Kano Na Karbar Bakuncin Babban Taron Kungiyar NUJ Na Kasa
Published: 13th, August 2025 GMT
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatinsa na samar da kyakkyawar alaka da kafafen yada labarai.
Gwamna Yusuf ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ), Kwamared Alhassan Yahaya, da ‘yan majalisar zartaswar NUJ na kasa (NEC) da suka je Kano domin taronsu.
Gwamnan wanda mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya wakilta, ya yaba wa kungiyar ta NUJ bisa zabar Kano a taron ta na kasa, yana mai jaddada cewa wannan shaida ce ta kyakkyawar alakar aiki tsakanin gwamnatin jihar Kano da kafafen yada labarai.
Ya ce gwamnatinsa ta samu gagarumar nasara wajen inganta rayuwar jama’a, da kuma tabbatar da cewa dole ne a cika alkawuran yakin neman zabe.
“Wadannan alkawuran sun hada da samar da ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, noma, da karfafa matasa da mata,” in ji shi, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da fitar da wasu ayyuka da za a yaba don inganta rayuwar al’umma.
Mataimakin gwamnan ya ci gaba da yaba wa kungiyar ta NUJ bisa rawar da take takawa wajen tabbatar da dimokuradiyya, da tabbatar da bin doka da oda, da wayar da kan al’umma, inda ya ce kafafen yada labarai na da matukar muhimmanci wajen samar da shugabanci na gari.
Ya kara da cewa “Gwamnatinmu tana da abokantaka da kafafen yada labarai kuma za ta ci gaba da bayar da dukkan goyon bayan da suka dace don tabbatar da cewa ‘yan jarida suna gudanar da ayyukansu cikin ‘yanci, da sanin ya kamata, da kuma samar da yanayi mai kyau,” in ji shi.
Shugaban kungiyar ta NUJ, Kwamared Alhassan Yahaya ya yabawa gwamnatin jihar Kano bisa karbar bakuncin taron, ya kuma yaba da ci gaban jihar, wanda tawagar ta lura da haka a ziyarar gani da ido da ta kai a babban birnin.
“Mun gamsu da ci gaban da aka samu kawo yanzu ta fuskar samar da ababen more rayuwa da ake samu a Kano,” inji shi.
Alhassan ya yabawa gwamnatin jihar Kano bisa goyon bayan da take baiwa kafafen yada labarai, kuma ya nemi a dore da wannan matakin.
Tun da farko kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Ibrahim Waiya ya yi maraba da shugabannin kungiyar ta NUJ tare da yi musu fatan zaman lafiya a yayin taron, inda ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin gwamnati da kafafen yada labarai.
Ana sa ran taron NUJ NEC zai tattauna kan muhimman batutuwan da suka shafi aikin jarida a Najeriya, da suka hada da jin dadin kafafen yada labarai, kare lafiyar ‘yan jarida, da dabarun kungiyar na kare ‘yancin ‘yan jarida.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: da kafafen yada labarai kungiyar ta NUJ tabbatar da
এছাড়াও পড়ুন:
Yajin Aikin NLC Da TUC Ya Gurgunta Ayyukan Gwamnati A Taraba.
Yajin aikin sai baba-ta-gani da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC reshen jihar Taraba, da kungiyar Kwadago (TUC) reshen jihar Taraba suka kaddamar a ranar Litinin da ta gabata, ya gurgunta ayyukan gwamnati a ma’aikatu da hukumomin gwamnati a jihar.
Matakin wanda ya fara da tsakar daren litinin, ya kasance tare da hadin gwiwar shugabannin kungiyoyin biyu bayan taron majalisar zartaswar jihar da aka gudanar a ranar Lahadi a sakatariyar kungiyar NLC ta jihar.
Taron ya yi nazari ne kan wa’adin da aka bayar tun da farko kan wasu kura-kuran da ake zargin an tafka a cikin ayyukan kwamitin tantance bayanan da gwamnatin jihar ta kafa.
A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da sakataren kungiyar NLC na jihar, Adamu.W.Buba, da sakatariyar TUC ta jihar, Polina Gani suka sanya wa hannu, kungiyoyin sun umurci dukkanin rassan kungiyar da su tashi tsaye tare da kafa kwamitin aiwatar da yajin aikin domin tabbatar da an bi cikakken aikin.
“Dukkan ma’aikatan suna nan ta hanyar umarnin su kaurace wa wuraren aikinsu kuma su janye ayyukansu har sai wani lokaci. Za a ci gaba da yajin aikin har sai gwamnati ta biya musu bukatunsu,” in ji sanarwar “.
Kungiyoyin kwadago a makon da ya gabata sun zargi kwamitin da aikata ayyukan da suka yi wa ma’aikata illa tare da zargin gwamnati da yin watsi da wa’adin.
Shugabannin kungiyar sun bayyana cewa ba za a dakatar da yajin aikin ba har sai an gyara kura-kuran da ake zarginsu da aikatawa, inda suka bukaci masu ruwa da tsaki da su shiga Tsakani su da gwamnatin jihar.
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, hukumomi daga gwamnati ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
COV/JAMILA ABBA