Yadda ɗan shekara 70 ya rasu a gobarar tankokin gas a Zariya
Published: 12th, August 2025 GMT
Wani dattijo ya rasu a sakamakon hatsari da gobarar tankokin sakon iskar gas da ta auku a yankin Zariya da ke Jihar Kaduna.
Aliyu Ramalan Babbale mai shekara sama da 70 ya rasu ne a lokacin da yake ƙokarin tsira da ransa a sakamakon hatsarin tankokin a safiyar ranar Litinin.
Dattijon ya gamu da ajalinsa ne a kan hanyarsa na zuwa gona, lokacin da wasu tankokin dakon gas biyu suka kama da wuta bayan su gogi juna.
Mai auran babban ’yar marigayi Malam Abdullahi Magaji, ya yi wa Aminiya bayanin yadda lamarin ya faru, akan rasuwar marigayin.
ya ce, “A jiya da safe marigayin yana kan babur ne a kan hanyarsa na zuwa gona, sai waɗannan motocin ɗakon man gas ɗin suka kama da wuta kuma suka yi ƙara.
“To a lokacin da yake ƙokarin tsira da rai ne wani shi ma da yake kan babur garin gudu sai ya kwashe shi a inda kafin a kai shi asibitin ya rasu,” in ji shi.
Marigayi ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya shida kuma tuni aka yi jana’izarsa a gidansa da ke Babbale cikin birnin Zariya.
Bayanai na ƙara fitowa dangane da wadanda suka rasu a sanadiyar hatsarin tankokin dakon gas ɗin da ya auku a garin Zariya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gobara Hatsari Zariya
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun kashe gomman mutane a ƙauyukan Sakkwato
An sake shiga tashin hankali a Jihar Sakkwato bayan wani sabon mummunan hari da ’yan bindiga suka kai a wasu kauyuka, lamarin da ke ƙara tsananta matsalar tsaro a faɗin jihar.
Rahotanni sun nuna cewa duk shekara musamman a lokacin damina, ’yan bindiga sukan ƙara ƙaimi wajen kai hare-haren da ke tarwatsa jama’a a garuruwansu da hana manoma zuwa gona ko kuma ƙaƙaba musu harajin zuwa gonakin.
An ɗaure tsohon Firaminista Succes Masra shekaru 20 a Chadi Dan wasan Barcelona Inigo Martinez ya koma Al-NassrAminiya ta ruwaito cewa, a bana ma, maharan sun ci gaba da addabar mazauna ƙananan hukumomi 20 daga cikin 23 na Jihar Sakkwato.
Majiyoyi sun tabbatar cewa a harin baya-bayan nan, ’yan ta’addan sun hallaka mutane da dama sannan sun yi garkuwa da wasu.
Shafin Bakatsine da ke bibiyar rahotannin da suka shafi sha’anin tsaro, a wannan Lahadin ya wallafa a manhajar X cewa, an kai hari a wani masallaci a garin Bushe da ke Karamar Hukumar Sabon Birni, inda aka sace aƙalla mutum 10 ciki har da limamin masallacin.
Rundunar ’yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa ana ci gaba da ƙoƙarin ceto waɗanda aka sace.
Haka kuma, rahotanni sun ce maharan sun sake kai wani hari a lokacin sallar Isha a ƙauyen Marnona na Karamar Hukumar Wurno, a daren Asabar, inda suka kashe masallata da dama sannan suka yi awon gaba da wasu.
Sanata Ibrahim Lamido, mai wakiltar Sakkwato ta Gabas a Majalisar Dattawa, ya yi Allah wadai da hare-haren da suka auku a Bushe da Marnona, inda ya buƙaci hukumomi su ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyar al’umma.