Aminiya:
2025-08-12@18:38:49 GMT

Nijeriya ta sake ƙulla alaƙar tsaro da Isra’ila

Published: 12th, August 2025 GMT

Nijeriya da ƙasar Isra’ila sun sake jaddada aniyarsu ta ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro a fannoni masu muhimmanci kamar yaƙi da ta’addanci, musayar bayanan sirri, samar da kuɗin tsaro da kuma horaswa ta musamman.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwar haɗin gwiwa wadda Ƙaramar Ministar Harkokin Wajen Nijeriya, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, da Mataimakiyar Ministan Harkokin Waje ta Isra’ila, Sharren Haskel-Harpaz suka fitar bayan wani taro na musamman da suka gudanar ranar Litinin a Abuja.

Tinubu na amfani da EFCC ya muzguna wa ’yan adawa — Atiku Amurka da China sun dakatar da harajin da suka ƙaƙaba wa juna

Sanarwar, wadda mai magana da yawun Ofishin Ƙaramar Ministar Harkokin Wajen, Dokta Magnus Eze ya fitar, ta ce taron ya nuna alaƙa mai ɗorewa da muhimmanci tsakanin ƙasashen biyu.

A  yayin taron, wakilan ƙasashen biyu sun tattauna batutuwan da suka shafi tsaro a duniya, musamman yaƙi da ta’addanci, da kuma inganta hulɗar siyasa da tattalin arziki.

Ministocin biyu sun yi ƙara jan hankali kan barazanar ta’addanci a duniya, inda suka ce dole ne ƙasashe su haɗa kai wajen yaƙi da shi, musamman wajen samun bayanai kan hanyoyin samar da kuɗaɗen da ke ɗaukar nauyin ta’addanci.

Mahalarta taron

Haka kuma, ƙasashen biyu sun amince su ƙara haɗin kai a fannonin da suka shafi ƙasa da ƙasa tare da mara wa juna baya a muhimman batutuwa masu kawo ci gaba.

Baya ga tsaro, taron ya mayar da hankali kan amfani da fasaha da ƙirkire-ƙirkire wajen kula da iyakoki, inganta ƙwarewar makamar aiki, musayar al’adu, yawon buɗe ido, noma, da ayyukan jakadanci da shige-da-fice.

Kazalika, ƙasashen sun amince da shirye-shiryen musayar ma’aikata da ziyarar ƙara ilimi, tare da kafa tsari na musamman domin ci gaba da tattaunawa da haɗin gwiwa a nan gaba.

A wani ɓangare na taron, an yi muhawara kan fasahar zamani wadda Ambasada Janet Olisa daga Ma’aikatar Harkokin Waje ta Nijeriya ta jagoranta tare da Ambasada Sharon Bar-Li daga Ma’aikatar Harkokin Waje ta Isra’ila.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Isra ila Nijeriya Sharren Haskel Harpaz Tsaro

এছাড়াও পড়ুন:

MDD za ta yi zaman gaggawa kan yunƙurin ƙwace Gaza

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kira taron gaggawa a wannan Lahadin domin tattauna ƙudirin Isra’ila na ƙwace iko da Zirin Gaza.

Wannan shirin, wanda Majalisar Tsaron Isra’ila ta amince da shi a ranar Juma’a, ya jawo suka daga ƙasashen duniya.

Al-Hilal ta ɗauki Nunez daga Liverpool Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram a Borno

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres ya kwatanta shirin da abin da zai ƙara dagula lamura a fadan da aka kwashe watanni 22 ana yi.

Kasashen Turai da ke cikin Kwamitin Sulhun da suka hada da Denmark da Faransa da Girka da Burtaniya da Slovenia ne suka kira wannan zaman gaggawan a birnin New York na Amurka.

DW ya ruwaito cewa, dukkan mambobin Kwamitin Sulhun banda Amurka sun goyi bayan wannan zaman na yau Lahadi wanda zai dubi abinda ya dace a yi a kan yunkurin na Isra’ila.

Za a fara zaman ne da misalin ƙarfe 10 na safe wato ƙarfe biyu kenan agogon GMT da Ghana.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yan Nijeriya Miliyan 14 Sun Yi Bikin Murnar Karɓar Kyautar N23m Daga Bankin STANBIC IBTC
  • Ruwan Wutan sojan Nijeriya Ya Kashe ‘Yan Bindiga A Zamfara.
  • Inganta Harkokin Gwamnati: Oyebanji Ya Sauke Kwamishinoni 19
  • Ana Neman Daukar Karin Matakin Kawar Da Shingayen Dake Hana ‘Ya’ya Mata Zuwa Makaranta A Zamfara
  • Runduunar ‘Yan Sandan Jihar kwara Ta Karfafa Tsaro A Banbila
  • Kwamitin Tsaro ya yi zaman gaggawa kan Shirin Isra’ila na mamaye Gaza
  • Ana Zanga-Zanga A Isra’ila Kan Shirin Netanyahu Na Mamaye Gaza
  • MDD za ta yi zaman gaggawa kan yunƙurin ƙwace Gaza
  • Gwamna Yusuf Ya Amince Da Korar Wasu Mataimaka Biyu Bisa Hannu Akan Belin Wani Dilan Miyagun Kwayoyi