NAJERIYA A YAU: Yadda matasa ke bayar da gudunmawa ga ci-gaban al’umma
Published: 12th, August 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Samun matasan da ke bayar da gudunmawa ga ci-gaban al’ummominsu abu ne da ba kasafai ake samu ba a wannan zamani.
Amma duk da haka, wasu matasa sun sadaukar da rayuwarsu wajen bayar da gudunmawarsu wajen ci-gaban al’ummarsu.
NAJERIYA A YAU: Yadda Damina Ke Shafar Masu Ƙananan Sana’o’i DAGA LARABA: Me Ke Sa Matasa Zama Karnukan Farautar ‘Yan Siyasa A Kafafen Sadarwa Na Zamani?Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan irin gudunmawar da matasa ke bayarwa wajen ci-gaban al’ummarsu.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ranar Matasa ranar matasa ta duniya
এছাড়াও পড়ুন:
Mutane 2 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Kebbi
Aƙalla mutane biyu ne suka mutu a rikicin da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a unguwar Dambo, wani kauye da ke da tazarar ’yan kilomita daga Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi.
Wani mazaunin yankin mai suna Ɗanladi Usman ya ce rikicin ya fara ne bayan an kashe wani mutum mai suna Sule yayin da yake aiki a gonarsa.
“Kashe Sule ya tayar da hankulan al’umma, inda manoma suka ɗauki fansa suka kashe wani makiyayi da har yanzu ba a gano sunansa ba,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa makiyayan sun sha faɗa da manoma a kwanakin baya bayan sun aike musu da sako cewa su hanzarta girbe amfanin gonakinsu domin za su riƙa wucewa da shanunsu ta gonakin nan ba da daɗewa ba.
An yi jana’izar sojojin da ’yan bindiga suka kashe a Kebbi Rashin wutar lantarki ya rusa harkoki a Kaduna, Kano da Katsina“A lokacin da wasu manoma suka je gonakinsu domin yin aiki, sai makiyaya suka kai musu hari, daga nan ne aka shiga tashin hankali,” in ji shi.
Wani mazaunin yankin, Abubakar Aliyu, ya roƙi gwamnati da ta kawo ƙarshen wannan rikici na dogon lokaci tsakanin manoma da makiyaya.
“Wannan matsala ba sabuwa ba ce, kuma sarakunan gargajiya sun san da ita. Muna fatan a samu adalci ga waɗanda abin ya shafa, kuma gwamnati ta kawo ƙarshen wannan rikici,” in ji shi.
Rundunar ’yan sanda a jihar ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba domin jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Nafiu Abubakar, ba a iya samun sa a waya ba lokacin da ake haɗa wannan rahoto.