EFCC Ta Bayar Da Belin Tambuwal, Ta Yi Allah-wadai Da Zargin Da Jam’iyar ADC Ta Yi
Published: 13th, August 2025 GMT
A halin da ake ciki, EFCC ta yi Allah wadai da jam’iyyar ADC bisa zargin sanya siyasa a binciken da ta gudanar kan Tambuwal.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp.এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu na amfani da EFCC ya muzguna wa ’yan adawa — Atiku
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da amfani da Hukumar EFCC wajen yi wa masu adawa da ita barazana.
Saƙon da ɗan takarar shugaban ƙasa a Zaɓen 2023 ya wallafa wannan Talatar a shafinsa na X, na zuwa ne bayan tsare tsohon Gwamnan Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal da EFCCn ta yi.
Amurka da China sun dakatar da harajin da suka ƙaƙaba wa juna Harin ’yan fashi: An rufe Federal Poly Bauchi BauchiA cewar Wazirin Adamawa, “dalilin da EFCC ta tsare tsohon Gwamnan Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, shi ne saboda yana cikin jam’iyyar adawa ta haɗaka.
“Wannan yana ƙara nuna yadda gwamnatin Tinubu ke ci gaba da yaɗa manufofinta na musgunawa, tsoratarwa, da rusa ‘yan adawa.”
Ya ƙara da cewa, “A yau dai duk wanda yake da alaƙa da ‘yan adawa to za a zarge shi da cin hanci da rashawa.
“Kuma da zarar an tilasta musu komawa kan tsarin tafiyar siyasar Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu, sai ya zama kamar an gafarta musu zunubansu ne.”
Martanin PDPIta ma jam’iyyar PDP reshen Jihar Sakkwato ta soki tsarewar da aka yi wa tsohon gwamnan, tana bayyana lamarin a matsayin “tuggun siyasa.”
Mai magana da yawun jam’iyyar a jihar, Hassan Sahabi Sanyinnawal, ya bayyana shi a matsayin yunƙurin rufe bakin jam’iyyun adawa da tsoratar da su.
Rahotanni sun ce EFCC da ke da alhakin yaƙi ta masu yi wa tattalin arziki ta’annati ta tsare Tambuwal a Abuja ranar Litinin kan zargin cire naira biliyan 189 ba bisa ƙa’ida ba, abin da ya saɓa wa dokar haramta sama-da-faɗi da kuɗi ta 2022.
Sai dai wasu majiyoyi daga hukumar sun ce gayyata ce kawai aka yi masa domin ya yi ƙarin haske kan batun, ba kama shi ba.
Tambuwal wanda ya taɓa zama shugaban Majalisar Wakilan Nijeriya, ya fara siyasarsa a jam’iyyar APC kafin ya koma PDP, sannan daga bisani ya shiga jam’iyyar haɗaka ta ADC, wacce ta ɗaura ɗamarar karɓe mulki daga hannun APC a 2027.
A bayan nan wasu rahotanni sun bayyana cewa EFCC ta gayyaci tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai kuma tsohon gwamnan Jihar Imo, Emeka Ihedioha, wanda ake sa ran zai amsa cikin mako ɗaya.