Tinubu na amfani da EFCC ya muzguna wa ’yan adawa — Atiku
Published: 12th, August 2025 GMT
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da amfani da Hukumar EFCC wajen yi wa masu adawa da ita barazana.
Saƙon da ɗan takarar shugaban ƙasa a Zaɓen 2023 ya wallafa wannan Talatar a shafinsa na X, na zuwa ne bayan tsare tsohon Gwamnan Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal da EFCCn ta yi.
A cewar Wazirin Adamawa, “dalilin da EFCC ta tsare tsohon Gwamnan Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, shi ne saboda yana cikin jam’iyyar adawa ta haɗaka.
“Wannan yana ƙara nuna yadda gwamnatin Tinubu ke ci gaba da yaɗa manufofinta na musgunawa, tsoratarwa, da rusa ‘yan adawa.”
Ya ƙara da cewa, “A yau dai duk wanda yake da alaƙa da ‘yan adawa to za a zarge shi da cin hanci da rashawa.
“Kuma da zarar an tilasta musu komawa kan tsarin tafiyar siyasar Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu, sai ya zama kamar an gafarta musu zunubansu ne.”
Martanin PDPIta ma jam’iyyar PDP reshen Jihar Sakkwato ta soki tsarewar da aka yi wa tsohon gwamnan, tana bayyana lamarin a matsayin “tuggun siyasa.”
Mai magana da yawun jam’iyyar a jihar, Hassan Sahabi Sanyinnawal, ya bayyana shi a matsayin yunƙurin rufe bakin jam’iyyun adawa da tsoratar da su.
Rahotanni sun ce EFCC da ke da alhakin yaƙi ta masu yi wa tattalin arziki ta’annati ta tsare Tambuwal a Abuja ranar Litinin kan zargin cire naira biliyan 189 ba bisa ƙa’ida ba, abin da ya saɓa wa dokar haramta sama-da-faɗi da kuɗi ta 2022.
Sai dai wasu majiyoyi daga hukumar sun ce gayyata ce kawai aka yi masa domin ya yi ƙarin haske kan batun, ba kama shi ba.
Tambuwal wanda ya taɓa zama shugaban Majalisar Wakilan Nijeriya, ya fara siyasarsa a jam’iyyar APC kafin ya koma PDP, sannan daga bisani ya shiga jam’iyyar haɗaka ta ADC, wacce ta ɗaura ɗamarar karɓe mulki daga hannun APC a 2027.
A bayan nan wasu rahotanni sun bayyana cewa EFCC ta gayyaci tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai kuma tsohon gwamnan Jihar Imo, Emeka Ihedioha, wanda ake sa ran zai amsa cikin mako ɗaya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Aminu Waziri Tambuwal Atiku Abubakar
এছাড়াও পড়ুন:
An ɗaure tsohon Firaminista Succes Masra shekaru 20 a Chadi
Wata kotu a N’Djamena, babban birnin Chadi, ta yanke wa tsohon firaminista kuma madugun adawa, Succes Masra, hukuncin ɗaurin shekaru 20 a gidan yari.
Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ya ruwaito kotun ta samu tsohon firaministan da laifin kalaman ƙiyayya, nuna wariyar ƙabilanci da kuma tayar da tarzomar da ta rikiɗe zuwa kisan kiyashi.
Dan wasan Barcelona Inigo Martinez ya koma Al-Nassr MDD za ta yi zaman gaggawa kan yunƙurin ƙwace GazaKotun a ranar Asabar ta ce ta sami Mista Masra da laifi kan rawar da ya taka wajen tayar da rikicin ƙabilanci wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 42 a ranar 14 ga Mayu — waɗanda galibi mata da yara ne a yankin Mandakao da ke kudu maso yammacin Chadi.
Tun a ranar Juma’ar da ta gabata ce, Lauyan gwamnati mai shigar ƙara, ya nemi kotun ta yanke wa Succes hukuncin ɗaurin shekaru 25 a gidan ɗan marina
An dai kama Masra a ranar 16 ga Mayu wanda aka tuhuma da “tayar da tarzoma da fitina, haɗin kai da ƙungiyoyi masu riƙe da makamai, taimakawa wajen kisan kai, ƙona gine-gine da kuma wulaƙanta kaburbura.”
An gurfanar da tsohon firaministan tare da wasu maza kusan 70 da ake zargi sun taka rawa a wannan kisa.
Masra, wanda asalinsa ɗan kudancin Chadi ne ya fito daga ƙabilar Ngambaye, kuma yana da karɓuwa sosai a wajen yawancin Kiristoci da masu bin addinin gargajiya a yankin kudu, waɗanda ke ganin ana nuna musu wariya daga gwamnatin da Musulmai suka fi rinjaye a N’Djamena.
A lokacin shari’ar, lauyoyinsa sun ce babu wata hujja tabbatacciya da aka gabatar a kotu da za ta tabbatar da laifinsa.
A watan Yuni, lauyoyinsa sun ce ya yi yajin cin abinci na kusan wata guda a gidan yari.
Masra ya tsere daga Chadi bayan mummunan matsin lambar da aka riƙa yi wa mabiyansa a 2022, sai dai ya dawo ne a ƙarƙashin afuwar da aka cimma a 2024.
AFP