Aminiya:
2025-08-12@09:00:18 GMT

EFCC ta tsare tsohon Gwamnan Sakkwato Tambuwal kan zargin N189bn

Published: 12th, August 2025 GMT

Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ta tsare tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal kan zargin almundahana.

A ranar Litinin ce EFCC ta tsare Tambuwal bayan da ya masa gayyatar da ta yi masa zuwa Ofishinta domin amsa tambayoyin kan badaƙalar Naira biliyan 189.

Majiyoyi sun shaida wa wakilinmu cewa Hukumar EFCC ta tsare tsohon Shugaban Majalisar Wakilan ne kan zargin cirar Naira biliyan 189.

Wata majiya a EFCC ta bayyana cewa, “Ba kama shi aka yi ba, zuwa ya yi domin amsa tambayoyi kan yadda ya yi amfani da Naira biliyan 189. Amma da ya kasa bayani sai aka tsare shi. Ina ganin shi ya sa mutane ke cewa an kama shi.

“Zai ci gaba da kasancewa a hannun har zuwa lokacin da zai iya bayar da cikakken bayani game da yadda ya kashe Naira biliyan 189 a lokacin da yake gwamna.”

Ta ci gaba da cewa, “Ka san abin da Naira biliyan 189 zai iya yi a Jihar Sakkwato kuwa? Yadda aka cire kuɗaɗen ya saɓa wa Ɗokar Haramta Safarar Kuɗaɗen Haram. Saboda haka dole sai ya yi cikakken bayani.”

Aminiya ta samu labarin cewa EFCC ta gayyaci tsohon Gwamnan Jihar Imo, Emeka Ihedioha domin amsa tambayoyi a cikin wannan makon.

Idan ba a manta ba, Ihedioha shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai a lokacin da Tambuwal yake matsayin shugaban majalisar.

Daga makusantan Tambuwal

A martaninsa kan wannan damvarwa, wani makusancin Tambuwal ya ya yi zargin cewa wannan “abin siyasa ce 100%”.

Ya yi zargin cewa abin ya samo asali ne tun wata huɗu da suka gabata inda wasu muƙarraban gwamnati suka buƙaci Tambuwal ya shiga “tafyar siyasar Tinubu.”

“Da ya tuntuɓe mum sai muka cika da mamakin yadda za a yi, da hankalinmu, mu shiga tafiyar gwamnatin da ta jefa mutane cikin wannan talauci da rashin tsaro da ke addabar musamman yankin Arewa,”in ji shi.

A cewarsa bayan rashin jin wata ƙwaƙƙwarar magana daga Tambuwal ne kimanin makonni uku da suka gabata, sai EFCC ta aiko masa da takardar gayyatar neman bayanai kan zamanin mulkinsa a Jihar Sakkwato.

“Sai muka nemi Hukumar ta fayyace haƙikanin abin da take neman bayanai a kai, amma ba ta yi ba. Don haka ya buƙaci su tuntuɓi gwamnatin jihar ko akwai wani abu da ba ta gamsu da shi ba game da gwamnoninsa.

“Amma duk da cewa ba su yi cikakken bayani ba, muna zargin yana da alaƙa da batun yadda aka gudanar da Kuɗaɗen Bankin Duniya da aka bayar a zamanin mulkinsa. Ta banki aka tura kuɗaɗen kuma Tambuwal ya samu sahalewar Bankin Duniya,” a cewarsa, amma ya nemi kasa a bayyana sunansa.

Ya ce tsohon Gwamnan ya samu gayyatar EFCC, wadda ya amsa a ranar Litinin kuma ya samu labarin cewa hukumar ta amince cewa zainiya samun beli.

A cewarsa, makusantan Tambuwal sun riga sun cika sharuɗan belin tsohon gwamnan, amma hukumar ta zaɓi ta ci gaba da ajiye shi zuwa ranar Talatar nan.

Shi ma wani makusancin Tambuwal ya alaƙanta tsarewar da siyasa, yana mai bayyana cewa, “Gwamnan Sakkwato na yanzu shi ne mataimakin gwamnan a lokacin mulkin Tambuwal kafin daga baya su raba gari.

“Shi (Gwamna Aliyu Sokoto) yana cikin waɗanda aka ɗauki mataki kan abubuwa da dama a jihar a zamanin Tambuwal. Saboda haka idan za a yi adalci ya kamata shi ma Gwamna EFCC ta ambaci sunansa a binciken, duk da cewa a yanzu yana da rigar kariya.

“Duk da cewa EFCC ta gayyaci wasu jami’an gwamnatin Tambuwal domin amsa tambayoyi. Amma abin da muke buƙata shi ne a yi adalci ba ɗaukar fansa ba. A daina tozarta mutane saboda neman biyan buƙatun siyasa,” in ji shi.

EFCC ta gayyaci Ihedioha

Wata majiya ta bayyana cewa an yi wa tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai a zamanin Tambuwal, Emeka Ihedioha tayin shiga tafiyar siyasar Tinubu kimanin wata shida da suka gabata. Shi ma Ihedioha, EFCC ta gayyace shi domin amsa tambayoyi a cikin wannan makon.

A wata wasika da hukumar ta hannun Daraktan Bincike Abdukarim Chukkol, a ranar 18nga watan Yuli, 2025, ta aike wa Sakataren Gwamnatin Jihar Iko ta buƙaci samun wasu bayanai daga wasu jami’an gwamnatin jihar.

Wasiƙar ta buƙaci jami’an su bayyana a ofishin hukumar EFCC a ranar Talata, 11 ga Agusta, 2025, domin amsa tambayoyi.

“Ana buƙatar su zo da takardun izinin duk kuɗaɗen da aka kashe daga ranar 29 ga watan Mayu, 2019 zuwa 14 ga watan Janairu, 2020.”

Majiyar da ta nuna wa wakilinmu takardar ta bayyana cewa Ihedioha ya dawo daga tafiyar da ya yi daga ƙasar waje domin amsa gayyatar EFCC.

Ihedioha wanda a yanzu ya koma jam’iyyar ADC ya kasance Gwamnan Jihar Imo daga ranar 29 ga watan Mayu, 2019 zuwa 14 ga watan  January, 2020, lokacin da Kotun Ƙoli ta soke zaɓensa tare da ayyana Hope Uzodinma, a matsayin wanda ya yi nasara.

Alaƙar Tambuwal da Atiku da ADC

Sanata Tambuwal, wanda ɗan babbar Jam’iyyar adawa ta PDP ne ya bayyana goyon bayansa ga tafiyar haɗakar ’yan adawa ta sabuwar Jam’iyyar ADC.

An gan shi tare da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar da ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai a yayin taron da suka shiga ADC a ranar 2 ga watan Yuli 2025.

A taron ne suka amince da ADC a matsayin inuwar da za su yi amfani da ita domin ƙalubalantar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 da ke tafe.

Kazalika Tambuwal ya kasance tare da Atiku a lokacin taron jana’izar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a mahaifasrsa da ke Daura, Jihar Katsina.

Sai dai saɓanin Atiku da ya sauya sheka daga PDP zuwa ADC, har yanzu Tambuwal bai fice daga PDP ba. Haka kuma yana da alaƙa mai ƙarfi da Atiku, wanda ake ganin ta wuce siyasa zuwa ƙawancen adawa.

Alakarsu ta fara ɗaukar hankali ne a lokacin babban zaɓen ’yan takarar shugaban ƙasa na PDP a 2019, inda bayan Tambuwal ya faɗuwa, ya bayyana goyon bayansa ga Atiku, domin fafatawa da shugaban kasa mai ci a lokacin, Marigayi Muhammadu Buhari.

A 2022 kuma Tambuwal ya janye neman takararsa a zauren zaɓen dan takarar shugaban ƙasa na PDP, ya kuma buƙaci deleget su zaɓi Atiku a madadinsa.

Wannan ne ake ganin ya ba wa Atiku damar kayar da Nyesom Suke da sauran masu neman tikitin takarar PDP.

A baya-bayan kuma Tambuwal ya raka Atiku wajen wasu manyan tattaunawa da shugabannin adawa kamar tsohon Shugaban Ƙasa Marigayi Muhammadu Buhari, gabanin ƙulla haɗakar ’yan adawa domin shiga ADC da nufin tunkarar APC a zaɓen 2027.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: adwa Siyasa Tambuwal zargi domin amsa tambayoyi Naira biliyan 189 tsohon Gwamnan Shugaban Ƙasa Gwamnan Jihar bayyana cewa Tambuwal ya

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu ya yi alhinin rasuwar tsohon shugaban PDP, Audu Ogbeh

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga jama’a da Gwamnatin Jihar Binuwai bisa rasuwar Cif Audu Ogbe tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Cif Audu Ogbeh.

Ya kuma yi wa iyalansa, abokansa da dukkanin ’yan uwansa ta’aziyya kan rashin da suka yi.

Kotu ta ɗaure wata mata shekara 3 a kan damfara  Tsohon Ministan Noma Audu Ogbeh ya rasu

Cif Ogbeh, ya rasu yana da shekaru 78 a duniya, ya hidimta wa Najeriya a ɓangarori daban-daban ciki har da Ministan Sadarwa a lokacin Jamhuriya ta Biyu.

Sannan daga baya ya zama Ministan Noma a Gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari.

A cewar sanarwar Bayo Onanuga, mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labaru, Ogbeh mutum ne mai basira da zurfin tunani wanda ya taimaka wajen tsara manufofin gwamnati da magance manyan matsalolin ƙasa.

Ogbeh, ya fara harkar siyasa a shekarun 1970 a matsayin ɗan majalisa, sannan daga baya ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar APC.

Shugaba Tinubu, ya bayyana shi a matsayin “Ɗan ƙasa wanda hikimarsa, jajircewarsa, da ƙoƙarinsa na ci gaba suka bar tarihi a siyasar Najeriya.

“Kullum yana da hujjoji da alkaluma don kare ra’ayinsa. Ƙasa za ta yi matuƙar kewar gogewarsa.”

Shugaban ya yi addu’ar Allah Ya jiƙansa ya kuma bai wa iyalansa haƙuri da juriya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Babban Dalilin EFCC Na Yi Wa Tsohon Gwamnan Sokoto, Tambuwal, Tambayoyi
  • Za a gyara tarbiyar tubabbun ’yan daban Kano
  • Majalisar Dokokin Kano Ta Karɓi Ƙarin Kasafin Kuɗi Na 2025
  • EFCC ta kama ’yan damfara a ɗakin karatun Obasanjo 
  • ’Yan bindiga sun kashe gomman mutane a ƙauyukan Sakkwato
  • An ɗaure tsohon Firaminista Succes Masra shekaru 20 a Chadi
  • Tinubu ya yi alhinin rasuwar tsohon shugaban PDP, Audu Ogbeh
  • Gwamnan Kano Ya Sallami Mataimaka Biyu Kan Zargin Karkatar Da Kayan Tallafi
  • Tsohon Shugaban PDP Audu Ogbeh Ya Rasu