Iran da Iraki sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro
Published: 12th, August 2025 GMT
Kasashen Iran da Iraki sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar tsaro ta hadin gwiwa a wannan Litinin, dangane da tabbatar da tsaron kan iyakokin kasashen biyu, a ziyarar da babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya kai kasar Iraki.
Larijani da mai baiwa gwamnatin Iraki shawara kan harkokin tsaro, Qasim al-Araji, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar a karkashin jagorancin firayi ministan Iraki Mohammed Shia al-Sudani.
A yayin ziyarar tasa a Bagadaza, Larijani da tawagarsa sun gana da shugaban kasar Iraki Abdul Latif Rashid, da kuma firayi minister al-Sudani da kuma shugaban majalisar dokokin kasar.
A yayin ganawar tasu, Rashid da Larijani sun tattauna batutuwan baya-bayan nan da suka shafi yanking abas ta tsakiya, da kuma na kasa da kasa, inda suka jaddada muhimmancin ci gaba da tattaunawa mai ma’ana a tsakanin kasashen yankin, don warware rikice-rikice da kuma yin aiki don tabbatar da ka’idojin mutunta juna da rashin tsoma baki cikin harkokin cikin gida, a cewar wata sanarwa da fadar shugaban kasar Irakin ta fitar.
Rashid ya jaddada “zurfin dangantakar tarihi da cin moriyar juna a tsakanin Iraki da Iran,” yana mai bayyana muradin kasarsa na samar da tsarin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu ta hanyar da ta dace da al’ummominsu da kuma karfafa tsaro da zaman lafiyar yankin.
A nasa bangaren, Larijani ya bayyana jin dadin kasarsa ga matsayin kasar Iraki na goyon bayan tabbatar da tsaron yankin da kuma rawar da take takawa wajen kusanto da ra’ayoyin bangarori daban daban.
Shi ma firaministan kasar Iraki ya tabbatar da “kokarin da Bagadaza ke yi na raya dangantakar da ke tsakaninta da Tehran da karfafa dangantakar abokantaka mai inganci a matakai da fagage daban-daban, bisa maslahar al’ummomin kasashen biyu.”
Al-Sudani ya bayyana matsayin kasar Iraki na kin amincewa da kai hare-haren da Isra’ila ta yi a kan Iran, sanann kuma ya bayyana goyon bayan Bagadaza ga tattaunawar Amurka da Iran.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Masar ta yi gargadin cewa a shirye take ta dauki duk wani mataki na kare muradunta August 12, 2025 Iran ta yi Allah wadai da kisan kiyashin da Isra’ila ta yi wa ‘yan jarida a Gaza August 12, 2025 Gaza: Yunwa ta kashe Falastinawa 5 a cikin kasa da Sa’o’i 24 da suka gabata August 12, 2025 Ministan tsaron Italiya ya caccaki gwamnatin Netanyahu kan batun Gaza August 12, 2025 Araghchi: Mataimakin Shugaban IAEA Zai Ziyarci Tehan َA Wannan Talata August 11, 2025 Iran: Lebanon Tana Da ‘Yancin Kare Kanta Da Makamanta August 11, 2025 Mali: An Kama Sojoji Fiye da 40 Bisa Zargin Yunkurin Juyin Mulki August 11, 2025 Iraki: Larijani Da Sudani Sun Gana A Bagdaza August 11, 2025 Mafi yawan Kasashen Duniya Sun Amince Da Samarda Kasar Falasdinu August 11, 2025 Mahukuntan Iraki: Adadin Masu Ziyarar Arba’een Daga Kasashen Ketare Zai Iya Haura Miliyan 40 August 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Iraki tabbatar da
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Cimma Matsayi A Yaki Kwanaki 12
Jami’in ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa; Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12
Ali Baqiri Kani mamba a majalisar tsare-tsaren a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa da yahudawan sahayoniyya.
Baqiri ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi ta gidan talabijin a yammacin jiya Asabar cewa: Tabbas Iran ta cimma matsayi sosai a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa, yana mai jaddada muhimmancin diflomasiyya wajen tunkarar hare-haren da ake kai wa kasar, yana mai jaddada cewa: “Dole ne Iran ta mayar da martanin wuce gona da iri kan kasarta a fagen diplomasiyya zuwa wani lamari da duniya ta amince da shi.”
Har ila yau Baqeri Kani ya yi ishara da hadin kan kasa a matsayin mafi girman bayyanar da Iran ta taka rawa a wannan yaki yana mai cewa: Wannan hadin kai yana nuna irin gagarumin goyon bayan da jami’an diflomasiyyar Iran suka nuna.
Ya kara da cewa: Goyon bayan jama’a ga manufofi da matakan gwamnatin na iya taimakawa wajen cimma manufofin diflomasiyya. Har ila yau ya bayyana cewa: A halin da ake ciki yanzu, kasashen yammacin duniya, baya ga Amurka, sun taka rawa wajen tallafawa hare-haren da aka kai wa Iran.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kasar Iran Ta Yi Allah Wadai Da Bukatar ‘Yan Sahayoniyya Ta Son Kwace Zirin Gaza August 10, 2025 Jami’an Tsaron Iran Sun Murkushe ‘Yan Ta’adda Kan Ofishin ‘Yan Sanda A Kudu Maso Gabashin Kasar August 10, 2025 Jefa Agajin Abinci Ta Sama A Zirin Gaza Ya Janyo Shahadan Falasdinawa 23 Tare Da Jikkata Wasu 124 August 10, 2025 Tehran Times: Mai Yiwuwa Iran da Amurka su koma Tattaunawa August 10, 2025 Tel Aviv: Dubban yahudawa sun yi zanga-zangar adawa da yakin Gaza August 10, 2025 Welayati: Makircin Amurka da Isra’ila na kwance damarar Hizbullah ba zai yi nasara ba August 10, 2025 Birtaniya: ‘Yan sanda sun kama akalla mutane 365 a zanga-zangar goyon bayan Falasdinu August 10, 2025 Venezuela: An dakile yunkurin kai wasu munanan hare-hare a cikin kasar August 10, 2025 Pezeshkiyan Ya Yabawa Yan Jarida A Ayyukansu A Yakin Kwanaki 12 August 9, 2025 Yansanda A Burtaniya Ta kama Mutane Fiye Da 200 Masu Goyon Bayan Falasdinawa August 9, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci