Gwamna Namadi Ya Yaba Wa Kungiyar NBA Bisa Inganta Manufofi Da Ka’idojin Aikin Lauya
Published: 13th, August 2025 GMT
Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da bikin makon shari’a na shekarar 2025 wanda ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) reshen jihar Jigawa ya shirya, inda ya yi kira da a ƙara ƙarfafa bin ƙa’idojin aikin shari’a da hanzarta gudanar da shari’a a duk fadin jihar.
A jawabinsa wajen bikin bude taron a Dutse, Gwamna Namadi ya yaba wa shugabannin NBA bisa hadin kai da kwarewarsu wajen gudanar da aiki.
“Na shafe watanni da dama ina bin diddigi da sha’awar yadda kuka kafa, tare da gudanar da ayyukan kungiyar reshen jihar, cikin haɗin kai da ƙarfafawa, inda ya zama wata gagarumar kafa wacce ke kare muradun aikin lauya da mambobin ƙungiyar a Jigawa ma da wajen ta.” In ji shi.
“Na yaba ƙoƙarinku na ganin yadda NBA reshen jihar ta samu nasara wajen inganta manufofi da ƙa’idojin da aka san ƙungiyar da su—wato kare doka, tabbatar da samun adalci ga kowa, ciki har da talakawa, da kuma tabbatar da gudanar da shari’a cikin sauƙi a jihar Jigawa.
“Baya ga hulɗar aiki da zamantakewa, abin farin ciki ne ganin yadda irin waɗannan taruka ke taimaka wa wajen inganta bin ƙa’idojin aikin lauya da kuma ƙarfafa tattaunawa, ba kawai tsakanin lauyoyi ba, har ma da sauran muhimman masu ruwa da tsaki a harkar shari’a.”
Yayin bayyana gyare-gyaren gwamnatinsa a bangaren shari’a, Gwamna Namadi ya ambaci shirye-shiryen da suka haɗa da kafa Cibiyoyin Doka na Al’umma, gabatar da Zauren Sulhu, shirye-shiryen faɗaɗa Sashen Kare Haƙƙin Ɗan Kasa a kowace kotu, da sauran muhimman tsare-tsare.
Ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su yi aikinsu bisa gaskiya da rikon amana.
Ya bayyana fatan cewa tattaunawar za ta bayar da gagarumar gudummawa wajen kare ƙa’idojin aikin lauya da kuma inganta gudanar da shari’a a jihar Jigawa.
Usman Mohammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna
Gwamna Uba Sani ya jaddada cewa wannan titin ba na yankin Arewa kadai ba ne, ya bayyana shi a matsayin jijiyar ƙasa da ƙasa ne wadda ke haɗa yankuna daban-daban tare da ƙarfafa haɗin kai da bunƙasar tattalin arziki.
Ya kara da cewa titin Abuja- Kaduna da Kano na ɗaya daga cikin manyan ayyukan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ƙarƙashin Manufar Sabon Fata na (Renewed Hope Agenda), wadda ke nufin sabunta manyan gine-ginen ƙasa da inganta tattalin arziki.
Yace “Wannan titi ba hanya ce kawai ba inda yace wata hanya ce ta tattalin arziki wadda ke haɗa mutane, kasuwanni, da dama a fadin Arewacin Nijeriya da ma bayan haka,”
A nasa jawabin, Sanata Umahi ya yaba wa Gwamna Uba Sani bisa yadda yake kaiwa da komowa domin kare muradun al’ummar Kaduna, tare da tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta kuduri aniyar kammala aikin cikin lokaci. Ya bayyana cewa an umarci kamfanonin da ke aikin da su rika aiki sau biyu a rana domin hanzarta cigaba ba tare da rage inganci ba.
Ministan ya kara da cewa amfani da fasahar siminti mai ɗorewa wanda zai tabbatar da cewa titin zai dawwama tare da rage kudin gyara nan gaba.
Kamfanonin da ke aikin sun yi alkawarin ƙara gaggautawa musamman a yankin Jere dake jihar Kaduna, inda ake sa ido sosai kan ci gaban aiki. Gwamnatin Jihar Kaduna ta kuma tabbatar da ci gaba da haɗin kai da Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya domin magance ƙalubalen da ke iya janyo tsaiko.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA