Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja, ya yaba wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan kama Abubakar Abba, jagoran kungiyar Mahmuda, daya daga cikin manyan kungiyoyin ta’addanci da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi a Najeriya.

 

An ce an kama shi ne a Wawa da ke karamar hukumar Borgu ta Jihar Neja inda aka kai shi Abuja domin ci gaba da bincike.

 

Gwamna Umar Bago ya bayyana matakin a matsayin nuni da irin jajircewar da shugaba Bola Ahmed Tinubu ke yi na tabbatar da tsaro da walwalar ‘yan Nijeriya.

 

Gwamnan wanda ya yi magana ta bakin babban sakataren yada labaran sa, Bologi Ibrahim, ya ce, “Eh gaskiya ne, zan iya tabbatar da cewa hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta kama shugaban kungiyar Mahmuda da ke daya daga cikin kungiyoyin ta’addanci a yammacin Afirka, Abubakar Abba, wanda jami’an tsaron farin kaya DSS suka kama shi da ransa.

 

“Wannan babbar nasara ce a gare mu a matsayinmu na jama’a da kuma gwamnati, kuma Shugaba Tinubu ya cancanci a yaba masa kan wannan labari mai ban sha’awa, yana mai jaddada cewa “Kamun Abba ya nuna cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jajirce wajen kawo karshen rashin tsaro da kuma inganta rayuwar ‘yan Nijeriya. In ji Gwamna Bago.

 

Gwamnan ya yi alkawarin cewa gwamnatin jihar Neja za ta ci gaba da hada kai da gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro domin ganin an dakile ta’addanci a jihar Neja da Najeriya.

 

ALIYU LAWAL.

 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

NDLEA Ta Kama Fasto Bisa Laifin Safarar Miyagun Kwayoyi A Legas 

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta kama wanda ya kafa kuma yake kula da cocin ‘The Turn of Mercy’, Adefolusho Olasele, wanda aka fi sani da Abbas Ajakaiye, bisa zarginsa da hannu wajen safarar miyagun kwayoyi da dama daga Ghana zuwa Nijeriya. Fasto Olasele, wanda ya shafe watanni ba a san inda yake ba, an kama shi ne a ranar Lahadi, 3 ga watan Agusta, 2025, a cocinsa da ke Okun Ajah, yankin Lekki, a Legas. NDLEA Ta Cafke Masu Baburan Da Ke Kai Saƙon Muggan Ƙwayoyi A Abuja Dole Ne Afrika Ta Mayar Da Hankali Wajen Amfana Da Damarmakin Da Ke Tekunanta – Ɗantsoho Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi, ya fitar a ranar Lahadi, ta ce, jami’an hukumar sun jira har zuwa lokacin da ya gama wa’azi na ranar Lahadi kafin su kama shi a lokacin da ya fito daga harabar cocin. A cewarsa, faston ya gudu zuwa Ghana a cikin watan Yuni don gujewa kama shi bayan da jami’an tsaro suka alakanta shi da laifin safarar miyagun kwayoyi  kulli biyu kimanin kilo 200 da aka gano a bakin tekun Okun Ajah a ranar 4 ga watan Yuni da kuma kilo 700 da aka samu a cikin motarsa ta kai sako a ranar 6 ga watan Yuli.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Namadi Ya Yaba Wa Kungiyar NBA Bisa Inganta Manufofi Da Ka’idojin Aikin Lauya
  • Gwamnatin Neja Ta Tabbatar Da Kama Hatsabibin Ɗan Bindiga, Abubakar Abba
  • Lafiyar Tinubu kalau – Soludo
  • ‘Yan Sanda Sun Kama Wasu Da Ake Zargin ‘Yan Kungiyar Asiri Ne A Jihar Kwara
  • Tinubu Ya Sake Nada Dankaka A Matsayin Shugaban Hukumar Kula Da Da’ar Ma’aikata Ta Kasa
  • Gwamna Bago Ya Kaddamar da Katafaren Kamfanin sarrafa Man Kade A Afirka.
  • An Yi Allah Wadai Da Hana Amfani Da Hijabi A Jami’ar LandMark, Omu-Aran Kwara
  • Runduunar ‘Yan Sandan Jihar kwara Ta Karfafa Tsaro A Banbila
  • NDLEA Ta Kama Fasto Bisa Laifin Safarar Miyagun Kwayoyi A Legas