdinawan da suke fama da yunwa saboda karancin abinci. A jiya kadai sojojin mamayar sun yi wa Falasdinawa 80 kisan kiyashi. Asibitocin yankin Gaza sun sanar da karbar gawawwakin shahidai a jiya da kuma yau Alhamis. A gefe daya, manzon Amurka Steve Vittkov zai ziyarci HKI a yau Alhamis domin tattauna halin da ake ciki a yankin Gaza. Wannan ziyarar tashi dai tana zuwa ne a daidai lokacin da majiyoyin ‘yan sahayoniyas suke Magana akan kara daukar matakai masu tsanani akan al’ummar Gaza da yunwa ta jigata su. A can yankin yammacin Kogin Jordan kuwa wani Bafalasdine ya yi sahahda, yayin...
    Wani sojan Amurka ya ba da shaida game da kisan wani yaro da sojojin mamayar Isra’ila suka yi a cibiyar bada agaji ta Rafah Wani sojan Amurka da ke aiki a cibiyar rarraba kayan abinci a zirin Gaza ya yi furuci da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun kai hari kan wani yaro Bafalasdine da ya yi tafiya mai nisan kilomita 12 a karkashin zafin rana, don neman kayan abincin agaji a yankin. A cikin wata sheda mai ratsa jiki da ya bayar a cikin wani dan gajeren faifan bidiyo a Amurka, Private Anthony Aguilar ya ba da labarin wani lokaci da ba za a manta da shi ba cewa: Wani yaro siriri mai suna Amir, babu takalmi a kafarsa, ya...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) ta zargi Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da kin yin adalci wurin ayyuka da raba mukamai tsakanin Arewa da Kudancin Kasar nan. Wadannan zarge-zarge suka sa fadar Shugaban Kasa ta hannun mai taimaka masa na musamman kan kafofin yada labarai Bayo Onanuga mayar da martani ga kungiyar ta ACF. Ko wadanne irin martani fadar shugaban kasar ta mayar ga kungiyar? NAJERIYA A YAU: Yadda Za A Dama Da Matan Arewa A Fannin Kimiyya DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
      A shekara ta 2009, hukumar Kwallon Kafa ta Nijeriya ta dauki Yusuf aiki a matsayin mataimakin koci ga Samson Siasia  wanda ke rike da mukamin babban kocin tawagar kwallon kafa ta Nijeriya, Yusuf har yanzu yana aiki da Siasia, ya taimakawa Pillars samun gurbin shiga gasar cin kofin CAF, a shekarar 2012 ya koma Enyimba inda ya maye gurbin Austin Eguavoen a matsayin koci kuma ya taimaka masu wajen lashe kofin gasar Federation Cup na shekarar 2013. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa za ta kammala aikin shimfiɗa layin dogo wanda ya taso daga Kaduna zuwa Kano a cikin shekarar 2026 mai zuwa. Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a yau Laraba. Kazalika, takwaransa na sufuri, Sa’idu Ahmed Alkali ya jaddada hakan ne a yayin jawabinsa a wajen wani taron tuntuɓa tsakanin ’yan ƙasa da gwamnati da ke gudana a Jihar Kaduna. Tattalin arzikin Nijeriya zai ci gaba da bunƙasa har zuwa baɗi — IMF Tinubu ya naɗa sabon shugaban hukumar kashe gobara ta ƙasa A cewar ministan, lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya hau mulki kashi 15 cikin 10 na aikin kawai aka...
    Adamu ya bayar da hujjar cewa, Sarkin Musulmi ne ke shugabantar daular gargajiya mafi girma a Arewacin Nijeriya, tare da dukkan sarakunan yankin karkashin jagorancinsa na ruhi da al’adu.   Ya yaba da shugabancin Sarkin Musulmi Abubakar na tsaka-tsaki, samar da zaman lafiya, da jagoranci na hadin kai.   Sun bayyana shi a matsayin mutum mai kishin kasa wanda ya yi namijin kokari wajen inganta tattaunawa tsakanin addinai da hadin kan kasa.   Kungiyar ta yi kira ga Majalisar Dokoki ta kasa, da fadar shugaban kasa, da sauran al’ummar Nijeriya da su goyi bayan nadin, inda ta ce hakan zai karfafa cibiyoyin gargajiya da kuma samar da hadin kai a tsakanin sarakunan gargajiya a fadin kasar. Daga kanmu, magana...
    Kakakin ofishi mai lura da harkokin yankin Taiwan a majalisar gudanarwar kasar Sin Chen Binhua, ya ce kalaman da aka jiyo jagoran yankin Taiwan na kasar Sin Lai Ching-te na yi dangane da sakamakon zagayen farko na kuri’ar kiranye da al’ummar Taiwan suka kada, ya nuna rashin gamsuwarsu da salon mulkin jam’iyyar DPP mai mulkin yankin. Chen Binhua, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a Larabar nan, ya ce kalaman Lai na cike da yaudarar kai, sun kuma fayyace manufar da ya dage a kanta ta “neman ’yancin kan Taiwan”. Kazalika, mummunan kayen da DPP ta sha a kuri’un da aka kada ranar Asabar din karshen makon jiya, ya fayyace ajandarta ta yin fito-na-fito da Sin, tare da fafutukar...
    Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya sauke Farfesa Muhammad Sani Bello daga matsayin Kwamishinan Yaɗa Labarai kuma memba na majalisar zartarwa ta jihar. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Malam Ibraheem Musa, ya fitar a ranar Talata, an bayyana cewa Ahmed Maiyaki, wanda shi ne Manajan Darakta na Kamfanin Yaɗa Labarai na Kaduna (KSMC), ne za a maye gurbinsa. Sin Da Benin Da Thailand Za Su Aiwatar Da Matakan Saukaka Tantance Kaya Na Kwastam Babu Wata Karamar Hukumar Da Ke Ƙarƙashin Ikon Ƴan Ta’adda A Filato -Gwamna Mutfwang Gwamna Sani ya gode wa Farfesa Bello bisa ayyukan da ya gudanar, inda ya ce shi ne kwamishinan ilimi na farko a gwamnatinsa, kafin daga baya ya...
    Gwamnatin jihar Kano tare da hadin gwiwar wata kungiya mai suna Partnership for Agile Governance and Climate Change (PACE) ta kaddamar da manufofinta na sauyin yanayi a hukumance. Wannan manufa mai mahimmanci ta samar da taswirar dabaru don ragewa, daidaitawa, da tsarin tafiyar da yanayi mai hadewa a duk sassan ci gaba a jihar.   Da yake jawabi a wajen taron kaddamar da taron wanda aka gudanar a dakin taro na Armani Event Centre dake Kano, Gwamna Abba Yusuf wanda sakataren gwamnatin jihar Ibrahim Farouk ya wakilta, ya bayyana taron a matsayin wani babban ci gaba a kokarin gwamnatinsa na mayar da jihar Kano a matsayin mai ci gaba a harkokin tafiyar da yanayi da muhalli.   Gwamna Yusuf ya...
    Sanarwar New York ya jaddada alƙawarin kasa da kasa na kawo ƙarshen yaƙin a Gaza da aiwatar da hanyoyin samar da ƙasashe biyu Majalisar Dinkin Duniya ta sanar a cikin “Sanarwar New York” da yarjejeniyar kasa da kasa kan matakan dole da suka dace don kawo karshen yakin Gaza da aiwatar da Shirin samar da kasashe biyu da zai kai ga kafa kasar Falasdinu mai cikakken ‘yanci, da sake gina Gaza, da tura tawagar tabbatar da zaman lafiya ta kasa da kasa karkashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya. Sanarwar karshe da taron Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar kan sasanta rikicin Falasdinu cikin lumana ya sanar da amincewar kasashen duniya kan daukar matakai na bai daya don kawo karshen hare-haren wuce gona...
    Fira ministan Birtaniya ya bayyana cewa: Za su amince da kasar Falasdinu a watan Satumba idan yanayin Gaza bai canza ba Keir Starmer ya kara da cewa, an dauki wannan matakin ne domin kare tsarin kasashe biyu, kuma kasarsa na da wani nauyi na musamman da ya rataya a wuyanta wajen ganin an samar da zaman lafiya a tsakanin kasashen biyu. Ya ce tallafin da kasarsa ke baiwa Tel Aviv yana nan daram. Fira ministan na Burtaniya ya jaddada cewa kin amincewar da fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi na samar da kasashe biyu kuskure ne kuma kuskure ne na dabi’a da dabaru. Ya jaddada cewa dole ne a bude mashigar kasa sannan kuma a bar manyan motocin...
    Ma’aikatar Harkokin Wajen Faransa ta bayyana cewa: Laifukan da aka aikata a Yammacin Kogin Jordan na Falasdinu ayyukan ta’addanci ne Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta tabbatar da cewa tashe-tashen hankula da laifuffukan da tsagerun yahudawan sahayoniyya suke yi a yammacin gabar kogin Jordan da aka mamaye sun zama ayyukan ta’addanci, biyo bayan kashe wani mai fafutukar yaki da mamayar da tsagerun ‘yan sahayoniyya suka yi. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ya ce: “Faransa ta yi Allah-wadai da wannan kisan gilla da kakkausar murya, da kuma dukkan ayyukan ta’addanci da gangan da masu tsattsauran ra’ayi ke yi kan Falasdinawa, wanda ke karuwa a ko’ina cikin yankunan Gabar Yammacin Kogin Jordan.” Ya kara da cewa, wadannan ayyukan wuce gona da irin, hakikanin ayyukan...
    An shawarci gwamnatocin jihohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara da su kirkiro hanyoyi na wayar da kan al’umma dangane da shirye-shiryen tallafi da ayyukan ci gaba da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa domin bunkasa tattalin arziki da tabbatar da tsaro a yankunansu. Shugaban sashen kimiyyar zamantakewa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, Farfesa Chika Umar Aliyu, ne ya bayar da wannan shawara yayin gabatar da takarda a wajen taron shekara-shekara na kungiyar Nigerian Institute of Management reshen jihar Sokoto na shekarar 2025, wanda aka hada da gabatar da lambar yabo ga wadanda suka cancanta.   Farfesa Chika ya bayyana cewa, gwamnati tarayya na da shirye-shiryen tallafi da dama da suka hada da na noma, kasuwanci da kuma koyar da sana’o’in hannu...
    Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da naɗa Muhammad Fa’iz a matsayin Kwamanda Janar na farko na Hukumar Hisbah ta Jihar. Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ne ya tabbatar da naɗin ga manema labarai a Dutse. Ya bayyana cewa hakan na daga cikin ƙoƙarin Gwamna Namadi na ƙarfafa ayyukan sabuwar hukumar Hisbah da inganta aikinta. A cewar sa, naɗin ya haɗa da Dr. Husaini Yusuf Baban a matsayin Babban Mataimakin Kwamanda Janar, da Lawan Danbala a matsayin Mataimakin Kwamanda Janar da hedikwatar hukumar, da kuma Yunusa Idris Barau a matsayin Mataimakin Kwamanda Janar naYankin Dutse. Sauran su ne Abdulkadir Zakar, Mataimakin Kwamanda Janar, Yankin Hadejia, da Suraja Adamu, Mataimakin Kwamanda Janar, Yankin Gumel, da...
    Shugaban Ivory Coast, Alassane Ouattara wanda ke jagorantar ƙasar tun daga shekarar 2011, na fuskantar suka na neman mayar da shugabancin ƙasar mutu ka raba. Wannan dai na zuwa ne bayan Ouattara mai shekaru 83 ya tabbatar da aniyar sake takara wa’adi na hudu a zaben da za a yi ranar 25 ga watan Oktoba. Za mu halasta kafa ƙasar Falasɗinu muddin Isra’ila ba ta cika wasu sharuɗa ba — Birtaniya Nijar da Rasha sun ƙulla yarjejeniyar makamashin nukiliya A wani takaitaccen bayani da ya yi, Ouattara ya ce takararsa ta samo asali ne daga buƙatarsa ta kiyaye zaman lafiyar ƙasa a daidai lokacin da ta ke fuskantar kalubalen tsaro da na tattalin arziki. Ya bayyana cewa, “Ni dan takara...
    Rundunar Ƴansandan jihar ba ta fitar da bayani kai tsaye ba, amma wani babban jami’i da ya nemi a ɓoye sunansa ya tabbatar da kama wanda ake zargi, tare da ce wa an tafi da shi zuwa Lokoja domin cigaba da bincike. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamna Lawal ya taya sabon sarki murna, tare da roƙon Allah Ya bashi hikima da ikon yin jagoranci na gari. Ya kuma buƙace shi da ya ci gaba da bin kyawawan ɗabi’u da tafarkin tsofaffin sarakuna domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a masarautar Gusau. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tawagogin wakilan kasashen Sin da Amurka sun hallara a kasar Sweden yau Litinin, domin fara wani sabon zagayen tattaunawa game da cinikayya da tattalin arziki. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jam’iyyar ta bayyana cewa bayan bincike daga reshen jam’iyyar na jihar Kaduna, ya tabbatar da cewa El-Rufai ba halataccen ɗan SDP bane. Saboda haka, Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar na Ƙasa ya kafa masa takunkumin shekaru 30, har zuwa shekarar 2055, ya hana shi sake neman zama mamba ko hulɗa da jam’iyyar ta kowace fuska. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan Harkokin Tsaron Ƙasa, Dakta Bello Mohammed Matawalle, ya baiwa iyalan marigayi Sarkin Gusau, Alhaji Ibrahim Bello, gudummawar naira miliyan biyar da kuma kayan abinci, bayan rasuwarsa a ranar Alhamis da ta gabata a birnin Abuja sakamakon gajeruwar rashin lafiya.   Dakta Matawalle, ya bayyana alhininsa bisa wannan rashi na Mai Martaba.   Baya ga gudummawar kuɗi, ministan ya kuma bada buhunan shinkafa 20, gero 10, masara 10 da kuma dawa 10 ga iyalan mamacin.   Wata tawaga mai ƙarƙashin jagorancin Sanata Hassan Muhammad Nasiha, tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara a zamanin mulkin Matawalle ne suka miƙa gudummawar a madadin ministan. Dakta Matawalle ya bayyana marigayi Sarkin Gusau a matsayin shugaba mai ɗabi’a ta gari, wanda ya kasance...
    122- Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da haka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttahhari, ko kuma cikin littafin mathnawa na maulana Jalaluddeen Rum ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sarir Imam Al-Hassan Almujtaba (a) diyar Fatima (s) kuma jikan manzon All..(s) na farko, idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata mun bayyana yadda. Ummul muminina Aisha...
    Al’ummar Arewacin Najeriya na shirin kayar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 saboda ƙuncin rayuwa da kuma tsare-tsaren gwamnatinsa da suka mayar da yankin saniyar ware. Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal  ne ya bayyana haka, yana mai cewa gamayyar shugabanni da ’yan siyasar Arewa na haɗa ƙarfi da ƙarfe domin tsayar Da ɗan takara da nufin yaƙar gwamnatin Tinubu a zaɓen 2027. Babachir David Lawal ya bayya cewa shugabannin siyasar Arewa na aiki tare da Kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF) da Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) domin cin ma wannan manufa, kuma “Babu yadda za a yi mutum ya ci zaɓe na tare da samun goyon bayan waɗannan ƙungiyoyin ba.” Ya ƙara da cewa tsare-tsaren Tinubu ciki...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Tattaunawar makamashin nukiliya wani zaɓi ne mai mahimmanci wanda ya ƙarfafa matsayin Iran a duniya Ministan harkokin wajen kasar Iran Seyyed Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa; Kasarsa ta shiga shawarwarin makamashin nukiliya ba na                         kai tsaye ba da Amurka bisa wata cikakkiyar shawarar kasa. Ya kara da cewa; Wannan mataki na diflomasiyya ya karfafa kimar Iran a duniya, bayan da ta samu goyon bayan kasashe fiye da 120 wadanda suka yi Allah wadai da cin zarafin da yahudawan sahayoniyya suka yi wa Iran a baya-bayan nan. Hakan dai ya zo ne a yayin wata ganawa da aka yi da Araghchi, inda ya yi nazari kan batutuwan da suka shafi makamashin nukiliyar...
    Babban jami’in kungiyar Hamas a Zirin Gaza ya bayyana cewa: Makiya yahudawan sahayoniya suna rufe gazawar sojojinsu da kisan kare dangi Khalil al-Hayya babban jami’in kungiyar gwagwarmayar Musulunci  ta Hamas a zirin Gaza ya jaddada cewa: Makiya yahudawan sahayoniyya suna rufe gazawar sojojinsu ta hanyar kisan kare dangi da suke aiwatarwa kan fararen hula. A cikin wani jawabi kai tsaye ta gidan talabijin, Al-Hayya ya bayyana cewa: “Ya ku ‘ya’yan Dakarun Qassam, da na Quds Brigade, da kuma sauran kungiyoyin gwagwarmaya, abin da kuke yi ya kawo cikas ga farmakin da motoci masu sulke na makiya suke yi. Khalil ya jaddada cewa: Babban hafsan hafsoshin sojin makiya yana rufe gazawar sojojinsa da kisan kare dangi da suke aiwatarwa kan fararen...
    Dubban ‘yan Najeriya magoya bayan kungiyar kwallon kafar ta ” Super Falcon” sun yi bikin samun nasarar da kungiyar tasu ta samu, wasan karshe na samun kofin nahiyar Afirka na kwallon kafa na mata. A wasan da aka yi kafin hutun rabin lokaci, ‘yan wasan kasar ta Moroko sun yi bajinta, inda  su ka ci kwallaye 2-0, sai dai bayan komawa hutu, ‘yan wasan na Najeriya sun farke kwallon da aka zura musu, sannan kuma su ka kara da daya akai.  Sai dai duk da cewa an sami galaba akan kungiyar kwallon kafar ta Moroko, magoya bayanta da suke bakin ciki, sun jinjinawa kungiyar tasu. Wasu sun bayyana cewa ba su tsammaci za a sami galaba akansu ba,, domin sun...
    Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibril, ya kaddamar da zaman jin ra’ayoyin jama’a na yankin Arewa maso Yamma kan sauya kundin tsarin mulkin Najeriya a Kano. Yayin gabatar da jawabinsa na bude taron, Sanata Barau ya yi maraba da manyan baki da suka halarci zaman, yana mai cewa: “Ina alfahari da zuwanku wannan zama na jin ra’ayoyin jama’a na yankin Arewa maso Yamma, wanda ya shafi kudurori da sabbin batutuwa dangane da gyaran kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya.” Sanata Barau ya tunatar da cewa Majalisar Ƙasa ta riga ta amince da gyaran kundin tsarin mulki sau biyar, da aka fi sani da alteration acts na farko zuwa na biyar. Ya jaddada cewa akwai muhimman batutuwa da ke buƙatar ƙarin...
    Tsare-tsaren farko: Da yake su Turawan mulkin mallaka su riga sun kasance sun zauna daram a Arewacin Nijeriya, daganan sai suka aiwatar da tsare tsarensu wadanda sun bullo da su ne domin hana cinikin Bayi.Suka maida lamarin wanda a shekarun baya ba matsala bace,amma yanzu a shar’ance, an hana shi,sannan kuma naka samu damar ‘yantar da wadanda Iyayen su suka zama Bayi bayan wani lokaci.   Yadda aka bullo ma lamarin: Yayin da ake ta kokarin hana cinikin Bayi, su Turawan mulkin mallaka sun,amince da yadda cinikin Bayi ya shafi lamarin zamantakewa da tattalin arziki a sashen na Arewacin Nijeriya. Don haka sai suka bi abin sannu- sannu, har dai suka samu damar kawo karshen lamarin, ta hanyar bada zabi...
    Daruruwan mutane daga sassa daban-daban na Jihar Zamfara da wajen ta sun halarci Sallar jana’izar marigayi Sarkin Gusau, Dr. Ibrahim Bello, wanda ya rasu a daren Alhamis bayan gajeruwar rashin lafiya. An gudanar da Sallar jana’izar ne a Masallacin Jumu’a na Gusau da ke Kanwuri, inda Mataimakin Babban Limamin masallacin, Malam Abdulkareem Umar, ya jagoranci addu’o’in. 172-days_english-3316981 Daga cikin manyan baki da suka halarta har da Gwamnan Jihar Zamfara, Dr. Dauda Lawal, wanda ya bayyana marigayin a matsayin Uba ga kowa, shugaba mai son zaman lafiya, kuma mutum mai hikima wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen ci gaba da hadin kan jihar. Gwamna Lawal ya nuna alhini matuka game da rasuwar Sarkin, inda ya yi addu’ar Allah ya...
      Tsofaffin shugabannin da suka rasu bayan kammala wa’adinsu Nnamdi Azikiwe An haife shi a ranar 16 ga Nuwamba, 1904, Dakta Nnamdi Azikiwe, wanda aka fi sani da “Zik of Africa,” fitaccen dan siyasar Nijeriya ne kuma mai kishin kasa wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen samun ‘yancin kai. Ya zama shugaban kasa na farko a Nijeriya daga 1963 zuwa 1966, bayan ya zama Gwamna-Janar a 1960 tare da Firai Minista Abubakar Tafawa Balewa. Azikiwe ya rasu yana da shekaru 91 a duniya a ranar 11 ga Mayu, 1996, a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Nijeriya, Enugu, bayan ya sha fama da rashin lafiya. Bayan shugabancinsa, Dakta Azikiwe ya kasance dan jarida na farko, haziki, kuma daya daga cikin wadanda suka...
    A ranar Alhamis 24 ga watan nan ne aka tantance tare da amincewa da biranen kasar Sin guda tara a matsayin biranen dausayi na kasa da kasa, yayin bude taron bangarorin da suka kulla yarjejeniyar Ramsar kan filayen dausayi karo na 15 (COP15), da aka gudanar a birnin shakatawa na Victoria Falls na kasar Zimbabwe, inda hakan ya kara adadin wadannan biranen a kasar Sin zuwa 22. Sabbin biranen tara da aka amince da su sun hada da Chongming na Shanghai, da Dali na lardin Yunnan, da Fuzhou na lardin Fujian, da Hangzhou na lardin Zhejiang, da Jiujiang na lardin Jiangxi, da birnin Lhasa na jihar Xizang mai cin gashin kanta, da Suzhou na lardin Jiangsu, da Wenzhou na lardin...
    Sai dai Sanatoci sun yi watsi da bayanin, inda suka zargi Ojulari da yin watsi da Majalisar. Kwamitin yana binciken tambayoyin tantancewa daga shekarar 2017 zuwa 2023, wanda ya nuna sabanin da ya kai Naira tiriliyan 210, ciki har da bashin da ba a tabbatar da shi ba na Naira tiriliyan 103. ‘Yan majalisar sun firgita cewa Naira tiriliyan 3 zuwa 5 ne kawai aka rubuta a cikin asusun ribar da kamfanin ya samu a cikin shekaru shida. “Wannan gayyatar ba tilas bace,” in ji Wadada. Ya kara da cewa kwamitin ba yana zargin hukumar ta NNPC da laifin sata bane amma ya jaddada cewa girman sabanin ya bukaci a yi karin haske kai tsaye. Ya bayyana rashin bayyanar Ojulari...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Taron Istanbul wata dama ce ta gyara matsayar Turai kan shirin makamashin nukiliyar Iran Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i, ya yi la’akari da taron na yau tsakanin Iran da kasashe uku mambobin kungiyar hadin gwiwa ta JCPOA a matsayin wata muhimmiyar dama ta gyara ra’ayoyinsu da gwada hakikaninsu kan batun makamashin nukiliyar kasar Iran. A cikin wata sanarwa da ya aikewa kamfanin dillancin labaran IRNA, Isma’il Baqa’i ya bayyana fatansa na cewa wadannan kasashe uku za su yi amfani da wannan damar wajen gyara tsarin da suka bi a baya wanda bai dace ba, wanda ya lalata martabar Turai da matsayin tattaunawa, tare da mayar da ita a matsayin...
    “Rasuwar Sarkin Zamfara babban rashi ne ga al’ummar jihar Zamfara, Arewa da ma ƙasar nan baki ɗaya. “Sarkin ya sadaukar da rayuwar sa a shekarun nan 10 da ya ya yi hana mulki a matsayin Sarkin Gusau na 15, wanda ya hau a ranar 16 ga watan Maris na shekarar 2015. Ya yi mulki cikin jajircewa da sadaukarwa. “Marigayin, kafin ya zama Sarki, ƙwararren ma’aikacin gwamnati ne, wanda har sai da ya kai matsayin Babban Sakatare a gwamnatin tsohuwar jihar Sakkwato da ta Zamfara. “Na rasa murshidin Uba mai basira, wanda ke nuna mani hanya, tare da sauran shugabanni a jiha. Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki ya gafarta masa kura-kuran sa, ya sa aljanna ce ce makoma. Daga kanmu,...
    Kafafen watsa labarun HKI sun ce wani mutum a cikin motar da yake tukawa ya nufi kan ‘yan sahayoniya a mahadar “Hahsrun” a kusa da “Kafar-Yona”dake yammacin Tul-Karam. Bayan da matumin ya take ‘yan sahayoniyar ya fice daga yankin ba tare an iya tsayar da shi ba. Majiyar ta kara da cewa; 9 daga cikin ‘yan sahayoniyar da su ka jikkata sojoji ne. Tashar talabijin din ta 12: ta ambaci cewa; Wanda ya take sojojin ya iya gudu daga wurin, ba tare da an tsayar da shi ba. Ita kuwa jaridar ‘ Yasrael Home” ta bayyana cewa; An baza ‘yan sanda a wurin da aka kai hari, domin gano inda maharin yake. Kungiyoyin Falasdinawa sun yi maraba da wannan harin,...
    Gwamnatin mamayar Isra’ila tana ci gaba da karya dokokin kasa da kasa, inda ta fara mamaye yankunan Gabar Yammacin Kogin Jordan da kwarin Jordan! Majalisar Dokokin yahudawan sahayoniyya ta Knesset ta kada kuri’a kan wani kudirin doka da ba shi da tushe don tilastawa gwamnatin mamayar Isra’ila cikakken ikon mallakar yankin Gabar Yammacin Kogin Jordan da kuma kwarin Jordan. Kuri’ar dai ta samu amincewar ‘yan majalisu 71, yayin da 13 suka nuna adawa da shi. Kungiyar Hamas ta dauki matakin a matsayin maras halacci a doka. A wani mataki da ya janyo ce-ce-ku-ce a cikin gida da na waje, Majalisar dokokin Isra’ila ta Knesset ta kada kuri’ar amincewa da wani kudirin doka da bai taka kara ya karya ba na...
    Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana aniyarta na ci gaba da hadin gwiwa da Bankin Lamunin Gidaje na Tarayya (Federal Mortgage Bank of Nigeria – FMBN) domin shawo kan matsalar karancin gidaje a jihar.   Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana hakan yayin wata ganawa da Babban Daraktan bankin Alhaji Shehu Usman Osidi a ofishinsa.   Gwamna Yusuf ya bayyana muhimmancin wannan hadin gwiwa, yana mai jaddada Kano a matsayin jiha ta biyu mafi yawan jama’a a Najeriya, inda adadin mutanenta ke kara karuwa cikin sauri.   “Kano tana daga sahun gaba wajen ci gaba, kuma samar da gidaje na daga cikin muhimman ginshikai na wannan ci gaba. Akwai bukatar samar da gidaje masu araha domin inganta rayuwar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta fasinja ta kasar Sin ta fidda bayani a jiya Talata cewa, cikin rabin farkon shekarar bana, yawan zirga-zirgar jiragen sama ta fasinja ya kai ton-kilomita biliyan 78.35, adadin da ya karu da kaso 11.4 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin a bara. Kana, yawan zirga-zirgar fasinjoji ya kai miliyan 370, wanda ya karu da kaso 6 bisa dari. A sa’i daya kuma, yawan zirga-zirgar hajoji da kunshin kayayyaki ya kai ton miliyan 4 da dubu 784, wanda ya karu da kaso 14.6 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. Cikin taron aiki da hukumar zirga-zirgar jigaren sama ta fasinja ta kira a jiyan, shugaban hukumar Song Zhiyong...