HausaTv:
2025-04-30@19:53:36 GMT

Amurka ta sanar da cewa za ta rage yawan sojojinta a Syria da rabi

Published: 19th, April 2025 GMT

Amurka ta sanar cewa ta rage yawan sojojinta a kasar Syria da rabi, tana mai cewa ta yi nasarar yaki da kungiyar IS, duk da cewa kungiyoyin masu da’awar jihadi na ci gaba da fafutuka a wannan kasa mai rauni.

Wannan shawarar ta zo ne kusan watanni uku bayan hawan Donald Trump kan karagar mulki, bayan da ya dade yana adawa da kasancewar Amurka a can.

Amurka dai ta shafe shekaru da dama tana da sojoji a Syria, a matsayin wani bangare na kawancen kasashen duniya da ke yaki da ISIS.

A cikin wata sanarwa da kakakin ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon Sean Parnell ya fitar, ya ce za a rage yawan dakarun Amurka a Siriya zuwa kasa da dakaru 1,000 a cikin watanni masu zuwa daga kusan 2,000.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Hajjin 2025: Gwamna Namadi Ya Nada Sarkin Kazaure Amirul Hajj

 

Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, ya amince da nadin Mai Martaba Sarkin Kazaure, Alhaji Dr Najib Hussaini Adamu, a matsayin Amirul Hajj na Jihar Jigawa, kuma shugaban tawagar Gwamnatin jihar domin gudanar da aikin Hajjin 2025.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya sanya wa hannu kuma aka raba wa manema labarai.

Gwamnan ya kuma amince da nadin mambobin tawagar Amirul Hajjin.

Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa, mambobin sun hada da Dr. Yusuf Abdurrahman, Babban Limamin Masarautar Hadejia da Alhaji Lawan Ya’u Roni, Talban Kazaure.

Sauran su ne Dr. Mahmoud Yunusa, Sa’in Dutse da kuma Alhaji Adamu Dauda Zakar, Durbin Hadejia.

Sanarwar ta bayyana cewa an yi wadannan nade-nade ne bisa la’akari da irin kwazon da suka nuna a ayyukansu, sadaukarwa, kishin kasa, amana da kuma tsoron Allah.

A cikin sakon taya murna ga wadanda aka nada, Sakataren Gwamnati ya bukace su da su ci gaba da nuna wadannan dabi’u yayin da za su gudanar da wannan muhimmin aiki da aka dora musu, don kara tabbatar da amanar da gwamnatin da al’ummar Jihar Jigawa suka dora a kansu.

Sanarwar ta kara da cewa, ana sa ran tawagar Amirul Hajjin za ta yi aiki kafada da kafada da Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa da kuma sauran hukumomin da suka dace a matakin Jiha, Tarayya da na kasa da kasa domin tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin nasara da inganci.

Sanarwar ta bayyana cewa nade-naden sun fara aiki nan take.

 

Usman Muhammad Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Katafaren Jirgin Daukar Jiragen Yaki Na Kasar Amurka Harry Truman Zai Fice Daga Tekun Maliya
  • Jaridar The Guardian Mafi Yawan ‘Yan Gudun Hijiran Sudan Ne A Gidan Yarin Kasar Girka
  • Karin Wata Kasa Da Bai San Ta Ba A Doron Duniya
  • HKI Tana Amfani Yunwa A Matsayin Makamin Yaki  A Kan Falasdinawa A Gaza
  • Hajjin 2025: Gwamna Namadi Ya Nada Sarkin Kazaure Amirul Hajj
  • Sin Na Maraba Da Karin Abokai Daga Kasa Da Kasa Su Ziyarci Kasar
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Ci Gaba Da Killace Gaza Da Kashe Mutane, Laifi Ne Da Ba A Taba Yin Irinsa Ba
  • Akwai Ƙarin Gishiri A Yawan  Masu Sauyin Jam’iyya Zuwa APC – El-Rufai
  • Uganda Ta Sanar Da Kawo Karshen Ebola Da Ta Barke A Kasar
  • Kasar Sin Za Ta Samar Da Dokar Da Ta Shafi Raya Kasa