Gaza: Yunwa ta kashe Falastinawa 5 a cikin kasa da Sa’o’i 24 da suka gabata
Published: 12th, August 2025 GMT
Ma’aikatar lafiya a Gaza ta sanar da isar shahidai 69 da wadanda suka jikkata su 362 zuwa asibitoci a cikin kasa da sa’o’i 24 da suka gabata.
Daga cikin shahidan akwai wadanda yunwa ce ta kashe su, da kuam wadanda suka yi shahada a wajen neman samun agajin abinci, ida Isra’ila take kai hari kansu abbu kakkautawa.
A cikin rahotonta na kididdiga na yau da kullun, ma’aikatar ta gano mutuwar mutane biyar da suka hada da yaro daya sakamakon yunwa a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, wanda adadin wadanda suka yi shahada sakamakon yunwa ya kai 222, ciki har da yara 101.
Ma’aikatar ta tabbatar da cewa adadin wadanda suka mutu a harin ta’addancin Isra’ila ya karu zuwa shahidai 61,499 da kuma jikkatar 153,575 tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023.
Haramtacciyar Kasar Isra’ila na ci gaba da yakin kisan kiyashi da kuma azabtarwa da yunwa a Gaza. Asibitin Al-Awda ya sanar da mutuwar wasu mutane da suka hada da yaro daya da kuma jikkata wasu 26, sakamakon harin Isra’ila a kan ma’aikatan agaji a kudancin Wadi Gaza, da kuma hare-haren da aka kai kan wasu yankuna a tsakiyar zirin Gaza cikin sa’o’i 24 da suka gabata.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ministan tsaron Italiya ya caccaki gwamnatin Netanyahu kan batun Gaza August 12, 2025 Araghchi: Mataimakin Shugaban IAEA Zai Ziyarci Tehan َA Wannan Talata August 11, 2025 Iran: Lebanon Tana Da ‘Yancin Kare Kanta Da Makamanta August 11, 2025 Mali: An Kama Sojoji Fiye da 40 Bisa Zargin Yunkurin Juyin Mulki August 11, 2025 Iraki: Larijani Da Sudani Sun Gana A Bagdaza August 11, 2025 Mafi yawan Kasashen Duniya Sun Amince Da Samarda Kasar Falasdinu August 11, 2025 Mahukuntan Iraki: Adadin Masu Ziyarar Arba’een Daga Kasashen Ketare Zai Iya Haura Miliyan 40 August 11, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Sun kai Wasu Munanan Hare-Hare Kan Yankunan Zirin Gaza August 11, 2025 Kwamitin Tsaron MDD Ya Gudanar Da Zaman Taro Kan Aniyar Isra’ila A Kan Gaza August 11, 2025 Shugaban Iran: Dole ne duniya ta kawo karshen laifukan yakin Isra’ila a Gaza August 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: wadanda suka
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar (ASUU) Ta Sanar Da Shiga Yajin Aikin Gargadi A Kasa Baki Daya .
Shugaban ƙungiyar, Farfesa Chris Piwuna, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a cibiyar ASUU ta ƙasa da ke Jami’ar Abuja, inda ya zargi gwamnatin tarayya da rashin gaskiya wajen tattaunawa kan buƙatun ƙungiyar. Don haka sun fara yajin aiki daga yau na gargadi na tsawon mako biyu.
Ana ta bangaren Gwamnatin tarayya ta gargadi ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa (ASUU) da ta guji shiga yajin aiki, tana mai jaddada cewa dokar “babu aiki, babu albashi” tana nan daram. Ministan Ilimi, Dr. Maruf Tunji Alausa, tare da ƙaramin Ministan Ilimi, Farfesa Suwaiba Sai’d Ahmed, sun bayyana haka a cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Boriowo Folasade, ya fitar a ranar Lahadi.
Ministocin sun tabbatar da cewa gwamnati na ci gaba da tattaunawa mai ma’ana da ASUU domin warware duk wasu matsaloli da ke addabar tsarin jami’o’i a Nijeriya.
Sun bayyana cewa gwamnati ta nuna gaskiya da hakuri a tattaunawarta da kungiyar, inda ta riga ta amince da mafi yawan bukatun ASUU, ciki har da karin wani kaso na alawus kin koyarwa da inganta yanayin aiki na malamai.
.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Aragchi: HKI Ba Zata Mutunta Tsaida Wuta A Gaza Ba October 13, 2025 Iran Ta Ki Zuwa Masar Saboda Bata Son Haduwa Da Azzaluman Da Suka Kashe Falasdinwa A Gaza October 13, 2025 Shugaban Kasar Amurka Donal Trump Ya Isa HKI Kafin Taron Sharm Sheikh October 13, 2025 An Fara Musayar Fursinoni Tsakanun Hamas Da HKI A Safiyar Yau Litini October 13, 2025 Falasdinawa Sun Gano Gawakin Wadanda HKI Ta Kashe A gaza Fiye Da 320 Cikin Kwanaki Biyu Kacal October 13, 2025 Iran Ba Zata Halarci Zaman Taron Sharm El-Sheikh Ba Saboda Wasu Dalilai Da Ta Bayyana October 13, 2025 Iran Ta Gayyaci Mukaddashin Jakadan Kasar Oman Zuwa Ma’aikatar Harkokin Wajenta October 13, 2025 Yemen Ta Gargadi Isra’ila Kan Fuskantar Hare-Hare Idan Ta Karya Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta October 13, 2025 Cibiyar Lafiya Ta Nasser Ta Ce: Yaran Gaza 5,500 Suna Bukatar Agajin Gaggawa A Kasashen Waje October 13, 2025 Shugaban Amurka Ya Yi Barazanar Aikewa Ukraine Makamai Masu Linzami Kirar Tomahawk October 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci