Giyar mulki Na Jan Trump – Ƴan Democrats
Published: 12th, August 2025 GMT
‘Yan Democrats a Amurka sun zargi Donald Trump da mutumin da giyar mulki ke ruɗawa, bayan ya ce zai tura jami’an rundunar tsaro ta ƙasar birnin Washington don yaƙi da laifukan da ake ganin sun gagari ƴansandan birnin.
Magajiyar birnin Muriel Bowser, ta ce matakin bai dace ba, sannan ta musanta batun da shugaban ke yi cewa an gaggara daƙile masu aikata laifi.
‘Yan Democrats a majalisa, sun ce wannan mataki babu wani abin da zai haifar face ‘tsoro da hargitsi, kuma wannan yunƙuri ne kama hanyar kama-karya.
Shugaban masu rinjaye a majilsar wakilai ya ce Mista Trump ya mayar da mulki kamar wata sarauta.
Shi dai Trump ɗin ya ce birnin washington a cike yake da masu gararamba a tittuna suna aikata miyagun ayyuka kuma dole ya kawo gyara.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Mutane 2 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Kebbi
Aƙalla mutane biyu ne suka mutu a rikicin da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a unguwar Dambo, wani kauye da ke da tazarar ’yan kilomita daga Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi.
Wani mazaunin yankin mai suna Ɗanladi Usman ya ce rikicin ya fara ne bayan an kashe wani mutum mai suna Sule yayin da yake aiki a gonarsa.
“Kashe Sule ya tayar da hankulan al’umma, inda manoma suka ɗauki fansa suka kashe wani makiyayi da har yanzu ba a gano sunansa ba,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa makiyayan sun sha faɗa da manoma a kwanakin baya bayan sun aike musu da sako cewa su hanzarta girbe amfanin gonakinsu domin za su riƙa wucewa da shanunsu ta gonakin nan ba da daɗewa ba.
An yi jana’izar sojojin da ’yan bindiga suka kashe a Kebbi Rashin wutar lantarki ya rusa harkoki a Kaduna, Kano da Katsina“A lokacin da wasu manoma suka je gonakinsu domin yin aiki, sai makiyaya suka kai musu hari, daga nan ne aka shiga tashin hankali,” in ji shi.
Wani mazaunin yankin, Abubakar Aliyu, ya roƙi gwamnati da ta kawo ƙarshen wannan rikici na dogon lokaci tsakanin manoma da makiyaya.
“Wannan matsala ba sabuwa ba ce, kuma sarakunan gargajiya sun san da ita. Muna fatan a samu adalci ga waɗanda abin ya shafa, kuma gwamnati ta kawo ƙarshen wannan rikici,” in ji shi.
Rundunar ’yan sanda a jihar ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba domin jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Nafiu Abubakar, ba a iya samun sa a waya ba lokacin da ake haɗa wannan rahoto.