Italiya Ta Janye Jirgin Ruwanta Daga Taken Bahar Maliya Saboda Barazanar ‘Yan Gwagwarmayar Yemen
Published: 12th, August 2025 GMT
Kasar Italiya ta janye jirgin ruwanta daga tekun Bahar Maliya bayan gazawarta a fage kwamawa da kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen
Kasashen Turai sun ci gaba da janye jiragen ruwa da jiragen yaki daga tekun Bahar Maliya, lamarin da ke tabbatar da hukuncin da kasashen nahiyar suka dauka na cewa ci gaba da zamansu a cikin tekun ba shi da amfani bayan da Dakarun ‘yan gwagwarmyar Yemen suka yi gargadin cewa; Duk masu alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila zasu fuskanci hare-haren makamai masu linzami da na jiragen saman yaki.
Kwanaki biyu bayan sanar da janye jirgin ruwan Faransa daya tilo, da rundunar Turai ta kafa don kare jigilar jiragen haramtacciyar kasar Isra’ila, “Aspedes,” ta sanar da janye jirgin ruwan Italiya “Caio Duilio” daga yankin tekun Bahar Maliya.
Ana sa ran sauran kasashen Turai da ke da jiragen ruwa a yankin za su janye jiragensu daga tekun Bahar Maliya a cikin lokaci mai zuwa, a daidai lokacin da kasashen Turai ke kara nuna damuwa game da ayyukan kasar Yemen da ke tafe a wani mataki na hudu na ci gaba da yaki da haramtacciyar kasar Isra’ila.
Ya kamata a lura da cewa jirgin ruwan “Caio Duilio” wani nau’i ne na Andrea Doria mai tarwatsa jiragen Ruwan yaki na Italiya, wanda ya ƙware a fagen tsaron iska. An ƙaddamar da shi a cikin 2007 kuma ya shiga aiki tare da sojojin ruwa na Italiya a ranar 3 ga Afrilun shekara ta 2009. Italiya dai ta sanar da shiga cikin haɗin gwiwar Turai don kare jigilar jiragen gwamnatin mamayar Isra’ila a ranar 19 ga Fabrairu na bara.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Majalisar Dinkin Duniya Ta Sanar Da Mutuwan Mutane 60 Saboda Yunwa A El-Fasher Na Sudan August 12, 2025 Iran da Iraki sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro August 12, 2025 Masar ta yi gargadin daukar tsauraran matakai domin kare muradunta August 12, 2025 Iran ta yi Allah wadai da kisan kiyashin da Isra’ila ta yi wa ‘yan jarida a Gaza August 12, 2025 Gaza: Yunwa ta kashe Falastinawa 5 a cikin kasa da Sa’o’i 24 da suka gabata August 12, 2025 Ministan tsaron Italiya ya caccaki gwamnatin Netanyahu kan batun Gaza August 12, 2025 Araghchi: Mataimakin Shugaban IAEA Zai Ziyarci Tehan َA Wannan Talata August 11, 2025 Iran: Lebanon Tana Da ‘Yancin Kare Kanta Da Makamanta August 11, 2025 Mali: An Kama Sojoji Fiye da 40 Bisa Zargin Yunkurin Juyin Mulki August 11, 2025 Iraki: Larijani Da Sudani Sun Gana A Bagdaza August 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: tekun Bahar Maliya
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan tsaron Italiya ya caccaki gwamnatin Netanyahu kan batun Gaza
Ministan tsaron kasar Italiya Guido Crosetto ya bayyana cewa gwamnatin Isra’ila ta fita hayyacinta a yakin da ake ci gaba da yi a zirin Gaza, yayin da kuma yake nuni da cewa Italiya a shirye take ta bi sahun kasashen duniya wajen kakaba wa Isra’ila takunkumi.
A cikin wata hira da jaridar La Stampa ta Italiya, Crosetto ya bayyana cewa, abin da ke faruwa a Gaza ba abu ne da za a amince da shi ba.
Crosetto ya kuma jaddada cewa Italiya ta ci gaba da jajircewa wajen bayar da agajin jin kai, amma ya kara da cewa, “Yanzu dole ne mu nemo hanyar da za mu tilasta wa Netanyahu sake yin tunani.”
Dangane da yuwuwar kakaba takunkumi, Crosetto ya yi nuni da cewa, mamayar Gaza da wasu munanan ayyuka da Israila ke yi a gabar yammacin kogin Jordan, na nuni da cewa akwai bukatar daukar kwararan matakai da zasu tilasta Netanyahu ja da baya.
Crosetto ya ci gaba da cewa, matakan nasu ba nag aba da Isra’ila ba ne, amma matakai ne na ceto Isra’ila daga ayyukan gwamnatinsu wadda ta rasa daidaito kuma ta fita hayyacinta na ‘yan adamtaka.
A baya-bayan nan dai Italiya tare da Australia da Jamus da New Zealand da kuma Birtaniya sun bayyana rashin amincewarsu da shirin Isra’ila na mamaye Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Araghchi: Mataimakin Shugaban IAEA Zai Ziyarci Tehan َA Wannan Talata August 11, 2025 Iran: Lebanon Tana Da ‘Yancin Kare Kanta Da Makamanta August 11, 2025 Mali: An Kama Sojoji Fiye da 40 Bisa Zargin Yunkurin Juyin Mulki August 11, 2025 Iraki: Larijani Da Sudani Sun Gana A Bagdaza August 11, 2025 Mafi yawan Kasashen Duniya Sun Amince Da Samarda Kasar Falasdinu August 11, 2025 Mahukuntan Iraki: Adadin Masu Ziyarar Arba’een Daga Kasashen Ketare Zai Iya Haura Miliyan 40 August 11, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Sun kai Wasu Munanan Hare-Hare Kan Yankunan Zirin Gaza August 11, 2025 Kwamitin Tsaron MDD Ya Gudanar Da Zaman Taro Kan Aniyar Isra’ila A Kan Gaza August 11, 2025 Shugaban Iran: Dole ne duniya ta kawo karshen laifukan yakin Isra’ila a Gaza August 11, 2025 Israila Ta Kashe ‘Yan Jarida 4 A Harin Da Ta Kai Kan Tantinsu A Gaza August 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci