An Yi Kira Ma’aikatan Watsa Labarai Su Tabbatar da Gaskiya A Ayukkan Su
Published: 13th, August 2025 GMT
An yi kira ga kwararrun kafafen yada labarai da su tabbatar da madogararsu domin tabbatar da samar da kyakykyawan rahoton abubuwan da ke faruwa a cikin al’umma.
Babban Limamin Masallacin Al-Waheed Central, Imam Mustapha Luqman ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake jawabi a wajen taron hadin gwiwa da kungiyar ‘yan jarida ta NUJ ta shirya domin fara taron makon manema labarai na shekara ta 2025, da kuma bikin cika shekara 45 daka guda a Ilorin jihar Kwara
Ya shawarce su da su bi ka’ida wajen gudanar da ayyukansu na yada labarai.
Imam Lukman ya bukaci masu aikin yada labarai da su kasance masu adalci da kyautatawa a tsakaninsu .
A nasa jawabin, Fasto Adedoyin Adeyemi ya shawarci masu sana’ar yada labarai da su kasance masu halin kirki a lokacin da suke aikin su.
Ya bukace su da su tuna cewa ba za su iya kasancewa kan aikin ba har abada. ya kara da cewa ya kamata mambobin cocin su yi tasiri a rayuwar mutane.
Fasto Adeyemi ya shawarce su da su so juna da kyautatawa a kowane lokaci.
Ya shawarci ‘yan Najeriya da su kasance da ruhin yafiya da kuma yi wa shugabanni addu’a Allah ya sa su jagoranci al’umma daidai.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kwara yada labarai
এছাড়াও পড়ুন:
Yajin Aikin NLC Da TUC Ya Gurgunta Ayyukan Gwamnati A Taraba.
Yajin aikin sai baba-ta-gani da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC reshen jihar Taraba, da kungiyar Kwadago (TUC) reshen jihar Taraba suka kaddamar a ranar Litinin da ta gabata, ya gurgunta ayyukan gwamnati a ma’aikatu da hukumomin gwamnati a jihar.
Matakin wanda ya fara da tsakar daren litinin, ya kasance tare da hadin gwiwar shugabannin kungiyoyin biyu bayan taron majalisar zartaswar jihar da aka gudanar a ranar Lahadi a sakatariyar kungiyar NLC ta jihar.
Taron ya yi nazari ne kan wa’adin da aka bayar tun da farko kan wasu kura-kuran da ake zargin an tafka a cikin ayyukan kwamitin tantance bayanan da gwamnatin jihar ta kafa.
A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da sakataren kungiyar NLC na jihar, Adamu.W.Buba, da sakatariyar TUC ta jihar, Polina Gani suka sanya wa hannu, kungiyoyin sun umurci dukkanin rassan kungiyar da su tashi tsaye tare da kafa kwamitin aiwatar da yajin aikin domin tabbatar da an bi cikakken aikin.
“Dukkan ma’aikatan suna nan ta hanyar umarnin su kaurace wa wuraren aikinsu kuma su janye ayyukansu har sai wani lokaci. Za a ci gaba da yajin aikin har sai gwamnati ta biya musu bukatunsu,” in ji sanarwar “.
Kungiyoyin kwadago a makon da ya gabata sun zargi kwamitin da aikata ayyukan da suka yi wa ma’aikata illa tare da zargin gwamnati da yin watsi da wa’adin.
Shugabannin kungiyar sun bayyana cewa ba za a dakatar da yajin aikin ba har sai an gyara kura-kuran da ake zarginsu da aikatawa, inda suka bukaci masu ruwa da tsaki da su shiga Tsakani su da gwamnatin jihar.
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, hukumomi daga gwamnati ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
COV/JAMILA ABBA