Leadership News Hausa:
2025-11-27@22:42:48 GMT

Gwamnatin Kano Za Ta Horar Da Tubabbun ‘Yandaba 718 Sana’o’i 

Published: 12th, August 2025 GMT

Gwamnatin Kano Za Ta Horar Da Tubabbun ‘Yandaba 718 Sana’o’i 

Gwamnatin jihar Kano ta gana da shugabannin ‘yan bangar siyasa da suka tuba a jihar tare da yi musu alkawarin tallafa musu ta hanyar sauya tunaninsu da horar da su sana’o’i da kuma kayan aikin fara sana’ar. Taron wanda ya gudana a ranar Talata a Kano ya samu halartar tubabbun ‘yan barandan siyasa da masu satar waya kusan 718.

Gwamnatin Kano Ta Bayar Da Kwangilar Hanyoyi 17 Akan Naira Biliyan 40.8 Sin Ta Gabatar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Kan Taron Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakaninta Da Amurka A Stockholm Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Ibrahim Waiya ya yi kira ga mahalarta taron da su rungumi tuba da gaskiya tare da bayar da hadin kai ga shirin gwamnati na sauya rayuwarsu. “An shirya tsaf, kawai jira ake ‘yansanda da hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa ta dauki bayananku. “Waɗannan matakai ne masu mahimmanci waɗanda ta hanyarsu za ku zaɓi irin sana’ar da kuke son koya kuma za a horar da ku duk irin sana’ar da kuka zaba, daga karshe a gwangwajeku da kayan aikin fara sana’ar,” in ji shi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnan Bauchi ya yi ta’aziyyar rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Bauchi, a matsayin babban rashi ga al’umma.

Gwamnan ya bayyana malamin a matsayin jagoran haɗin kai, zaman lafiya, da fahimtar juna tsakanin Musulmi da mabiya addinai daban-daban.

’Yan sanda sun gano harsasai 210 a kan titin Zariya-Funtuwa Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa

A cikin saƙon ta’aziyya da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Mukhtar Gidado, ya sanya wa hannu, gwamnan ya ce Gwamnatin Jihar Bauchi tana alhinin rasuwar malamin.

Dahiru Bauchi, ya rasu da safiyar ranar Alhamis, 27 ga watan Nuwamba, 2025 a Bauchi, yana da shekara 102.

Gwamnan, ya ce Sheikh Dahiru Bauchi babban malami ne na addinin Musulunci, mai imani, tawali’u da hikima.

A cewarsa ya sadaukar da rayuwarsa wajen yaɗa addinin Musulunci, koyar da Alƙur’ani, da kuma taimaka wa mutane wajen tarbiyya.

Marigayin, ya koyar da dubban ɗalibai da suka haddace Alƙur’ani tare da yaɗa addinin Musulunci a sassan nahiyar Afrika.

Gwamnan, ya ƙara da cewa gudunmawar da marigayin ya bayar a fannin tafsiri, fiqhu da tarihi sun taka muhimmiyar rawa wajen ɗora al’umma kan turbar tsira.

Har ila yau, ya ce Gwamnatin Jihar Bauchi za ta ci gaba da girmama marigayin ta hanyar tallafa wa makarantu da manufofin da ya gina, musamman a fannin ilimin addinin Musulunci, tarbiyya da ci gaban al’umma.

Ya yi addu’a rAllah ya gafarta masa kurakuransa, ya sanya shi aAljannatul Firdausi, ya kuma bai wa iyalansa, mabiyansa da ɗaukacin al’ummar Musulmi haƙurin rashinsa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • El-Rufai ya koma jami’yyar haɗaka ta ADC
  • Gwamnan Bauchi ya yi ta’aziyyar rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
  • Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai
  • UNIFIL: Isra’ila tana sabawa wa kudurorin MDD a cikin  Lebanon
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Yi Wa Yara Miliyan 1.5 Rigakafin Cutar Shan Inna
  • Kano Pillars ta kawo ƙarshen wasanni 8 ba tare da nasara ba
  • An buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarawaba a Katsina
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 8 a Kano
  • Abbas Arakci Ya Yi Gargadi Akan Abin Zai Biyo Bayan Keta Dokokin Duniya Da “Isra’ila” Take Yi A Cikin Wannan Yankin
  • NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta