Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo, ya ce ranar Litinin ya ziyarci Shugaban Kasa Bola Tinubu, kuma sabanin yadda ake ta rade-radi, shugaban na nan cikin koshin lafiya kuma babu abin da ke damun shi.
A ’yan kwanakin nan dai ana ta samun jita-jitar cewa shugaba Tinubu na can kwance magashiyyan yana fama da rashin lafiya a daidai lokacin da aka shafe sama da mako guda ba a ji motsin shi ko an gan shi a wajen wani taro ba.
Sai dai da yake zantawa da ’yan jaridar Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja bayan ya gana da shi, Gwamnan ya ce Tinubu na na kalau.
“Shugaban Kasa na nan kalau, kuma cikin koshin lafiya yana kuma ci gaba da ganawa da jama’a, kuma ni ma na ji dadin tattaunawa da shi,” in ji Gwamnan.
Baya ga Gwamna Soludon, shi ma takwaransa na jihar Ekiti, Biodun Oyebanji da Sanatan Nasarawa ta Yamma, Aliyu Wadada da kuma Ministan Kudi Wale Edun, su ma sun je fadar don ganawa da Tinubu a ranar ta Litinin.
Gwamnan Soludo dai wanda ke neman wa’adi na biyu a zaben Gwamnan jihar da za a gudanar ranar takwas ga watan Nuwamba mai zuwa, ya yi kira ga jama’a da su yi gangamin mara wa Tinubu baya, yana mai bayyana shi a matsayin jagoran bunkasa Dimokuradiyya da habaka tattalin arzikin Najeriya.
Kodayake dai ya ki bayyana ainihin abin da suka tattauna ga ’yan jarida, amma dai ya ce ganawar tasu ta yi kyau.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Rashin lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Wakilai ta nemi gwamnati ta gaggauta dauko Jonathan daga Guinea Bissau
Majalisar Wakilai a ranar Alhamis, ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta yi amfani da diflomasiyya da duk wasu hanyoyi don tabbatar da dawowar tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan lafiya daga Guinea Bissau, bayan juyin mulkin sojoji a ƙasar.
Wannan kuduri ya biyo bayan amincewa da kudurin gaggawa da Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Farfesa Julius Ihonvbere, ya gabatar.
Ihonvbere ya shaida wa Majalisar cewa Jonathan, wanda ya je ƙasar domin sa ido kan zaɓe, ya makale bayan juyin mulkin, yana mai cewa gwamnati ta nemo hanyoyin da za su tabbatar da dawowarsa lafiya.
Muna tafe da karin bayani…