Nijeriya Da Isra’ila Na Kara Karfafa Alaka A Tsakaninsu
Published: 13th, August 2025 GMT
Nijeriya da Isra’ila sun sake jaddada aniyarsu ta karfafa haɗin gwiwar tsaro a fannoni daban-daban, kamar batun yaƙi da ta’addanci, musayar bayanan sirri, samar da kuɗin tsaro da kuma bayar da horo na musamman ga jami’an tsaron Nigeria.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwar haɗin gwiwa wadda Ƙaramar Ministar Harkokin Wajen Nijeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, da Mataimakiyar Ministan Harkokin Waje ta Isra’ila, Sharren Haskel-Harpaz suka fitar bayan wani taro na musamman da suka gudanar a Abuja.
Sanarwar, wadda mai magana da yawun Ofishin Ƙaramar Ministar Harkokin Wajen, Dokta Magnus Eze ya fitar, ta ce taron ya nuna alaƙa mai ɗorewa da muhimmanci tsakanin bangarorin biyu.
A yayin taron, wakilan bangarorin biyusun tattauna batutuwan da suka shafi tsaro a duniya, musamman yaƙi da ta’addanci, da kuma inganta hulɗar siyasa da tattalin arziki.
Ministocin biyu sun jaddada aniyarsu ta yin aiki tare wajen samar da bayanai na sirri kan barazanar ta’addanci a duniya, musamman kan hanyoyin samar da kuɗaɗen da ke ɗaukar nauyin ta’addanci.
Najeriya na daga cikin kasashe masu alaka mai karfi tsakaninsu da Isra’ila, musamman a bangarorin da suka shafi batutuwan tsaro da kuma noma.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kasashe 27 Sun Bukaci Isara’ila Ta Kawo Karshen Hana Shigar Da Abinci A Gaza August 12, 2025 Iran: Duk Wani Sabon Hari, Zai Fuskanci Mummunan Martanin Soji August 12, 2025 Larijani: Iraki Ba Ta Karbar Umarni Daga Iran August 12, 2025 Iran: Ma’aikatar Harkokin Waje Ce Ke Kula Da Lamarin Makamashin Nukliyar Kasar August 12, 2025 Armenia Ta Tabbatarwa Iran Zata Kula Da Muradunta Bayan Yarjeniya Da Azarbaijan A Amurka August 12, 2025 Araqchi: Kisan Kiyashi A Gaza Babban Abin Kunya Ne Ga Gwamnatocin Yammacin Turai August 12, 2025 Larijani Ya Ce: ‘Yan Gwagwarmaya Sun San Abubuwan Da Suka Dace August 12, 2025 Iraki Ta Bukaci Tattaunawa Tsakanin Larabawan Yankin Tekun Farisa Da Iran August 12, 2025 Italiya Ta Janye Jirgin Ruwanta Daga Tekun Bahar Maliya Saboda Barazanar ‘Yan Gwagwarmayar Yemen August 12, 2025 MDD Ta Sanar Da Mutuwan Mutane 60 Saboda Yunwa A El-Fasher Na Sudan August 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Gudanar Da Jana’izar Shahidai 300 A Dai-Dai Ranar Shahadar Zahra (s) A Jiya Litinin
Miliyoyin mutanen kasar Iran sun gudanar da jana’izar shahidai kimani 300, a duk fadin kasar, a dai-dai lokacinda ake makokin shahadar diyar manzon Allah (s) Fatimah Azzahra (s).
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, shahidan, wadanda har yanzun ba’a tantance su ba, an ganosu a wurare daban-daban a cikin kasar Iran inda suka yi shahada a yakin shekaru 8 tsakanin Iran da Iraki a farko-farkon nasarar juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran. (1980-1988).
Ya zuwa yanzu dai an gano gawakin shahidai fiye da 45,000, sannan akwai wasu fiye da 2000 wadanda ake neman inda suke a cikin kasar ta Iraki.
Labarin ya kara da cewa a nan Tehran kadai an yi jana’izar shahidai 100. Sannan sauran gawakin shahidan, wadanda aka ganosu a tsibirin Maimoon da Shalamce, an yi masu jana’iza a lardin Golestan, Qom, Fars, Sistan da Baluchestan, Ardabil, gabacin Azerbaijan da wasu wurare.
Wadannan shahidan sun yi shahada ne a ayyukan farmaki na Kheibar, Karbala-4, Karbala-5, da kuma Valfajr-1.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Amurka Da HKI Sun Kawo Karshen Hukumar GHF Mai Raba Abinci A Gaza November 25, 2025 Babban Kwamandan Sojojin Sudan Ya Yi Watsi Da Tsirin Trump Na Zaman Lafiya November 25, 2025 Hamas Ta Ce Keta Hurumin Tsagaita Wutan Da HKI Take Yi Zai Iya Kawo Karshen Tsagaita Wutar November 25, 2025 Gwamnonin Kudu Maso Yammacin Najeriya Sun Ce Lokacin Kafa Yansandan Jihohi Ya Yi November 25, 2025 Hizbullah Ta na Juyayin shahadar Babban Kwamanda Haitham Ali Da Isra’ila Ta Kashe. November 24, 2025 Dubban Alummar Kasar Tunisia Ne Suka Gudanar Da Zanga-zangar Adawa Da Mulkin Kama Karya A Kasar November 24, 2025 Mutane 6 Ne Suka Mutu Sakamakon Harin Kunar Bakin Wake Da Aka Kai A Peshavar Na Kasar Pakistan November 24, 2025 Hamas Tayi Gargadi Game Da Rushewar Yarjejeniyar Bude Wuta Idan Israila Ta ci Gaba Da Kai Hare-Hare November 24, 2025 Amnesty International Ta Zargi Najeriya Da Gazawa Wajen Kare Rayukan Al’ummarta November 24, 2025 Wakilin MDD Ya Bukaci Goyon Bayan Iran Wajen Tabbatar Da Zaman Lafiya A Yamen November 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci