Yajin Aikin NLC Da TUC Ya Gurgunta Ayyukan Gwamnati A Taraba.
Published: 12th, August 2025 GMT
Yajin aikin sai baba-ta-gani da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC reshen jihar Taraba, da kungiyar Kwadago (TUC) reshen jihar Taraba suka kaddamar a ranar Litinin da ta gabata, ya gurgunta ayyukan gwamnati a ma’aikatu da hukumomin gwamnati a jihar.
Matakin wanda ya fara da tsakar daren litinin, ya kasance tare da hadin gwiwar shugabannin kungiyoyin biyu bayan taron majalisar zartaswar jihar da aka gudanar a ranar Lahadi a sakatariyar kungiyar NLC ta jihar.
Taron ya yi nazari ne kan wa’adin da aka bayar tun da farko kan wasu kura-kuran da ake zargin an tafka a cikin ayyukan kwamitin tantance bayanan da gwamnatin jihar ta kafa.
A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da sakataren kungiyar NLC na jihar, Adamu.W.Buba, da sakatariyar TUC ta jihar, Polina Gani suka sanya wa hannu, kungiyoyin sun umurci dukkanin rassan kungiyar da su tashi tsaye tare da kafa kwamitin aiwatar da yajin aikin domin tabbatar da an bi cikakken aikin.
“Dukkan ma’aikatan suna nan ta hanyar umarnin su kaurace wa wuraren aikinsu kuma su janye ayyukansu har sai wani lokaci. Za a ci gaba da yajin aikin har sai gwamnati ta biya musu bukatunsu,” in ji sanarwar “.
Kungiyoyin kwadago a makon da ya gabata sun zargi kwamitin da aikata ayyukan da suka yi wa ma’aikata illa tare da zargin gwamnati da yin watsi da wa’adin.
Shugabannin kungiyar sun bayyana cewa ba za a dakatar da yajin aikin ba har sai an gyara kura-kuran da ake zarginsu da aikatawa, inda suka bukaci masu ruwa da tsaki da su shiga Tsakani su da gwamnatin jihar.
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, hukumomi daga gwamnati ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
COV/JAMILA ABBA
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Taraba
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Tarayya Ta Gargaɗi ASUU Kan Yajin Aiki, Ta Ce “Babu Aiki, Babu Albashi”
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Tinubu Ya Isa Birnin Rome Don Halartar Taron Tsaro Na Aqaba October 12, 2025
Manyan Labarai An Sauya Kwamishinan Ƴansandan Abuja Saboda Rashin Tsaro October 12, 2025
Tsaro Sojoji Sun Kashe Kwamandan IPOB ‘Alhaji’, Da Wasu 26, Sun Kama 22 October 12, 2025