An kama basarake kan zargin yi wa ’yar shekara 12 fyaɗe a Gombe
Published: 13th, August 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta cafke wani basarake, Mohammed Tukur mai shekaru 55, a kauyen Sabon Gari da ke yankin Zambuk na Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba, bisa zargin yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyaɗe.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.
Ya ce abin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na daren ranar 9 ga Agusta, 2025, lokacin da ake zargin ya yaudari yarinyar wadda ya kaita wani wuri da babu idon jama’a ya aikata ta’asar.
Bayan samun rahoton faruwar lamarin ne, jami’an ’yan sanda daga ofishin Zambuk suka hanzarta zuwa wurin, sannan suka mika yarinyar zuwa Asibitin Zambuk domin duba lafiyarta.
Nan take dai rundunar ta cika hannu da wanda ake zargin, kuma a halin yanzu yana tsare a hannun ’yan sanda, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: basarake fyaɗe jihar Gombe yarinya
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Shura ta fara ganawar sirri da Malam Triumph
Majalisar Shura ta Jihar Kano ta fara zama da Malam Lawan Shu’aibu Abubakar (Triumph) kan zargin da wasu kungiyoyi biyar ke masa zargin batanci ga Manzon Allah SallalLahu alaihi Wasallama.
Wannan tattaunawa tana gudana ne a cikin sirri a Ofishin Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) kuma ya samu halarcin fitattun malaman Musulunci na Jihar Kano.
Mahalarta sun haɗa shugaban majalisar shurar Malam Abba Koki da Wazirin Kano, Sa’ad Shehu Gidado, da sakatare, Shehu Wada Sagagi, da mambobin kwamitin da Majalisar Shurar ta kadfa domin zargin binciken zargin da ake wa Malam Triumph.