Yaushe Ronaldo Zai Daina Jefa Kwallo A Raga?
Published: 24th, March 2025 GMT
Cristiano Ronaldo ya zura ƙwallo a wasan da Portugal ta doke abokiyar karawarta ƙasar Denmark a daren ranar Lahadi, ƙwallon ita ce ta 929 da tsohon ɗan wasan na Manchester United ya jefa a tarihinsa na ƙwallon ƙafa, duk da cewar ya ɓarar da bugun daga kai sai mai tsaron gida a wasan da Portugal ta tsallake rijiya da baya, hakan ya sa ta kai wasan dab da na kusa da na karshe a gasar ta Nations League.
An tashi wasan ne da ci 3-3 jimilla bayan mintuna 90, amma Francisco Trincao ya sake zura kwallo a minti na 10 na ƙarin lokaci bayan da mai tsaron ragar Denmark Kasper Schmeichel ya ture wata ƙwallon da Goncalo Ramos ya buga.
Ronaldo Da Messi Ne Kan Gaba A Jerin ‘Yan Wasan Da Suka Fi Karbar Albashi Ballon D’or: An Zaɓe Ni Ne Kamar Yadda Aka Zaɓe Ka – Martanin Rodri Ga RonaldoGoncalo Ramos wanda ya maye gurbin Cristino Ronaldo ne ya jefa ƙwallo ta biyar a ragar Denmark gab da za a tashi daga wasan, a wasan farko da ƙasashen su ka buga a ranar Alhamis, Denmark ce ta doke Portugal da ci ɗaya mai ban haushi.
Kafin a tashi wasan dai an karrama ɗan wasan tsakiya na Manchester City Bernardo Silva da kyautar girmamawa kasancewarshi ɗan wasa na 8 a tarihin ƙasar Portugal, da ya buga wasanni 100 a tawagar ƙwallon ƙafa ta Portugal ta maza, tawagar Roberto Martinez za ta kara da Jamus a wasan gaba, bayan da tawagar Julian Nagelsmann ta doke Italiya da ci 5-4 a wasanni biyu da su ka buga.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Araghchi : Za’ayi Tattaunawar Iran da Amurka ta gaba a Rome bayan taron E3
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce za a yi taro karo na hudu na shawarwari tsakanin Tehran da Washington kan shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a birnin Rome na kasar Italiya a ranar Asabar mai zuwa.
M. Araghchi ya fadawa manema labarai a gefen taron majalisar ministocin gwamnatin kasar na mako-mako yau Laraba cewa, inda ya ce taron na Rome zai kasance gabanin wani taro a ranar Juma’a na tsakanin Tehran da kasashen Turan nan uku da ake wa lakabi da E3 wato – Ingila, Faransa da kuma Jamus wadanda suka sanya hannu kan yarjejeniyar nukiliyar Iran ta 2015.
Ya ce rawar da kasashen Turai uku ke takawa ta ragu sakamakon manufofinsu a tattaunawar da aka dade ana yi, don haka a shirye muke mu gudanar da zagaye na gaba na shawarwari da su a birnin Rome.
Babban jami’in diflomasiyyar ya kara da cewa, Tehran na da burin warware batun nukiliyarta cikin lumana.”
Da aka tambaye shi game da halin da ake ciki na baya-bayan nan na kudaden da Iran ta toshe saboda takunkumin da kasashen yamma suka kakaba mata, Araghchi ya ce daskararrun kudaden na daga cikin takunkumin da ya zama dole a dagewa iran.
Kawo yanzu Iran da Amurka sun yi tattaunawa har uku ta farko a Oman, ta biyu a Italiya sai kuma wace aka gudanar a ranar Asabar data gabata a Oman.
Dukkanin bangarorin na cewa akwai fata mai kyau a jerin tattaunawar da suka gabata.