Majalisar Dokokin Jihar Zamfara karkashin jagorancin Bashar Aliyu Gummi, ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta hada kai da ayyukan tsaro a Jihar domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, kamar yadda babi na biyu na kundin tsarin mulki ya tanada.

 

A zaman taron na ranar Talata, mambobin sun yi zargin cewa, ‘yan bindiga sun mamaye al’ummomi da dama a fadin jihar Zamfara, kuma sun zargi Gwamnan da mayar da hankali kan burin siyasa da kuma zargin abokan hamayya.

 

Sun kuma yi zargin cewa, Gwamnan bai kai ziyara ko aika tallafi ga al’ummomin da hare-hare ya shafa ba, inda suka ce ziyarar da ya shirya kai wa al’ummar Banga da ke karamar hukumar Kaura Namoda ta kasance da alaka da siyasa gabanin zaben fidda gwani na majalisar dokokin jihar.

 

A nasa gudunmuwar, Bashir Abubakar Masama na Bukkuyum ta Arewa ya yabawa kokarin gwamnatin tarayya na yaki da ‘yan fashi, inda ya bayyana cewa Adapka, Zauma, Gwashi, da Mayanchi a mazabarsa sun sha fama da hare-hare akai-akai.

 

Da yake goyon bayan kudirin, Bashir Bello Sarkin Zango na Bungudu ta Yamma, ya yi zargin cewa, Gidan Bugaje, Zaman Gida, Kukan Tara, da Gidan Dan-Inna, gungun miyagu sun mayar da yankin nasu, yayin da shugaban marasa rinjaye Aliyu Ango Kagara na Talata Mafara ta Kudu ya sanya Morai, Bobbo, Makera, Jangebe, Gwaram, da Ruwan Gizo a matsayin kauyukan da lamarin ya fi shafa a mazabarsa.

 

‘Yan majalisar sun bukaci gwamnatin tarayya da ta yi watsi da gwamnatin jihar a harkokin tsaro.

 

Sun yi kira ga mazauna yankin da su kasance masu bin doka da oda tare da bayar da sahihan bayanai ga hukumomin tsaro.

 

A nasa bangaren, Ibrahim Tudu Tukur na Bakura ya yi zargin cewa al’ummarsa na ci gaba da zama a killace da ‘yan bindiga, inda ya bayar da misali da harin da aka kai a kwanan nan a Damri, Dakko, Sama, Sabon Garin Damri, da Sade, yayin da Faruk Musa Dosara na Maradun ya yi kira da a duba yiwuwar tsige Gwamnan bisa zarginsa da yin sakaci da aikinsa.

 

Ya kuma jaddada bukatar mazauna yankin su baiwa jami’an tsaro sahihin bayanai kan duk wani nau’in da ake zargi da aikata laifuka domin a kama su kafin su aikata wani laifi.

 

Sun kuma yi alkawarin ci gaba da yin kira da a samar da shugabanci na gari a Zamfara domin ci gaban jihar.

 

AMINU DALHATU.

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: siyasa yi zargin cewa

এছাড়াও পড়ুন:

Hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna Ta Bukaci Maniyyatan Aikin Hajjin 2026 Su Fara Biyan Kudaden Ajiya

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna ta shawarci maniyyata aikin Hajjin shekarar 2026 da su fara shirin biyan kudaden ajiya.

Kiran ya biyo bayan taron da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta gudanar tare da hukumomin Alhazai na jihohi, inda aka bayar da shawarar ajiyar naira miliyan 8 da rabi ga masu niyyar zuwa aikin Hajji, kafin a sanar da hakikanin kudin aikin Hajjin shekarar 2026.

A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun hukumar, Yunusa Mohammed Abdullahi, ya shawarci wadanda ba su da fasfo da su gaggauta zuwa Hukumar Shige da Fice ta Kasa domin yin nasu, yana mai cewa shi ne ake amfani da shi wajen hada takardun tafiya.

Najeriya ta sake samun kujeru 95,000 daga Masarautar Saudiyya domin aikin Hajjin 2026, ana kuma sa ran  jihar Kaduna za ta sake samun yawan kujerun da aka saba bata.

Yunusa Mohammed ya kuma bayyana cewa hukumar za ta sanar da maniyyata lokacin da za a fara yin rajista a Jihar Kaduna.

 

Safiyah Abdulkadir 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisar Kano Ta Karbi Kudirin Karamin Kasafin Kudi Na Shekarar 2025
  • ‘Yan Sanda Sun Kama Wasu Da Ake Zargin ‘Yan Kungiyar Asiri Ne A Jihar Kwara
  • Rundunar ‘Yan Sandan Kano Ta Yi Gargadi Game Da Sabawa Dokokin Fitillun Bada Hannu A Titinan Jihar
  • EFCC ta tsare tsohon Gwamnan Sakkwato Tambuwal kan zargin N189bn
  • Gwamnatin Jigawa Ta Raba Naira Miliyan 50 Ga Mata Da Matasa
  • Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda sama da 400 a Zamfara
  • Hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna Ta Bukaci Maniyyatan Aikin Hajjin 2026 Su Fara Biyan Kudaden Ajiya
  • Majalisar Dokokin Kano Ta Karɓi Ƙarin Kasafin Kuɗi Na 2025
  • Runduunar ‘Yan Sandan Jihar kwara Ta Karfafa Tsaro A Banbila