Bankin Duniya zai kashe $300m domin inganta rayuwar ’yan gudun hijira a Arewacin Nijeriya
Published: 12th, August 2025 GMT
Bankin Duniya ya amince da bayar da dala miliyan 300 domin aiwatar da wani sabon shiri da zai inganta rayuwar ’yan gudun hijira da kuma al’ummomin da suka ba su matsugunni a Arewacin Nijeriya.
Bankin ya bayyana cewa a ƙarƙashin shirin mai suna Solutions for the Internally Displaced and Host Communities Project wato SOLID, wanda aka amince da shi a ranar 7 ga Agusta, za a lalubo hanyoyin da za a bi wajen taimakon ’yan gudun hijira, da ma garuruwan da suke rayuwa a ciki.
Ya bayyana cewa shirin SOLID zai ruɓanya ƙoƙarin da gwamnati ke yi da ma wanda sauran abokan hulɗa suka riga suka gudanar, ciki har da Shirin Farfado da Yankunan Da Rikici Ya Shafa (MCRP).
Haka kuma, bankin ya jaddada cewa rikice-rikicen tsaro da rashin kwanciyar hankali da ke gudana a yankin sun raba mutane fiye da miliyan 3.5 da muhallansu, lamarin da ya shafi ababen more rayuwa, wanda a cewar bankin hakan ya sa ababen more rayuwan suka yi ƙaranci a garuruwan da suke zama.
Daraktan Bankin Duniya a Nijeriya, Mathew Verghis, ya ce: “Muna farin cikin ƙaddamar da wannan shiri mai matuƙar tasiri da zai taimaka wa Nijeriya magance ƙalubalen da take fuskanta wadanda suka shafi ’yan gudun hijira”
“Daga cikin ɓangarorin da za mu mayar da hankali akwai rage illolin sauyin yanayi, samar da haɗin kai ta hanyar sasanci, tallafa wa iyalai da inganta ababen more rayuwa.
“Muhimman fannoni sun haɗa da gina ababen more rayuwa masu jure wa sauyin yanayi, ƙarfafa zaman lafiya, tallafa wa hanyoyin samun abin yi, da kuma ƙarfafa cibiyoyi domin su iya magance matsalolin da tsugunar da ’yan gudun hijirar ya haifar.”
Bayanai sun ce shirin SOLID na iya amfanar da mutane kusan miliyan 7.4, wadanda daga cikinsu miliyan 1.3 ’yan gudun hijira ne.
Za a aiwatar da shirin ne ta hanyar tsari na haɗin gwiwar al’umma, tare da shigar dukkan bangarorin gwamnati da kuma haɗin kai da ƙwararrun abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan gudun hijira Bankin Duniya ababen more rayuwa yan gudun hijira
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaba Xi Jinping Ya Gabatar Da Shawarwari Hudu A Taron Kolin Mata Na Duniya
Na farko, hada kai don samar da yanayi mai kyau ga ci gaban mata. Na biyu, a karfafa abubuwan da za su habaka ingancin ayyukan mata cikin hadin kai. Kana na uku, a gina tsarin kare hakkin mata tare. Sai na hudu, a bude sabon babin hadin gwiwa tsakanin mata a duniya.
Za a gudanar da taron kolin mata na duniya a yau da gobe Talata a birnin Beijing. Kuma tuni shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan, suka yi musafaha da shugabannin tawagogin kasashe, da kungiyoyin duniya da suka halarci taron, tare da daukar hotuna tare da su. (Amina Xu)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA