Masar ta yi gargadin cewa a shirye take ta dauki duk wani mataki na kare muradunta
Published: 12th, August 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Masar Badr Abdelatty ya yi gargadin cewa a shirye take ta dauki duk wani mataki na kare muradunta na iyakokin teku.
Da yake magana a wani taron manema labarai na hadin gwiwa a birnin Alkahira tare da ministan harkokin wajen kasar Ivory Coast, Léon Kacou Adom, wanda aka gudanar a wani bangare na shawarwarin siyasa karo na uku tsakanin Masar da Cote d’Ivoire, Abdelatty ya ce tattaunawar ta yi tsokaci kan kalubalen ci gaban kasashen Sahel da yammacin Afirka.
Ya kuma kara da cewa, an tattauna hadin gwiwa kan yaki da ta’addanci, inda ya yaba wa Cote d’Ivoire bisa kokarin da take yi a wannan fanni.
Abdelatty ya jaddada cewa, “Masar na mai da hankali matuka kan samar da tsaro da kwanciyar hankali a yankin Sahel da Afirka ta Yamma,” yana mai bayyana tasirin rashin zaman lafiya a wadannan yankuna a kan kasashe makwabta da kuma tsaron kasa na Masar.
A cewar wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Masar ta fitar, ministocin biyu sun kuma yi nazari kan sabbin abubuwan da suka faru a yankin Gabas ta Tsakiya, da yankin kahon Afirka, da kuma tekun Red Sea, tare da lalubo hanyoyin inganta zaman lafiya da tsaro da kwanciyar hankali a nahiyar Afirka.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, bangarorin biyu sun amince su ci gaba da yin hadin gwiwa da tuntubar juna a matakai na kasashen biyu, da yin musayar ra’ayi a mataki na yankin da kuma na kasa da kasa.
A nasa bangaren, ministan harkokin wajen kasar Ivory Coast ya yaba da muhimmiyar rawar da Masar ke takawa wajen tallafawa da gina karfin kasashen yammacin Afirka da yankin Sahel, da kuma kokarin da take yi na samar da tsagaita bude wuta a zirin Gaza da saukaka isar da kayayyakin jin kai da agaji ga al’ummar Palasdinu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran ta yi Allah wadai da kisan kiyashin da Isra’ila ta yi wa ‘yan jarida a Gaza August 12, 2025 Gaza: Yunwa ta kashe Falastinawa 5 a cikin kasa da Sa’o’i 24 da suka gabata August 12, 2025 Ministan tsaron Italiya ya caccaki gwamnatin Netanyahu kan batun Gaza August 12, 2025 Araghchi: Mataimakin Shugaban IAEA Zai Ziyarci Tehan َA Wannan Talata August 11, 2025 Iran: Lebanon Tana Da ‘Yancin Kare Kanta Da Makamanta August 11, 2025 Mali: An Kama Sojoji Fiye da 40 Bisa Zargin Yunkurin Juyin Mulki August 11, 2025 Iraki: Larijani Da Sudani Sun Gana A Bagdaza August 11, 2025 Mafi yawan Kasashen Duniya Sun Amince Da Samarda Kasar Falasdinu August 11, 2025 Mahukuntan Iraki: Adadin Masu Ziyarar Arba’een Daga Kasashen Ketare Zai Iya Haura Miliyan 40 August 11, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Sun kai Wasu Munanan Hare-Hare Kan Yankunan Zirin Gaza August 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: harkokin wajen
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Amurka Ya Yi Barazanar Aikewa Ukraine Makamai Masu Linzami Kirar Tomahawk
Shugaban kasar Amurka ya yi barazana ga shugaban kasar Rasha na aike wa Ukraine makamai masu linzami kirar Tomahawk
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce: Zai gargadi takwaransa na Rasha Vladimir Putin cewa: Akwai yiwuwar Ukraine za ta iya samun makamai masu linzami kirar “Tomahawk” idan Rasha ba ta kawo karshen yakin Ukraine ba.
Da aka tambaye shi a cikin jirgin Air Force One da ke kan hanyarsa ta zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila da Masar da yammacin ranar Lahadi ko shi da kansa zai tattauna da Putin kan batun, Trump ya ce, “Yana iya magana da shi. Yana cewa: Idan ba a warware wannan yakin ba, zai aika wa Ukraine da makamai masu linzami na Tomahawk.”
Trump ya kara da cewa shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya bukaci makamai masu linzami na Tomahawk lokacin da suka tattauna sabbin makamai ga kasar ke bukata ta wayar tarho a ranar Asabar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Trump, da Al’Sisi za su jagoranci taron zaman lafiya kan Gaza October 12, 2025 ‘Yan Kamaru na kada kuri’a a zaben shugaban kasar October 12, 2025 Wata Kotu a Faransa ta yi watsi da rufe wata makarantar musulmi a birnin Nice October 12, 2025 Gwamnatin Cuba ta yi watsi da zargin da Amurka ke yi na hannu a yakin Ukraine October 12, 2025 Arachi: HKI Ba Abar Amincewa Ba Ce, Falasdinawa Su Yi Hattara October 12, 2025 Iran Ta Yi Allawadai Da HKI Kan Hare-Haren Da Take Kaiwa Kudancin Lebanon October 12, 2025 An Gudanar Da Taron ‘Farkawar Musulmi’ A Nan Tahren Inda Aka Tattauna Batun Falasdinu October 12, 2025 Amurka Da Masar Ne Zasu Jagoranci Taron Rattaba Hannu Tsakanin HKI Da Falasdin A Sharm Sheikh October 12, 2025 China Ta Sha Alwashin Maida Martani Kan Harajin Trump A Kanta Na 100% October 12, 2025 An Yi Girgizar Kasa Mai Daraja 5 A Ma’aunin Richter A Kasar Habasha October 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci