Za mu farfaɗo da Madatsar Ruwa ta Biu — Zulum
Published: 24th, March 2025 GMT
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya jaddada kudirin gwamnatinsa na sake farfaɗo da Madatsar Ruwa ta Biu da aka daɗe da watsi da ita domin bunƙasa noman rani da nufin samar da wadataccen abinci a Kudancin Borno da ma Jihar ta Borno gaba ɗaya.
Zulum ya yi wannan alkawarin ne a yayin wata ziyarar ban girma da ya kai wa Mai martaba Sarkin Biu, Mustapha Umar Mustapha, a ziyarar aiki ta kwana uku da ya kai masarautar kwanakin baya.
“Kokarin farfado da wannan madatsar ruwa na da matuƙar muhimmanci wajen magance ƙalubalen ƙarancin ruwa da aka shafe shekaru biyu ana yi a yankin,” in ji gwamnan.
Ya kuma jaddada cewa, farfado da madatsar ruwan zai dawo da ayyukan noman rani masu yawa a Kogin Hawul, wanda zai amfanar da kananan hukumomi shida na Kudancin Borno.
Da yake jaddada muhimmancin noman rani ga al’umma, gwamnan ya lura cewa, noma ya kasance ginshiƙin manufofin gwamnatinsa, wadda ya ce ita ce manufarsu, domin tabbatar da wadatar abinci da samar da rayuwa mai dorewa, musamman ga wadanda rikicin Boko Haram ya shafa.
Ya kuma tabbatar wa mai martaba sarki da al’ummar Biu cewa, in an kammala madatsar ruwan a 2026 in Allah Ya so, zai kawo sauyi sosai a fannin noma da kuma damar bunkasa tattalin arziki a yankin.
“Aikin noma na daya daga cikin manyan ginshikan gwamnatina, kuma za mu ci gaba da saka hannun jari a fannin don inganta samar da abinci da inganta rayuwar al’ummarmu,” in ji shi.
Gwamna Zulum ya kuma bayyana cewa, za a kara aiwatar da ayyukan raya kasa a masarautar kafin wa’adinsa ya kare a 2027.
Ya kuma jaddada bukatar hadin kan shugabannin siyasa, inda ya bayyana cewa hadin kai zai iya kara habaka tattalin arziki da samar da ababen more rayuwa a fadin jihar.
“Abin farin ciki ne ganin cewa Jihar Borno ba ta fama da rikicin siyasa, ‘yan majalisar dokokinmu na kasa da na jiha da sauran masu rike da mukaman siyasa, sun ci gaba da kasancewa da haɗin kai wajen samar da ribar dimokuraɗiyya,” in ji Zulum.
A nasa martanin, Mai martaba Sarkin Biu Mustapha Umar Mustapha ya yaba wa Gwamna Zulum bisa jajircewarsa wajen gudanar da ayyukan da suka shafi al’umma a Masarautar Biu.
Ya kuma yaba wa gwamnan musamman kan kaddamar da shirin tallafa wa matasa da marasa galihu, wadanda rikicin shekaru 15 na masu ta da kayar baya da aka yi fama da shi a Jihar Borno da ma wasu jihohin makwabta ya shafi rayuwarsu.
Sarkin ya nuna jin dadinsa da tallafin da gwamnatin jihar ke ci gaba da bai wa al’ummar jihar, inda ya tabbatar da cewa, shirin farfado da madatsar ruwa ta Biu da sauran ayyukan raya kasa za su inganta rayuwar mazauna yankin.
Kasancewar noma a sahun gaba a cikin abubuwan da gwamnatinsa ta sa gaba, ana sa ran sake mayar da hankali kan noman rani da Gwamna Zulum ya yi alkawarin zai bunkasa domin inganta tattalin arziki da kuma karfafa juriyar al’ummar Borno kan karancin abinci.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Babagana Umara Zulum jihar Borno Madatsar Ruwa Noman rani da madatsar
এছাড়াও পড়ুন:
Kotu Ta Kori Ƙarar Neman Diyyar N1bn A Kan Buhari Da Emefiele Kan Sauya Fasalin Naira
Haka kuma ya nemi kotu da ta bayar da umarnin ci gaba da amfani da tsoffin takardun kuɗi na Naira 200, 500 da kuma 1000.
Baya ga haka, ya buƙaci a umarci su da su nemi gafara ta hanyar wallafa bayani a manyan jaridu biyu na ƙasa.
Amma a zaman kotu na ranar Litinin, wanda ya shigar da ƙarar da lauyansa ba su halarci zaman kotu ba.
Lauyan da ke kare Emefiele da CBN, Mista Chikelue Amasiani, ya sanar da kotu cewa tun da aka shigar da ƙarar, mai ƙarar da lauyansa ba su nuna wata alama ta son ci gaba da shari’ar ba.
Ya roƙi kotun da ta kori ƙarar.
Mai shari’a Ekwo ya amince da buƙatar kuma ya kori ƙarar, inda ya bayyana cewa mai ƙarar zai iya dawo da ita idan ya shirya yin shari’ar da gaske.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp