A wani bayanin hadin giwa wanda ministocin harkokin wajen kasashe 27 suka rattabawa hannu, ya bukaci firai ministan HKI Benyamin Natanyahu ya bude hanya don shigoda abinci cikin gaza, don kawo karshen yunwa da ta bayyana a fili.

Tashar talabijan ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa daga cikin kasashen da suka sanyawa bukatar hannu har da kasashen Faransa da Burtaniya da kuma tarayyar Turai a yau Talata.

Bayanin ya kara da cewa lalle musibar yunwa da ta sami Gaza, ta kai matsayinda mutum ba zai sawwara shi ba, suna bukatar Natanyahu ya bada izinin a shigar da kayakin agaji zuwa gaza ba tare da bata lokaci ba.

A wani labarin kuma yawan mutanen da abincin da ake jefawa ta sama a gaza suka kashe ya kai 23 a yayinda wasu mutane 124 suka ji rauni.

Banda kasashen faransa da Burtania da kuma tarayyar Turai, kasashen da suka sanyawa wanan bukatar hannu sun hada da Australia Canada da Japan. Har’ila yau da Jamus, Italiya, Newzeeland. Wasu daga cikin kasashen sun bayyana rashin amincewarsu da kara mamayar gaza da HKI take son yi.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran: Duk Wani Sabon Hari, Zai Fushin Sojojin Kasar August 12, 2025 Larijani: Iraki Bata Daukan Umarni Daga JMI August 12, 2025 Iran Tace Ma’aikatar Harkokin Waje Kasarce Take Kula Da Lamuran Makamacin Nukliyar Kasar August 12, 2025 Armenia Ta Tabbatarwa Iran Zata Kula Da Muradunta Bayan Yarjeniya Da Azarbaijan A Amurka August 12, 2025 Araqchi: Babban Abin Kunya Ne Shuru Gwamnatocin Yammacin Turai Kan Abin Da Ke Faruwa A Gaza August 12, 2025 Larijani Ya Ce: ‘Yan Gwagwarmaya Sun San Abubuwan Da Suka Dace August 12, 2025 Iraki Ya Bukaci Tattaunawa Tsakanin Larabawan Yankin Tekun Farisa Da Iraki Da Iran August 12, 2025 Italiya Ta Janye Jirgin Ruwanta Daga Taken Bahar Maliya Saboda Barazanar ‘Yan Gwagwarmayar Yemen August 12, 2025 Majalisar Dinkin Duniya Ta Sanar Da Mutuwan Mutane 60 Saboda Yunwa A El-Fasher Na Sudan August 12, 2025 Iran da Iraki sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro August 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu Ya Nuna Farin Cikinsa Bisa Bayyanar Daliban Kebbi, Ya Bukaci a Ceto Sauran

Daga Bello Wakili 

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana farin cikinsa bisa dawowar ’yan mata 24 da ’yan ta’adda suka sace a Maga, Jihar Kebbi.

’Yan ta’addan sun kai hari makarantar  ranar 17 ga wantan Nuwamban 2026, inda suka yi awon gaba da ’yan matan, jim kaɗan bayan wata rundunar soji ta bar harabar makarantar.

Lamarin Kebbi ya haifar da wasu sace-sace makamanta a Eruku da ke Jihar Kwara da kuma Papiri a Jihar Neja.

An sako dukkan mutune 38 da aka sace a Eruku ranar Lahadi, inda a wannan ranar ce shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) Jihar Neja ya ce an samu yara 50 daga cikin ɗaliban makarantar Katolika da suka ɓace a gidajen iyayensu.

Shugaba Tinubu ya yaba wa jami’an tsaro bisa ƙoƙarin da suka yi wajen ganin an kubutar da dukkan mutanen da ’yan ta’adda suka sace.

Ya umarci jami’an tsaro da su ƙara ɗaukar matakan gaggawa don ceto sauran ɗaliban da har yanzu ke hannun ‘yan bindiga.

“Ina farin cikin cewa an samu dukkan ’yan mata 24. Ya zama wajibi mu ƙara tura jami’an tsaro  yankunan da ke da rauni don hana sake faruwar irin wannan lamari. Gwamnatina za ta bayar da dukkan tallafin da ake buƙata don cimma haka,” in ji Shugaba Tinubu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Palasdinawa Sun Karbi Gawawwakin Shahidai 15 Daga ‘Yan Mamaya
  • HKI Tana Amfani Da Tsagaita Wuta A Gaza Don Sake Shata Kan Iyakokin Yankin
  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Falasdinu Ta Sanar Cewa Akalla Yan Mata 33000 Ne Isra’ila Ta Kashe A Gaza
  • Isra’ila Tana Ci Gaba Da Rushe Gidaje A Yankin Gaza
  • Aljeriya Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Dauki Mataki Don Kawo Karshen Ta’asan HKI A Yankin Asiya Ta Kudu
  • Tinubu Ya Nuna Farin Cikinsa Bisa Bayyanar Daliban Kebbi, Ya Bukaci a Ceto Sauran
  • Hizbullah: Isra’ila na kuskure idan ta na tunanin kashe-kashen kwamandodinmu zai kawo karshen kungiyar
  • Bincike : Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa Akalla 100,000 a Gaza
  • Amurka Da HKI Sun Kawo Karshen Hukumar GHF Mai Raba Abinci A Gaza
  • Hamas Ta Ce Keta Hurumin Tsagaita Wutan Da HKI Take Yi Zai Iya Kawo Karshen Tsagaita Wutar