Leadership News Hausa:
2025-08-01@01:10:14 GMT

NDLEA Ta Kama Ƴar Indiya Ɗauke Da Hodar Iblis A Kano

Published: 24th, March 2025 GMT

NDLEA Ta Kama Ƴar Indiya Ɗauke Da Hodar Iblis A Kano

Hukumar yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta kama wata mata ‘yar ƙasar Indiya mai suna Neetu Neetu, mai shekara 42, a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano, ɗauke da hodar iblis mai nauyin kilo 11 da aka ɓoye a cikin ledojin da ke kama da kwallon alawar cakulati. An cafke ta ne a yayin binciken shigowarta daga jirgin Qatar Airways daga Bangkok ta Vietnam da Doha.

Shugaban hukumar, Birgediya Janar Buba Marwa (Rtd), ya ce wannan kamun ya sake nuna yadda masu safarar kwayoyi ke amfani da ‘yan ƙasashen waje don kutsawa da miyagun kwayoyi cikin ƙasar. A cewarsa, NDLEA na ci gaba da daƙile irin wannan yunƙuri ta hanyar bayanan sirri da fasahohin zamani.

NDLEA Ta Gargadi Iyaye Kan Bayyanar Alawar Ƙwaya A Kano Jami’an NDLEA Sun Kashe Budurwa A Kano, An Damƙe Su 

A wani sumame a Kano, an kama Michael Ogundele dauke da tramadol guda 50,000 da aka boye a cikin bututun gas, yayin da a Gunduwawa aka cafke Sunday Ogar da kilogram 27 na wiwi. Haka zalika, an kama Khadijah Abdullahi a Lungun Bulala da kwalabe 424 na maganin tari mai sinadarin Kodin.

A Lagos kuwa, jami’an NDLEA sun kama mutane da dama da wiwi, da tramadol, da Kodin a Mushin, Apapa da Ikotun. NDLEA ta ci gaba da shirinta na wayar da kai a faɗin ƙasar, ciki har da makarantu da masallatai. Marwa ya yaba wa jajircewar jami’an hukumar, yana mai kira da su ci gaba da aiki da kwazo da rikon amana.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnan Zamfara Ya Naɗa Abdulkadir Ibrahim A Matsayin Sabon Sarkin Katsinan Gusau Na 16

Gwamna Lawal ya taya sabon sarki murna, tare da roƙon Allah Ya bashi hikima da ikon yin jagoranci na gari.

Ya kuma buƙace shi da ya ci gaba da bin kyawawan ɗabi’u da tafarkin tsofaffin sarakuna domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a masarautar Gusau.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kamfanonin Sadarwa Za Su Ci Gaba Da Rajistar Sabon SIM – NIMC
  • Za a fara yi wa ɗaliban jami’o’i gwajin ƙwaya — Gwamnatin Nijeriya
  • Sin Na Ci Gaba Da Kyautata Rayuwar Al’umma Ta Amfani Da Hidimomin Dijital Da Na Kirkirarriyar Basira
  • Kwara Ta Kwashe Mabarata Daga Titunan Jihar Su 94
  • Tinubu ya karɓi baƙuncin Abdulmumin Jibrin Kofa
  • Za a kammala shimfiɗa layin dogo daga Kaduna zuwa Kano a 2026 — Gwamnatin Tarayya
  • Gwamnatin Jihar Kano Ta Kaddamar da Manufar Sauyin Yanayi
  • ‘Yan Sanda A Kano Sun Kama Kasurgumin Dan Fashin Nan Barga Da Wasu Mutum 14
  • Gwamnan Zamfara Ya Naɗa Abdulkadir Ibrahim A Matsayin Sabon Sarkin Katsinan Gusau Na 16
  • EFCC Ta Kama Mutane 11 Kan Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Akwa Ibom