Iran ta yi Allah wadai da kisan kiyashin da Isra’ila ta yi wa ‘yan jarida a Gaza
Published: 12th, August 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya yi Allah wadai da kisan da aka yi wa ‘yan jarida biyar a wani harin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kai a zirin Gaza, yana mai bayyana wannan laifi a matsayin shaida ta yanke kauna daga gwamnatin da duniya ta juya mata baya saboda munanan laifukanta.
A wani sakon da ya wallafa a shafin sada zumunta a yammacin wannan Litinin, Araghchi ya bayyana cewa kisan gillar da aka yi wa wasu manyan ‘yan jarida na Falasdinu ba alama ce ta karfin gwamnatin sahyuniya ba, hakan alama ce ta gazawa da yanke kauna.
Ya kuma kara jaddada cewa hadin kan da wasu gwamnatocin kasashen Yamma suke baiwa Isra’ila yana mai ishara da kasashe irin su Amurka, da cewa hakan shi ne ke kara karfafa gwiwar Haramtacciyar Kasar Isra’ila wajen ci gaba da tafka laifuka yakin kisan kare dangi a kan al’ummar Falastinu.
Su ma a nasu bangaren Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun yi Allah wadai da matakin da gwamnatin yahudawan ta dauka na kaddamar da yaki a kan ‘yan jarida, tare da yin tir da kasashen da suke ikirarin kare hakkokin bil adama da fadar albarkacn baki.
Rundunar IRGC ta bukaci kasashen duniya da kungiyoyin kare hakkin bil adama da su tofa albarkacin bakinsu tare da daukar matakin dakatar da laifukan yaki na gwamnatin sahyuniya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gaza: Yunwa ta kashe Falastinawa 5 a cikin kasa da Sa’o’i 24 da suka gabata August 12, 2025 Ministan tsaron Italiya ya caccaki gwamnatin Netanyahu kan batun Gaza August 12, 2025 Araghchi: Mataimakin Shugaban IAEA Zai Ziyarci Tehan َA Wannan Talata August 11, 2025 Iran: Lebanon Tana Da ‘Yancin Kare Kanta Da Makamanta August 11, 2025 Mali: An Kama Sojoji Fiye da 40 Bisa Zargin Yunkurin Juyin Mulki August 11, 2025 Iraki: Larijani Da Sudani Sun Gana A Bagdaza August 11, 2025 Mafi yawan Kasashen Duniya Sun Amince Da Samarda Kasar Falasdinu August 11, 2025 Mahukuntan Iraki: Adadin Masu Ziyarar Arba’een Daga Kasashen Ketare Zai Iya Haura Miliyan 40 August 11, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Sun kai Wasu Munanan Hare-Hare Kan Yankunan Zirin Gaza August 11, 2025 Kwamitin Tsaron MDD Ya Gudanar Da Zaman Taro Kan Aniyar Isra’ila A Kan Gaza August 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Faransa Da Jamus Da Kuma Birtaniya Sun Bayyana Aniyarsu Ta Ganin An Farfado Da Tattauna Da Iran
Shugabannin Faransa, Jamus, da Biritaniya: Sun kuduri aniyar farfado da tattaunawa da Iran
Kasashen Faransa da Jamus da Birtaniya sun bayyana aniyarsu ta farfado da shawarwari da Iran da Amurka dangane da shirin makamashin nukiliyar Iran da nufin cimma cikakkiyar yarjejeniya mai dorewa.
A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa, kasashen uku sun yi la’akari da Shirin kunna yarjejeniyar fahimtar juna. A baya dai Faransa da Birtaniya da Jamus sun sanar da cewa za su ci gaba da neman hanyar diflomasiyya don warware rikicin, amma Iran ta tabbatar da cewa ba ta son ci gaba da tattaunawa a halin yanzu idan dai har za a kakaba mata takunkumi.
A gefe guda kuma shugabannin kasashen Birtaniya da Faransa da Jamus sun yi maraba da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a zirin Gaza tare da yin alkawarin dawo da taimakon jin kai da zarar an amince da yarjejeniyar.
A cikin sanarwar da suka fitar, shugabannin sun jaddada cewa, sun amince da cewa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya ba da cikakken goyon baya ga shirin na Gaza, da saukaka aiwatar da shi, tare da sa ido kan matakai na gaba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kungiyoyin Falasdinawa Sun Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Kan Tsagaita Bude Wuta A Gaza October 11, 2025 Venezuala Ta Bukaci Kwamitin Sulhun M.D.D Da Ya Tabbatar Da Cewa: Amurka Tana Barazana Ga Zaman Lafiya October 11, 2025 Pakistan Ta Kai Hari Kan Kasar Afganistan, Inda Ake Rade-Radin Kashe Shugaban Taliban Na Kasarta October 11, 2025 Putin: Natanyahu Yana Son Warware Matsaloli Da Iran Cikin Lumana Ba Tare Da Yaki Ba October 10, 2025 Majalisar Turai Ta Bukaci Kasashen Nahiyar Su Kakkabo Jiragen Yakin Rasha October 10, 2025 Sa’o’ii Da Fara Janyewar Sojojin HKI A Gaza An Fara Gano Gawakin Falasdinwa October 10, 2025 Falasdinawa Daga Kudancin Gaza Sun Fara Komawa Gidajensu Da Aka Rusa A Arewacin Yankin October 10, 2025 Rahotanni : Isra’ila ta fara janye dawa wasu yankuna na Gaza October 10, 2025 Amurka ta kakaba wa wasu kamfanoni 50 takunkumi saboda sayen man Iran October 10, 2025 Isra’ila ta ce yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta fara aiki October 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci