Fasahohin AI Sun Bude Sabon Babi Na Hadin Gwiwar Sin Da Afirka
Published: 12th, August 2025 GMT
Lokacin da bukatun Afirka suka hadu da karfin Sin, muna da dalilin yin imani cewa, tare da tallafin dandalolin kamar su “dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC)” da shawarar “ziri daya da hanya daya”, hadin gwiwar AI tsakanin Sin da Afirka tabbas za ta samar da samako mai armashi nan gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya tafi Rome don halartar taro kan sha’anin tsaro
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tafi birnin Rome na Ƙasar Italiya, domin halartar taron shugabannin ƙasashe kan sha’anin tsaro.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin labarai, Bayo Onanuga, ya ce za a fara taron ne a ranar 14 ga watan Oktoba, kuma zai mayar da hankali kan matsalar tsaro da ke addabar yankin Yammacin Afirka.
’Yan sanda sun ceto mutum 10 daga hannun ’yan bindiga a Kaduna Talauci da tsangwama na hana yara mata karatu a Gombe — KwamishinaTaron na ‘Aqaba Process’ an kafa shi ne a shekarar 2015 ta hannun Sarki Abdullah II na Ƙasar Jordan, kuma ana gudanar da shi tare da haɗin gwiwar Jordan da ƙasar Italiya.
Taron na nufin tattauna hanyoyin yaƙi da ta’addanci da kuma magance matsalolin tsaro da ke adabbar ƙasashe daban-daban, musamman a yankin Yammacin Afirka.
Taron zai haɗa shugabannin ƙasashe na Afirka, jami’an leƙen asiri da na tsaro, da wakilan ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da na ƙungiyoyin fararen hula, domin tattauna yadda za a magance matsalolin tsaro da ke addabar yankin.
Za a tattauna kan yadda ƙungiyoyin ta’addanci ke yaɗuwa a Yammacin Afirka, alaƙa tsakanin masu laifi da ’yan ta’adda, da kuma alaƙar da ke tsakanin ta’addanci a yankin Sahel.
Hakazalika, za a tattauna yadda za a daƙile yaɗuwar aƙidar ta’addanci a Intanet da kuma lalata hanyoyin sadarwar da ’yan ta’adda ke amfani da su wajen yaɗa ra’ayoyinsu da ɗaukar sababbin mabiya.
Shugaba Tinubu zai kuma tattauna da wasu shugabannin ƙasashe don neman hanyoyin daƙile matsalar tsaro da ke addabar yankin.
Tinubu ya samu rakiyar Ministan Harkokin Waje, Ambasada Bianca Odumegwu–Ojukwu; Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar.
Sauran sun haɗa daMai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu; Darakta-Janar na Hukumar Leƙen Asiri ta Ƙasa (NIA), Ambasada Mohammed Mohammed; da wasu manyan jami’an gwamnati.