Tinubu Ya Sake Nada Dankaka A Matsayin Shugaban Hukumar Kula Da Da’ar Ma’aikata Ta Kasa
Published: 12th, August 2025 GMT
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake nada Dr. Muheeba Dankaka a matsayin shugaban hukumar kula da da’a ta tarayya (FCC) a wa’adi na biyu na shekaru biyar.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai, Bayo Onanuga, ya ce nadin na daya daga cikin alkawurran da shugaban kasar ya yi na “karfafa hukumar don tabbatar da adalci, daidaito da kuma hada kai a nade-naden na tarayya bisa tanadin tsarin mulki.
Shugaban ya kuma nada Mohammed Musa a matsayin sakataren hukumar sannan Kayode Oladele daga jihar Ogun a matsayin kwamishina. An nada Oladele, wanda tsohon dan majalisar wakilai ne a hukumar a shekarar 2024 kuma ya rike mukamin shugaban riko bayan kammala wa’adin farko na Dankaka.
Sauran kwamishinonin da suka dawo sun hada da Lawal Ya’u Roni (Jigawa), Abubakar Atiku Bunu (Kebbi), da Eludayo Eluyemi (Osun).
Sabbin kwamishinonin da aka nada sune:
Hon. Obina Oriaku (Abia)
Mrs. Bema Olvadi Madayi (Adamawa)
Obongawan Dora Ebong (Akwa Ibom) Hon. Nnoli Nkechi Gloria (Anambra)
Babangida Adamu Gwana (Bauchi)
Sir Tonye Okio (Bayelsa)
Aligba Eugene Tarkende (Benue)
Engr. Modu Mustapha (Borno)
Dr. Stella Odey Ekpo (Cross River)
Edrin Lovette Idisi (Delta)
Barr. Nwokpor Vincent Nduka (Ebonyi)
Hon. Chief Victor Sabor Edoror (Edo)
Hon. Sola Fokanle (Ekiti)
Peter Eze (Enugu)
Ibrahim Baba Mairiga (Gombe)
Hon. Jerry Alagbaoso (Imo)
Ruth Jumai Ango (Kaduna)
Muhammad Awwal Nayya (Kano)
Hon. Anas Isah (Katsina)
Bello Idris Eeye (Kogi)
Dr. Ibrahim Abdullahi (Kwara)
Alh. Isah Jibrin (Niger)
Comrade Ajimudu Bola (Ondo)
Prince Ayodeji Abas Aleshinloye (Oyo)
Hon. Pam Bolman (Plateau)
Haruna Chukwuemeka (Rivers)
Alh. Aminu Tambar (Sokoto)
Comrade Bobboi Bala Kaigama (Taraba)
Hon. Jibir Maigari (Yobe) Sani Garba (Zamfara)
Solomon Ayuba Dagami (FCT)
PR/BELLO WAKIL
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Fadar Shugaban Ƙasa Ta Ƙaryata Batun Rashin Lafiyar Tinubu
Sai dai wasu daga cikin hadiman shugaban kamar Abdulaziz Abdulaziz, mai taimaka masa a kafafen watsa labaru, ya ce labarin ba gaskiya ba ne.
Batun rashin lafiyar Tinubu ba sabon abu ne, domin tun yana yaƙin neman zaɓen takara a 2023 ake kai ruwa rana kan batun.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp