Kasar Iraki Ta Ce: Yarjejeniyar Da Ta Kulla Da Iran Zai Amfani Dukkan Kasashen Yankin
Published: 13th, August 2025 GMT
Gwamnatin Iraki ta bayyana cewa: Yarjejeniyar da Iran ta kulla da Iraki zata yi gagarumar amfani a fagen tsaron yankin
Ofishin jakadancin Iraki a Amurka ya tabbatar da cewa: Iraki kasa ce mai cin gashin kanta kuma tana da hakkin kulla yarjejeniyoyin da kuma yarjejeniyar fahimtar juna. An yi nuni da cewa, yarjejeniyar tsaro da aka rattabawa hannu a baya-bayan nan tsakanin Iran da Iraki ta zo ne a cikin tsarin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu don tabbatar da tsaro da kuma kula da kan iyakokin kasashen biyu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa: Ofishin jakadancin ya bayyana a cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labaran kasar Iraki INA ya watsa cewa: “A matsayin martani ga kalaman da kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta yi a yayin taronta na ‘yan jarida na baya-bayan nan, Iraki kasa ce mai cikakken ‘yancin kai, kuma tana da hakkin kulla yarjejeniyoyin da kuma bayanan fahimtar juna bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulkinta da dokokin kasa, kuma ta hanyar da ta dace da manyan muradunta.”
Ta kara da cewa, “Iraki na jin dadin huldar sada zumunci da hadin gwiwa da kasashe da dama a duniya, ciki har da kasashe makwabta, Amurka, da sauran kasashe abokantaka, kuma tana da sha’awar gina wannan dangantakar bisa tushen mutunta juna da moriyar juna.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sojojin Yemen Sun Kai Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’Ila Har Sau Shida August 13, 2025 Wakilan Hamas sun isa Alkahira don shawarwarin tsagaita wuta a Gaza August 13, 2025 Iran: Amurka Da Isra’ila Ne Da Kansu Suka Bukaci Dakatar Da Bude Wuta August 13, 2025 Habasha: Madatsar ruwanmu amfanin dukkanin kasashen yankin ne August 13, 2025 Bankin Duniya Zai Kashe $300m Don Inganta Rayuwar ’Yan Gudun Hijira A Arewacin Nijeriya August 13, 2025 Nijeriya Da Isra’ila Na Kara Karfafa Alaka A Tsakaninsu August 13, 2025 Kasashe 27 Sun Bukaci Isara’ila Ta Kawo Karshen Hana Shigar Da Abinci A Gaza August 12, 2025 Iran: Duk Wani Sabon Hari, Zai Fuskanci Mummunan Martanin Soji August 12, 2025 Larijani: Iraki Ba Ta Karbar Umarni Daga Iran August 12, 2025 Iran: Ma’aikatar Harkokin Waje Ce Ke Kula Da Lamarin Makamashin Nukliyar Kasar August 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yawaba Pakistan Saboda Goyon Bayanta
Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr Ali Larijan wanda ya ke ziyarar aiki na kwanaki uku a kasar Pakistan ya yabawa kasar saboda goyon bayan da ta bawa kasarsa a lokacin yakin kwanaki 12 wanda Amurka da HKI suka dorawa kasar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Dr Ali Larijana yana fadar haka a shafinsa na X a jiya Talata. Sannan yace ya isar da sakon gaisuwa na Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khami’ae ga mutanen kasar Pakistan. Banda haka ya gana da Firai ministan kasar Shehbaz Sharif da shugaban kasa Asif Ali Zardari da kuma kakakin majalisar dokokin kasar kasar Sardar Avaz Saadik.
A ganawar Larijani da Sharif sun tattauna kan dangantaka mai tsawo da ke tsakanin Iran da Pakisatan, da kuma bukatar a kara zurfafata.
Sharif a nasa bangaren ya bayyana cewa nan ba da dadewa waministan harkokin wajen kasar Mohammad Ishak Dar zai ziyarci Tehran inda ake saran zai rattaba hannu kan yarjeniyoyi na bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu, daga ciki har da batun kammala aikin shimfida bututun gas daga kasar Iran zuwa Pakistan. Da kuma harkokin sadarwa.
A cikin wannan shekarar ne dai kasashen biyu suka rattaba hannu kan yarjeniyar bunkasa kasuwanci ta dalar Amurka billion 10 a tsakaninsu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka EU da AU na taro kan diyya ga laifukan mulkin mallaka da cinikin bayi November 25, 2025 Hizbullah: Isra’ila na kure idan ta na tunanin kashe-kashe zai kawo karshen kungiyarmu November 25, 2025 Tashar Press TV ta kaddamar da sashen harshen Hebrew November 25, 2025 Bincike : Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa Akalla 100,000 a Gaza November 25, 2025 Kasar Gambia Ta Bai Wa Jagoran ‘Yan Hamayyar Siyasar Kasar Kamaru Mafaka Ta Wucin Gadi November 25, 2025 China Ta Yi Tir Da Yadda Kasar Japan Ta Girke Makamai Masu Linzami A Kusa Da Yankin Taiwan November 25, 2025 Velayati: Alakar Iran da Iraki tana da karfi November 25, 2025 Arakci Ya Yi Gargadi Akan Abin Zai Biyo Bayan Keta Dokokin Duniya Da “Isra’ila” Take Yi A Cikin Wannan Yankin November 25, 2025 An Gudanar Da Jana’izar Shahidai 300 A Dai-Dai Ranar Shahadar Zahra (s) A Jiya Litinin November 25, 2025 Amurka Da HKI Sun Kawo Karshen Hukumar GHF Mai Raba Abinci A Gaza November 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci